Page .....46.....

Start from the beginning
                                    

Kallon su mu'azzam din take cikin bacin rai kafin ta koma kan Ahmad din ma.

"Abinda nakeji gaskiya ne,sumayyah ta bata dagaske,yanxu duk abinda ta shiga saida aka rabata da gida,tun ba kai ba yah mu'azzam matanku su suka hada wasu abubuwan"

Kowa kallonta yake har abban shima,ita kuwa ko a jikinta tafara magana,tundaga abinda taji suna fada ran auren sumayyah da kuma zigon da sukeyiwa maryam.

"Bazaku san sanjawar sumayyah ba sai kunga yanda take takura kanta da saka kamta a kunci a gidan Ahmad duk dan kuyi farin ciki abbah.

Su antu Maimuna da humairah sun sha zuwa gidan su cimata mutunci son ransu,sannan su jigaku ku hau ku zauna,komai suka fadamuku tayi sai ku hau ku zauna ku ga masu mata,idan nayi kokarin zuwa na fadawa hajiya mama sai tace ranki zai baci.

To Bayan tafiyata ma nasan abubuwa sun faru da dama,wln ancuci baiwar allah,abu daya tayi aka mata miliyan,tunda abinnna yafaru babu wanda ya taba tunanin yar adam ce tana bukatar abubuwan rayuwa,wani lokacin ni take roka kudi idan ya kure mata,idan kuma naga takasa roka na bata,wani lokacin kuwa sai tacemin babu abinda take bukata,kuma nasan dan karta tambayeni ne lokacin da take gidan Ahmad din ma mai yataba yimata a gidan,mijina ne ya biya mata kudin makarantar ta na farko,na biyu kuwa kin fadamin tayi ashe kayan dakinta ta siyar ta biya kidin,sannan ta shiga sana'a da sauran kudin,abinda ko wamda baku sanshi ba zaku iya masa,amma haka abubuwa da dama sukafi karfinta a rayuwar nan, saida aka bari ta samu sana'a ta fara dogaro da kanta yanxu kuma an dora mata sharri an jefata duniyah,wannna wace irin rayuwa bace allah yasa ma zuciyarta bata buga ba ta mutu,waya san yanzu wane hali take ciki"

Cikin masifah ta rufe ido take zazzago masifarta son ranta,ko girmansu a lokacim bata ganiba,bacin raine yake cinta sosai,saida tagama kafin ta fashe da kuka ta bar gidan tana fadin,

"In allah ya yadda zan bincika duniya inshaallah saina nemo sumayyah,rayuwarku kuwa tafita ma yanda kuke so din"

Da sauri tabar gidan tana gunjin kuka ta shiga motar ta tareda figarta da karfi,ikon allah ne kadai ya kaita gidansu.

Yanzu dakin yayi shuru ihun hajiyah mama ne kadai tana a fito mata da yar ta,dan dataji abinda bata saniba wanda yar ta take ciki bakaramim harzuka ta yayi ba,kara rike akwatin yah mu'azzam yayi,dan shi yake ganin tashin hankali.

"Ka shikamin akwatina bazan kwana a gidannan ba,ku masu mata sun rabaku da yar uwarku,saiku zauna dasu yanzu hankalimku ya kwanta,sun maidaku gararori,su haka sukeyiwa yan uwansu,ku a ganinku wato sun fi sonku fuyeda yar uwarku koh,abu kadan zatayi ku tunzura ubanku yana jigaku ku yi mata dari,toh wlh kar wanda ya nemeni in ba samota kukayi ba,matannaku kuma zakuga yanda zaku kare dasu"

Fisge akwatinta tayi tabar gidan da sauri,sakawa tayi a cikin motar tareda cewa ya kaita gidansu,abin mamaki ya bashi saida tasake magana.

"Ka kaini zariya gidanmu nace,ko baka jine?"

Shiga motar tayi suka ja sai tafiya.

Bin bayan motar yah mu'azzam yayi da kallo tareda sauke ajiyar zuciya,ko ta kan abbah dayake tsaye bai bi ba da kuma Ahmad wamda shima yazama mutun mutumi,motarsa ya dauka shima yabar gidan.........

A kwance take da wata riga a jikinta yar doguwa mai kalar sky blue,da alama ta asibiti ce.

A kan wani gado take duk kanta wayoyine wanda suke jinkin na'urah.

Daga ganin kayan aikin wajen da yanda fararen fata suke jirga jirga kasan wajen ba kasarmu bace ta hausawa.

Wata matace a gefenta fara mai yar kiba,amma kalar fatar mu ta yan Nigeria,magana suke da wani mai fararen kaya inda yake fada mata yau zasu daga ta daga kan na'urar,abin bashida worse sosai dam haka sati daya ma ya isa.

KAICO NAHWhere stories live. Discover now