Part 1

18 1 0
                                    

               🏜️ WATA ALKARYA 🏜️

*Daga Kundin ✍️📚✍️
*Alkhamis KSA*
Wattpad: @KhamisSulaiman
Whatsapp: +2348095933008

Bismillahir rahamanir rahim wa sallallahu allan nabiyyil karim wa ahlihi wa sahbihi wa sallam.

Dukkan godiya ta tabbata gun Allah sarki guda daya mai kowa mai komai wanda ya bani ikon fara rubuta wannan sabon littafi mai suna WATA ALKARYA. Tsira da aminci su kara tabbata ga Shugabanmu masoyinmu Annabi Muhammad S.A.W. wanda duk wani abu da muke muna yi ne a cikin albarkacinsa.

Wannan littafin na WATA ALKARYA yazo da sabon salon Jan hankali da kaguwa yasha bamban da sauran littafai na. Ban rubuta shi don cin zarafi ga kowa ba idan kaga wani yayi daidai da kai to kayi hakuri kamanceceniya aka samu.

Ban yarda wani ya daukar min littafi ko ya dauki wani bangare na yayi amfani dashi ba tare da izinina ba.

                            *page 1*

   Sarauniya Mundila tana zaune a bisa karagar milkin kasar Dizhwar, zaune take ranta a bace dalilin da yasa fadar tayi tsit! kamar wajen da aka yi mutuwa, dama kuma kowa tsoronta yake saboda Sarauniya Mundila ta kasance azzaluma ce kuma mai tsattsauran ra'ayi, gata dai mace ce amma hakan bai hana ta cin zarafin al'ummar kasarta ba. A yanzu ma da take zaune ranta a bace ba komai bane ya bata mata rai face rashin ganin data daya tilo Yarima Harzik, wanda ya fita daga gida kimanin kwana biyar kenan, ya fita ne da niyyar zuwa farauta kamar yadda ya saba amma sai gashi bai dawo ba har kwana biyar, kuma tunda aka haifeshi bai taba kin kwana a gida ba koda kuwa sau daya, Sarauniya Mundila ta tura nemansa duk inda zata iya amma babu labarinsa wasu wadanda suka tafi nemansa ma basu dawo sunce mata komai ba, babu su babu shi, su kuwa sun ki dawowa ne saboda kada su dawo suce babu labarinsa sarauniya ta azabtar dasu, shi yasa suka bata a duniya idan suka ji labarin ya dawo suma sai su dawo.

       Yarima Harzik jarumi ne na gani na fada har ma da nunawa, kyakkyawa ne matuka gaya kuma fari ne tas akwai alamun kwarjini a tare dashi, ya kasance ma'abocin zuwa farauta ne duk da cewa ya tashi a gidan sarauta kuma dan sarki amma hakan baya hana shi zuwa farauta, kullum yakan tafi tun asubar fari ba zai dawo ba sai la'asar sakaliya, idan ya dawo yakan zauna tare da babarsa Sarauniya Mundila cikin turakarta da daddare su raba dare suna hira.

      Har dai aka tashi daga fada sarauniya Mundila taba ga Yarima Harzik ya dawo ba, kai har dare yayi sai can sai gashi ya dawo, dama sarauniya kullum sai ta cewa kuyangi komai dare in dai ya dawo a  shaida mata zuwansa, ai kuwa yana dawowa sai wata amintacciyar kuyanga taje ta shaida mata zuwansa, take tace a kira mata shi, koda taje gareshi sai korota amma data koma sai tace mata yana zuwa, don dama haka yake yi idan ta aika a kira shi sai korosu wani lokaci ma yace ba zai zo kuma sai yaje, shi yasa ita kuma taje tace gashi nan zuwa, duk kuyangi da bayin cikin masarautar sun san halin sa, kuyangar nan tana fita kuwa sai gashi yazo ya zauna nesa da ita yayi shiru ransa a bace.

     "Wai meke damunka? kuma ina kaje? kasan rabon dana saka a idona yau kwana biyar kenan, baka kwana a gida, babu labarinka" Sarauniya Mundila ta fada tana kallon Harzik tana masa kallon neman amsa.

      "Abinda yake faruwa ranki ya dade! yau kwana biyar da suka wuce ina cikin tafiya a hanyata ta dawowa gida daga farauta, a iyakar kasar Kishwar da kasar nan akwai wani karamin kauye mai suna Kanash, a daidai nan na hadu da wasu 'yam mata guda biyu babba da karama sun debo ruwa daga rafi, yaran idan kika gansu kamar su daya kamar an tsaga kara, ina ga ko dai tagwaye ne ko kuma yaya da kanwa ne, ina hada ido da babbar sai naji gaba daya tunanina ya kafe, kwakwalwa ta jirkice, jinin jikina ya tsaya, hankalina ya gushe, zuciyata ta faskara ta bijiro min da wani abin arziki wanda zan iya gaya mata ta yarda dani a cikin zuciyarta, nayi ta kallon su har suka wuce na kasa ce musu kala. Bayan sun tafi na daina ganinsu sai na tsinci kaina da kasa dawowa gida, nayi ta zama a gurin har dare yayi gari ya waye rana ta fito sai da rana ta kusa faduwa sai gasu nan sun zo zasu wuce su tafi debo ruwa kamar kullum nan ma na kasa cewa dasu komai har suka wuce suka debo ruwan suka dawo suka kuma tafi gida na kuma tsayawa dare ya kuma yi gari ya waye ina wannan wuri har suka zo suka zo suka wuce amma na kasa ce musu uffan, haka nayi tayi tsawon kwana biyar dinnan da kyar na taho gida shine nazo nan na takure guri daya na rasa abinda yake min dadi, ina ta tunanin hanyar da zan bi naga na samu karbuwa a gurin wannan kyakkyawar yarinya!"

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Apr 01, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

WATA ALKARYA Where stories live. Discover now