_Tsaye take a matatakalar bene ta zuba wa k'asan falon ido,ranta yayi matukar 6aci sanadiyar hango kakarta da kanwarta Jeedah da suka zo daga kauye ._ *** *** *** *** *** _Zarah Kenan 'yar kimanin shekaru 21 a duniya ,tana karatun ta a babbar Université ta Abdu Moumuni Wadda take garin Niamey a k'asar Niger, sauran shekara biyu ta kammala tana da tsayi bâ sosai ba,fara ce tas tana da dogon hanci da kuma manyan idanuwa farare hancinta a Mik'e yake kamar biro, tana da yalwataccen gashin gira, ya kwanta lub ,bakinta d'an k'arami ne, gashin kanta bak'i ne gashi da tsayi har baya,kirjinta acike suke kamar an hura masu iska, yana yin jikinta irin na cikakkun mata masu kyan diri ne domin qugunta a matse yake masha Allah! Zarah ta had'u ako ina gâta da farinjinin samari da wuya tafito waje ba ta samu Wanda ya biyota gida bâ, ita kuma ba ta damu dasu bâ karatunta tasa agaba, shi ya sa wasu mazan suke shakkar yi mata magana domin sunce ta fiye girman kai da wulakanci, kad'an Kenan daga cikin labarin Zarah._