Ya zauce ya gigice akan ta wai ta yafe masa ta dawo gidansa, har iyayensa saida suka zo gidan amman ta murje idonta tace wallahi ko shikadai ne namiji a duniya ta yafe, sai lokacin iyayen sa suka san da abunda yake faruwa duk da can da yake cusa mata bakin cikin nasu san da ita ba sai yanxu da d'ansu yake neman haukacewa, haka suka tafi badan sun hakura ba anyi haka ba jimawa sukaje super market siyayya acan suka had'u da Ishaq, yaron mai matukar natsuwa da hankali gashi kyakkyawa, matar sa d'aya da yara biyu kuma na kyautata ma matar tashi don har waya suna d'anyi da ita, har yaran saida ya kawo mata.

Nai murna da wannan auren kowa yana saka ran zata zauna kuma shima zai rik'eta yadda dai akaga yana kula da dayar matar tashi, tunda na dawo aka hau mana gyaran jiki ba ranar baza da baza'ai mana wani abu ba, tuni har an kawo lefen yaya yusra set biyu  masu masifar kyau, ni kuma nawa sai gab biki aka kawo su set biyu nima kowa yana yaba wa duk da annur ba aiki yake ba amman sunyi kokari dashi da su Abban.

Tunda aka fara mana gyara na rikice wani irin feelings kamar zasu kasheni, na dauka ni kadai nakejin hakan saida mukai maganar da yaya yusra tace, "naki wasa ne yarinya, nifa bana iya bacci duk randa nai doguwar waya da Abban sameer, ciwon mara kamar zai kasheni"

Nace, "aini bana yarda ma muyi waya data wuce  minty biyar da Annur don in na sake muka haura haka ranar saina dan dana kudata,"

Dariya tayi tace, "shiyasa naki yarda yazo don bansan ya abun zai kaya ba"

Mukai ta dariya a haka mai gyaran ta iske mu aka cigaba daga inda aka tsaya, ita yaya yusra anfi yi mata na matsi sosai ni kuma na ni'ima yafi yawa, shiyasa dan danan zan ta zuba da farko ma tsoro naitaji sai daga baya na dayaye, ga turare da ake mana safe da yamma gaskiya muna shan gyara.

Ana jibi biki ya kirani yake mun albishir cikin doki da murna nace, "Besty gaya mun menene don Allah"

Yace, "Abby ya bani aiki company sa kin san yai mun cuku cuku na anshi result dina, shine ya bani opper sabon company sa dazai bud'e bayan biki da kwana uku, nine shugaban wajen gaba d'aya Baby kiyi taya ni godiya don Allah"

Nace, "kai ma ai mahaifinka ne Besty inyayi maka kamar ni yayi mawa, karka wani damu indai Abby ne tamkar ni haka ya dauke ka don niban san ma zai bude sabon company ba sai bakin ka, ina taya Besty na murna Allah yasa alkairi"

Yana dariya yace "Ameen babyn Besty, Allah dai ya kaimu jibi lafiya ga sabuwar amarya ga sabon gida ga sabon aiki, waya kai annur farin ciki"

Dariya nai masa nace "to sai anjima"

"Shine zaki gudu ko? Ko yar firar nan ta marmari bazaki tsaya muyi ba"

Nace, "To me kakece na baka na zuba ba kace jibi bane"

Yace, "jibine fa,kuma ba mai kwanan mani wallahi in b'arje gumina son raina inzo inyi lallashi kuma"

Saidai yaji kittt na kashe wayar, ai ba abunda ke tada mun hankali irin wannan ranar don bansan ya zata kaya ba.

Sham ta gayyato kawayen mu sosai nai mamakin har da suka samu zuwa, aiko naji dadi sosai ba wani event da na shirya walima ce mukai a gida ta gaba daya dangi, kuma abun yai kyau karma ace dai mu amare, sai walauniya muke ranar juma'a su Annur da abokan sa suka iso hotel ya kama masu don su zauna, sunzo har gida akai hotuna akaci akasha duk yadda yaso mu keb'e k'iyawa nayi, don nasan me nake ciki yadda nake kan gab'a nan idan ya tab'ani za'a samu mishkila.

*******

*ALK'AWARIN ALLAH YA TABBATA*

Ranar Asabar da misalin karfe shad'aya na safe aka d'aua Auren YUSUF HUSSAIN KALLAH DA MARYAR SA SAFRA'U NURA, akan sadaki dubu dari biyu da yake duk cikin masallaci guda aka daura, ana gama na yaya yusuf akai na yaya yusra.

YUSRA HUSSAIN KALLA DA ANGON TA ISHAQ INUSA akan sadaki naira dubu d'ari sai aka daura namu NAJA'ATU HUSSAIN KALLAH DA ALIYU ALIYU TAHIR akan sadaki dubu d'ari da hamsin, daurin Auren yayi mutane sosai har ma wanda bamu zata ba sunzo sosai, sai fatan Allah ya zaunar damu lafiya da zuria d'ayyi ba, ana yin salar azahar aka tafi kai yaya yusra saboda itace nesa dagida sosai, aiko nida ita munsha kuka kamar aurenta na farko.
Munaji muna gani mun sake rabuwa, rabuwar da ake saka ran anyita kenan saidai ziyarar juna inta kama, bayan an dawo kaita aka tafi dauko ta yaya yusuf da yake gidan sa nan cikin unguwa ne ba wani nisa, aka kawo masa matarsa sannan aka fara shirin tafiya dani, ban zaci zan yi irin wannan kukan na rabuwa da Ammi ba saida naga dagaske dai tafiya za'ai dani, ai da yawa sun tausaya mani yadda na rik'e ammi daker aka cireni jikinta karshe dai saida naga likita bayan an kaini saboda azabebben zazzabi ya rufe ni harda su karin ruwa, kowa ya tausaya mani don shakuwar mu da Ammi takai har takawo ba wanda ya shak'u da ita cikin ya'y'anta irina, dole zamuji ba dadi irin wannan ranar.

Annur dake cewa zai kori yan biki sai gashi ba yadda ya iya saida aka kwana, washe gari akai walima sannan kowa ya watse aka barni dagani sai halina kawayena daman tun ranar auren suka tafi, sham kawai aka barni da ita sai wata yar unguwar mu, duk nai sukuku tsoro da fargaba kawai ne ke lillib'e dani har sadda abokan sa suka rakoshi watau Hamid da Bilal, abokai na amana kenan inajin shigowar su gabana yai masifar fad'uwa....................





Mom muhseen✍🏻

FRIENDSHIP (A BOTA)Where stories live. Discover now