[5/20, 3:20 PM] 💄Meryerm Abdool💄: 🍇🍇🍇🍇 🍇🍇🍇🍇 *HADUWATA DAKE* 👉🏻🍇🍇🍇

430 18 0
                                    

[5/20, 3:20 PM] 💄Meryerm Abdool💄: 🍇🍇🍇🍇
🍇🍇🍇🍇 *HADUWATA DAKE* 👉🏻🍇🍇🍇🍇
🍇🍇🍇🍇

( _Base on love story_ )

Story by:-
💄 *Meryerm Abdool* 💄

Edited by:-
*Maman Usseey* & *AAJ*

        *page* 5-6

2 days later.........
Haydar ne tafe cikin car din'shi,Fuskarshi kunshe da annuri,Daka kallesa xaka fahimci yana cikin farinciki...
   
" Sannu a hankali yake driving,Yana biyar music din' da ke tashi cikin car din ,hade da daddadan kamshi  dama *Haydar* akwai son kamshi....
        
    A haka ya karasa cikin school d'in, yana danno hancin car d'insa,Attention din students ya koma Kansa.....Ihu kawai sukeyi suna fadin,D one  hannu kawai yake daga musu

  Dai2 faculty d'insu yai parking ya fito, Sanye yake da jeans black sai red top Mai ratsin black nd white,suman nan sai  kyalli take alaman tasha gyara .     
   Hannunsa rike da tab d'insa yana dannawa.
       Bayan car dinsa yaje ya zauna,Snn ya dauko phone dinsa ya danna digit din Saleem...tuh.tuh.. Saleem ya daga sannan yace"yane D one koka karaso ne.....??

   Shuru yayi kamar ba waya yake kamin nan yace gani waje. (Sarkin jan Aji kenan).

" Ganinan xuwa cewar Saleem"  gyara zaman eye glass nashi Yayi ya tsare gida sosai Almar bawasa.

"   Fitowar Saleem daga nesa ya hangoshi, dayake duk wanda zai fito daga Cikin Hall zai hangosa, Karasowa yayi ya bashi hannu suka gaisa.

"  Saleem yace ya naganka zaune guy ba karasowa zakayi bane..... ??

" Tabe baki yayi yana kallonsa,Nifa ba attending lecture naxoyi ba,cewar Haydar,(Dama sai yaga dama yake attending Lectures. Idan lecturer ya ganshi sau 2 a samister toko yanada sa'a sosai 😅).

_Fita zamuyi Kenan.....?? Cewar Saleem_

   " Nop yafada yana wani felling , Agric dept zamuje "

"  Ohhhhhh!! Nifa na dauka
kabar xancen.......Cewar Saleem

   Dago kai yayi ya kallesa yace what...!❓Zunubi kenan! ai idan kaga nabar wanan abu to ba *Haydar* Sunana ba.
   " Leem kenan...!! Some time kana magana kaman bakasanni ya karisa fadar maganar Ya fada yana dirowa daga motarsa.

" Murmushi Saleem yayi yace" maxah!!!
  Towai ma mexa'a Mata ne Don Allah...??
     Dafa kafadarsa yayi yace ka biyoni kawai kasa kallo guy......
      Daga kafada Saleem yai tare da cewa" to muje.... ko. 

  " A haka suka doshi Agric dept suna tafe cikin izza da tak'ama da an gansu sai a fice a basu guri (Ni kuwa nace kome xai yi wa silly *siddiqa* oho...! 🤔).

----------------------------------------

" Zaune suke cikin library wasu sunyi group suna fira, Yayinda wasu ke duba littafansu.
 
" A can na hango Siddiqa zaune kan seat book  ne rike a hannunta tana dubawa,

" Atampa ce a jikinta koriya saidan hijab fari mai hannu,Powder kawai ta Shafa sai lip protector amma duk da haka tayi kyau sosai.
 
   " Gefenta naga Shamcy ita kuma sai faman rubutu take  bags dinsu na ajiye  saman desk.......
    

" *Leeem da Haydar* ne suka Shigo cikin lab, din

  Nan take sowaa!! Ta tashi sai ji kake Ana *D one* karasawa yai wani group na big boy, hannu ya basu suka gaisa.

  " Jin Ana kiran D one ne yaja hankalin Shamcy tabo Siddiqa tayi tace ke fafa mutumen ki can......yazo wa kenan.....??

   "Ta tamvayaa tare da dago kanta ta dubi inda Shamcy ke na mata  Carap....idonsu ya hadu,murmushi yai Mata Wanda ta kasa gane ma'anarsa ba.
 
