SIRRINTACCEN SO

6.2K 131 68
                                    

*💞SIRRINTACCEN SO💞*

*Nagarta Writers Ass0....*

*Written by Mum Irfaan*
*Follow me on wattpad-MumIrfaan*

*SHAFI NA 1⃣*

*_Bismillahir-rahmanir-raheem_*

Aguje ta shigo cikin gidan tana faman fad'in "Inna! Inna!!" kamo Innarta tayi kamar wacca zata shige cikin jikinta tana faman yin huci, la'bewa tayi a bayanta tana faman rarraba idanu, shigowa yayi ranshi a 'bace yana kallanta yadda ta lafe bayan Innar, nunata yayi da yatsa yace "Wallahi ki shiga taitayinki kinji na fada miki, tunda naga ba abunda kika saka a gaba sai wasa da maza, ke namijice da zaki runka wasan maza, bakyajin magana ko?"

Tana lafe a bayan Innarta tana d'aga mai kai tamkar wata 'kadangariya, cikin siririyar muryata tace "Dan ALLAH yaya kayi hak'uri bazan k'ara ba, dama su Dayyabune sukace muzo muyi 'yar wasan gudu, kuma saida nace mai ka hanani yace ai lokacinmune inhar banyi yanzu ba nan gaba inaso ina ganin bazan iyaba saboda na tsufa, shiyasa ni kuma nace da ace saina tsufa zanyi sha'awar gwara inyi yanzu idan yaso sai na bada labarin tawa kuruciyar"

Kallanta yayi yana zabga mata harara yace "Wannan k'uruciyar hauka kike bata yara ba, kuma kinji na fad'a miki inhar na kamaki kina fad'a da maza to ki sani saina zaneki, babu mai k'watanki a gidannan, mtswwww" wucewa d'an madaidaicin d'akinsa yayi yajiyo muryarta tana fad'in "Yo in banda abun Yaya inaji rannan ana fad'an taka k'uruciyar kai har dambe ma kake da mata" tana fad'an haka ta zura a guje ta shige d'akinsu, babu inda ta dosa sai k'ark'ashin gadon k'arfen Innarta ta 6oye dan tasan had'uwarsu da shi bazai mata da dad'i ba.

Giriza kai kawai yayi yana mamakin karfin hali irinna HIBBAH, sai d'an banzan tsiwa amma akwaita da tsoro, zama yayi a 'yar katifarsa wacca ta yamushe dan tsufa, dauko manya manyan text book yayi ya duk'ufa wajan karantasu.

Inna tana zaune tana faman kai rogo bakinta taji motsi a k'ark'ashin gado, tasan ko ba'a fad'a mata ba HIBBAH ce, girgiza kai tayi tace "To malama saiki fito ko, uwar tsokana kawai da ita, wallahi ba abunda ya shafeni, tunda ke bakyajin magana, wani irin juyin duniyane banyi dake ba akan kidaina wasa da maza amma kink'i, to bari kiji daga yau na daina bama yayan naki hak'uri gwanda ya nad'eki yadda yakeso kinga gobe bakya kuma ba"

HIBBAH fitowa tayi daga k'ark'ashin gadon, tana ta faman karkad'e jikinta tace "Yo Inna bisabilillahi a hanani wasa da sa'annina, shikenan ba daman inji dad'ina sai an takuramin, yoni ba auta bace a wanga gida ba?, to gaskiya a barni nad'an mori tawa k'uruciyar"
Zama tayi kusa da Innarta tana kallanta tace "Inna kima girman ALLAH ki fad'amin k'uruciyar yaya, kwarankwatsa bazan fad'a masa komai ba, kuma bazance ke kika fad'amin ba, so nake kawai naji tashi k'uruciyar" wangale baki tayi tana kallan Innarta da wani wagegen gi'binta.

Inna kawar da kanta gefe tayi tace "Tashi kibani waje, kinsan ALLAH ki kiyayeni da wannan tambayar taki, waike ba tun d'azu nace kije kimin wanke-wanke ba kika aje kika tafi wasa ba?"

HIBBAH tuno d'an k'aramin bakinta tayi tace "Inna na fad'a miki gaskiya kwarankwatsa ban iya wanke-wanke ba, kinga rannan ma yayane ya wankemin nace nice" ta fad'a tana washe baki.

Inna tace "Wallahi, kinji na rantse saikinyi, a haka zaki koya, tashi ki 6acemin da gani kafin na kira SADIQ yazo ya zanemin ke"

Zunbur HIBBAH ta tashi ta nufi tsakar gidan danyin wanke-wanke, zamanta keda wuya saiga Imran ya lek'o tsakar gidan yakoci sa'a ita kad'aice a wajan, cikin murya k'asa-k'asa ya fara kwalla mata kira yana fad'in "Hibbah!!!"

Hibbah tana ta faman d'an rera wak'arta batasanma ana kiranta ba, kamar daga sama taji ana k'walla mata kira, waigowar da zatai ta hango Imran ya lafe a k'ofar fita waje.

SIRRINTACCEN SOWhere stories live. Discover now