Mai Unguwa ya karɓe zancen da, " Ƙyaleshi shi da ya san zafin ƴa kenan, wato tsagerancin ka Auwalu har ya kai ka samu a gaba kana cin zarafinmu, Eh ai ka ganmu a tsaye kafaɗa da kafaɗa dole ka gaya mana san ranka. "

     Abba baibi ta kansu ba ya juya yabi gurin da ya hango Yusra zaune tana kuka da niyyar yayi mata magana ko zai samu ta amsa masa.

       Daga gurin da suke zuwa gurin da Yusra take zaune tafiyar da ƴar tazara, Abba ya kusa ƙarasawa gurin Yusra Mai Unguwa ya kalli Alhaji Babba ya ce, " Kai Yaron nan fa kar ya samu mafita ya fice ya barmu a gurin nan " Alhaji Babba nazari yayi ya ce, " Wallahi Tanko zancenka na hanya " kamar haɗin baki su Alhaji Babba suka rufawa Abba baya.

        Umma na zaune jigum kamar wacce aka zarewa laka haka ta haɗa kai da gwiwa, Shatu jinjina kai tayi ta koma gefe ta zauna a koda yaushe tana haƙuri akan irin rashin adalcin da ake mata, ammz wannan karan gani take haƙurinta kamar yazo ƙarshe, a saninta dai itace da miji ranar amma bata da kataɓus anmaida ta kamar marasa ƴanci a cikin gida, kallan Umma tayi ta ce, " Saratu ki tashi kije naji Alhaji yace Auwalu ya dawo kije kiji halin da yake ciki ki tambayi halin da suka shiga. " Tausayin Shatu ne ya kama Umma saboda ta lura yanayinta yana cikin damuwa, ko ba'a faɗa ba kowa yasan irin zaman da Shatu ke yi a cikin gidan, sai dai kowa xargin da yakeyi ba banza akabar Alhaji Babba ba tunda a zamansu na baya ba haka yake ba, yana nuna mata kulawa dai-dai gwargwado da saɓanin yanzu da bata da wani galihu a gurun.

     Umma jiki a sanyaye murya ƙasa-ƙasa ta ce, " Shatu ni wani abu ne dana gani nake jin shakku a zuciyata " da mamaki Shatu ta ce, " Shakkun me Saratu? " Umma sai da ta ɗaga kai ta leƙa bakin ƙofar Falmata sannan ta ce, " Nifa Yaya Alhaji ne naga babu kunnuwa a jikin kansa, baki lura da gurina shafe yake ba? " Zaro ido Shatu tayi tana dafe ƙirji ta ce, " Ke Saratu yanxu Alhaji ne babu kunne a jikin kansa? "Sunkuyowa Umma tayi tana ƙara ƙasa da murya ta ce, " Wallahi haka idona ya gani amma bansani ba ko idona kemun gizau " Shatu jinjina kai tayi har zuwa lokacin da mamaki bayyane a zuciyarta.

   Falmata suna shiga cikin ɗaki ta zaunar da Alhaji Babba a kan gado tana faɗin, " Sannu Alhajin Allah, wai ni meye gaskiyar maganar ne? Ance wai ɓacewa kukayi, nifa wallahi dama inada ɗan zargi akan sheɗaniyar yarinyar nan da uwarta, dama tana fama da ido ya na tsohuwar mayya "

    Alhaji Babba gwalalo mata idanu yayi ya kafeta da kallo baice mata uffan ba sai dai yanda ta lura da fuskarsa gaba ɗaya ta sauya alamun baiji daɗin maganarta ba, ɗauke kai gefe tayi tana jan guntun tsaki ta cigaba da cewa.

     " Wai Alhaji ba magana nake ba kayi shiru, wai ma ya aka kaya ina ita wannan koɗaɗɗiyar yarinyar? " ta ƙarasa faɗa tana zuba masa ido domin taji abinda zai ce mata.