" Siririn tsaki taja sannan ta maida kanta ga book din' ta.bata kawo komai a'ranta ba da yake ya Saba shigowa..
  
  "  Wata yarinya ya tsinka can baya daga yanayin shigarta kasan ba natsuwa a tare da ita, da  hannun ya yafito ta alaman tazo...aiko abin nema ya samo dama Meena ta Dade tana sonsa,badai dama ta tunkareshi ne.....

    "Abin nema yasa mu jiki na rawa ta isa gurinsa  gefe ya koma  yabar leem gurin fans dinsun nan..
  " Kallonta yayi tare da yatsine fuska awa yaga kashi sanann ya fito da bandir din en #1000 ya danka mata hannu na rawa ta ansa tana washe bakinta Mai Kama Dana jaba.......😜

" Sannan ya fito da wata er karamar bottle daga Aljihunsa  ya baiwa meenah abin ciki jane Zare ido nayi tare da cewa
(What...!😳. Blood da Sauri na Kama bakina kada yaji🙊ya mareni.......Amma Ina ta mmk me xaiyi dashi?? Koda yake gani xanyi innasa hakuri) Lol😉

" Kallon meenah...! yayi yafara magana  cikin voice dinshi Mai sanyi yace mata.

"Aiki zan baki kuma don't ever try to mistake me so nake at any cost ki zuba ma wancen yarinyar ya fada yana nuna Mata Siddiqa........  kallon gurin da ya nuna mata tayi sai tace dashi.
  
Wai *Siddiqa* kake nufi  tamke fuska yayi sanan yace koma meye sunanta bandamu ba,kawai ki saka Mata shi yai kaman tayi staining, Idan aka samu kuskure to kinbar sch dinnan kenan....
  Da sauri tace a'a bama za'a  samu ba ranka shi Dade da hannun yai Mata Alaman ta wuce sannan ya koma gunsu Saleem.....

"Meenah kuwa dadi uku ne ya hadewa Mata ,na farko dama ta tsani siddiqa Coz of kyanta da kokarinta , na biyu  ta samu kudinda bata taba rike wa ba a rywrta,na uku yau itace gata ga D one wai har yai magana da ita,wayyo dadi kasheta Anya xata iya bacci yau kuwa...🤔
 
" Karasa tayi gurinsu Siddiqa tayi  kaman wani Abu take nema a kusa dasu . *Siddiqa* wadda ita batama San da zuwanta ba Coz hankalinta na gurin text book dinda take karatu.

Sannu a hankali  meenah..!ta bude bottle din ta zuba Mata daidai mazaunanta, Abinka da farin hijab nan take ya fito sosai kaman tayi staining.......
    Da Dan sauri Meena tabar gun ta koma gurinta tana dariyar aranta.....cewa take yau zakici kunya matsiyaciya!!!
    Bayan 2mn shamcy ta mike tana cewa wash...."na kare da kyar besty,tashi muje mu samu  mu karya ko....??ta fada tana hada littatafan su  tasa a bag.

" Mikewa Siddiqa itama tayi ta maida book dinta a bag sanan ta sagala tace "muje acici"
    " Cewa tai ai da gaskia na, tunda ba irinki nake ba marar  son  cin abinci...

"To naji muje nidai kada kisa min kuka"

"  Daria shamcy tayi sanan tace kinsan  "shi yafi komai sauki  ko awajenah....!"

    " Ai nasan xaki aikane" Siddiqa ta fada suna tafia...

"Saida suka kawo tsakiyar lab din sannan Meena tai magaana  da karfi tace  *Siddiqa*meye haka a hijab dinki.....???

" Wayyo Allah!!!!🙈Aiko Attention din kowa ya dawo kansu Subhanallah..!  shine abinda shamcy ta fada cikin kaduwa.....Siddiqa kam daskarewa tai anan.

" _Kunya,Takaici,Bakinciki sune suka rufeta ta kasa motsawa_
   
Da murmushin mugunta ya karaso inda suke sanan yace"keko wace irin village ce......? Kinsan kina cikin wannan yanayin. Imagine baki masan yadda zaki kula da kanki ba.....??

  " Any way ya kamata ki rinka kulawa SBD Tsaro..! Ya fada yana kashe Mata ido daya tare da scrolling yatsushi Alaman bye.....

_wayyo tsananin tausayin Siddiqa yasa Al-kalamina ya fadi_ 😢😢

Frnd Ina Neman Addu'arku Ina mafa da mura😤😤😤

Taku

  💄Meryerm Abdool💄

HAD'UWA DAKEWhere stories live. Discover now