A lokuta da dama ƙaddara tana zuwar mana ba tare da mun shirya mata ba,na kasance ni mutum ne a rayuwata mai taka tsantsan sannan ni mutum ne da babu abun da na tsana a rayuwata kamar rashin tarbiyya. Tun da nafara girma nasan menene fari da baƙi,nasan ciwon kaina naji a rayuwata bazan taɓa iya auren macen da bata da tarbiyya ba,daga cikin abun da na tsana a rayuwata akwai SATA,na tsani SATA na tsani mai aikatata,Saidai kuma kash! duk yadda nakai ga tsanartata hakan bai hanani cin karo da WATA ƘADDARA ba wadda ta sanya na auri ƴar gidan SATA ma'ana ita yarinyace da ta ginu akan SATA domin kuwa babu wanda bai san mahaifinta ba indai shahara ne a fannin SATA sannan itama yarinyar ta gado halin SATAR.
10 parts