    Alhaji Babba lanƙwasa kansa gefe ɗaya yayi cikin wata irin dakusashshiyar murya ya ce, " Wannan ta zama kalmarki ta ƙarshe da zaki furta akan Yusra, Idan ba haka ba kuwa..." A zafafe ta ce, " Inba haka ba me? Me zakayi mun? Lallai da aiki kenan a gaba na. " Uffan bai ce mata ba, sai sunkuyar da kansa ƙasa da yayi, yana ɗagowa yasa hannuwansa biyu ya riƙe wuyansa.

Falmata sai lokacin ta lura da kansa babu kunnuwa, da sauri taja baya har tana buguwa da jikin drower, cikin tsoro ta ce, "Alhaji Ina kunnuwanka? " Alhaji Babba ɗagowa yayi da gwalagwalan idanunsa ya ce, " Ina ruwanki da kunnunawa na? " tun daga lokacin Falmata tasha jinin jikinta, tana nan tsaye tabi Alhaji Babba da kallo, sai gani tayi ya fara wulwula kansa da hannuwansa, kansa ya koma ƙeyarsa sai ƙeyar da dawo goshi.
     Falmata jikinta ne ya hau tsuma da karkarwa saboda tsabar tashin hankali ji tai yawun bakinta ya ƙafe, har zuwa lokacin bai daina juya kansa ba tun yanayi a hankali har ya cigaba da yi da sauri kamar mai juya garai-garai,tana nan tsaye taji fitsari na bin jikinta gabanta sai faɗuwa yake.

      Dabara ce ta faɗo mata a hankali ta fara takawa zata wuce ta fita, bai fasa abinda yakeyi ba cikin wata irin murya ya ce mata, " Ina zaki? "

     Falmata cikinta ne ya yamutsa tayi ƙarfin halin cewa, " Ammm dama, dama  ruwa zan ɗebo maka " Nuna ta yayi da ɗan yatsa take aka janyota aka makata da jikin bango, hura bakinsa yayi akan gado take ruwa ya fara fitowa daga bakinsa kafin wani lokaci ruwa ya cika saman katifarta, tsaida wuyansa yayi a lokacin ƙeyarsa ce a gabansa fuskarsa na bayansa, nuna ruwan kan gadonsa yayi ya ce, " Ina da ruwa wadatacce agurina idan kina buƙata kema zaki iya ɗiba ki sha, ina zaki tafi tare da kin sauke hakkina a kanki ba? " Falmata na jin haka gabanta ya yanke ya faɗi cikin razana ta ce, " Alhaji wai yau me yake damunka ko tsaface ka sukayi ne? " tana gama faɗa sai jin saukar bulala tayi a jikinta, tana shirin kurma ihu taji ƙofar ɗakinta ta rufe da ƙarfin gaske.

     Su Umma da ke tsakar gida basusan budurin da akeyi ba sai ihun Falmata da sukaji da yanda ƙofar ɗakinta ta banke da ƙarfin gaske.
      Zabura sukayi lokaci guda kowacce na shirin neman mafin sakamakon jin wata irin razananniyar dariya, gashi har zuwa lokacin basu daina jin kukan Falmata ba.
      Da gudu suka tashi zasu faɗa ɗakin Shatu har ana rige-rige a tsakani har Allah ya bawa Umma nasarar faɗawa daƙin ta banko ƙofa Shatu na tsakar gida, iya ƙarfinta take buga ƙofa tana roƙon Umma akan ta taimaka ta buɗe mata itama ta shige.

     Saboda tashin hankali Shatu batasan zaninta ya faɗi ba tun miƙewarsa daga ita sai ɗan underwear, Umma da sauri ta buɗewa Shatu ƙofa suka maida ta suka rufe kowa na maida ajiyar zuciyar.

INA MUKU FATAN ALHERI🌚

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_

WANDA BAI JI BARI BA....Where stories live. Discover now