Ahankali tace " bari a shirya maka warm floral bath"
Wanan wani abu ne dayake ƙauna tun yana yaronsa,
Ta gama haɗa komi bayin ya gauraye da kamshin sabulan wanka masu tsada abunka da masu hannu da shuni.
Ganin bai tuɓe kayansa ba ya sanyata cire kunya, ta soma tuɓe masa kayan, shi kam mamakine ya kamashi, taruko hanunsa ta kaishi har bakin ban ɗakin ta juya zata fice ya ruƙota yana cewa " ya zaki gudu bayan baki karasa ladanki ba?
Ta ɗanyi yar dariya idanunta a ƙasa tace " zanje na shirya maka dining ne"
Ya ɗan saketa yana cewa
" Toh jeki saina fito, yau Allah ya ceceki"
Ranta fari tas ta gyare teburin cin abinci, tana jiransa.
Yafito cikin kayan bacci masu kyau na kamfanin max me kalar ruwan omo daya tura.
Tare ta zuba musu komi, sunaci suna hira yana santi, ta sake tanata shagwaba da hira irin ta jan hankali, sun zauna a falo sukayi kallo yaran suna tareda su,
Ta faɗo falon tana huci , a ka ta tsaya musu
Ta musu kallon wulakanci kafin tace
" Ashe ka dawo ina ta famar jiranka zamuyi magana"
Ya dubeta ya watsar kafin yace " eh nadawo tun ɗazu ai"
Ta cigaba da tsayuwa ganin bazai tanka mata bama wasa yakeyi da yarsa a kan cinya, wacce tayi kyau mul mul da ita, sai yanzu ma tayiwa ɗiyar kallon ƙwarai, ashe dashi take mugun kama,
Azafafe tace " magana nakeso nayi dakai!
"Kunne ne yakeji ai ko?
Ya ce da ita, baidaina wasan da yakeyi da yarinyarsa ba.
Yau ta yadda da abinda boka ya faɗa mata komi ya ƙare, hakqn kuma na nufin rugujewarta acikin gidan.
" Yaya zanyi nayinmaganar sirri dakai acikin mutane?
Se a lokacin ya ɗago ya dubeta yace " iyalina ne mutanen?
" Ashe baki shirya magana ba toh"
Kansa tayi tana masifa
" Yaya zakace nayi magana agavan wata banza jaka, ƙaramar yarinya mummuna, wacce kace bama sonta kakeyi ba ubanta ne ya maƙala maka ita"
Khulsum tayi iya ƙoƙarinta gurin shanye zancen amma takasa
" Eh gwara ni ai da mutuncina aka bashi ni koda baya so, kefa daya tsintoki a bariki duk yan mazan abuja sun cinye sun bar masa suɗi"
Kukan kura tayi tayi kanta, itakuwa daman a shirye take,
Sede yayi ta maza ya ajiye farhan da wuri, ya damki ramlat, tareda tureta gefe yana masifa
" For god sake meye hakane, agaban yara wanan wace irin ɗabia ce haka"
Ita uwar baki seta fara zaginsa
" An shanyeka dole ai kace haka, yarinyar tayimin rashin kunya kuma ka hanani magana, ko dukanta na farfasa bakin shegiya"
Cikin tsawa yace " karki ƙara cewa matata shegiya wallahi zakiji jiki"
" Au akan wanan matar da aka kakaba maka ɗinne zaka min butulci?
Yace " wanan da kenan, danayi kuskuren sonki da kaunarki that was the biggest mistake danayi a rayuwata, yanzu inason matata dn ta kasance mata ta gari, khulsum ta sayi soyayyarta aguna da halaye nagari, ke kuma kika watsar da taki da halayen banza, na bauta miki iya bauta, nasoki iya so amma kinyi biris da hakan saboda haka ki barni naso wacce zata kyautatamin, ta kuma samamin ɗiya nagari"
YOU ARE READING
ZABEN TUMUN DARE
RomanceMafi yawancin lokuta zabin zuciyarmu shi mukafi kanbamawa, Bama duba mai zaije yazo, a kasar Hausa mukan bawa abu guda shaida kuma haka zamuyi ta bibiyar abun nan da shaida marar kyau bazamu taba la'akari da bangare mai kyawu ba na abin, dayawa daga...
ZAƁEN TUMU 38
Start from the beginning