3️⃣9️⃣

2.4K 481 40
                                    

ƘWARƘWARAH!!?

{ITAMA MATAR SARKI CE}

_HAZAKA WRITERS ASSO...._

ʍaɨ_ɖaʍɮʊ
օʊʍ ʍʊաaɖɖaɦ

https://my.w.tt/ngUvKpKtO7


#MY ZAHRAH🌹
Gabaki d'aya Labarin sadaukarwa ce gareki😍
ZAHRAN-ADDA RAMLA


               '''Gaisuwa ban girma? Gare ku Masoyan Kawu da Yarshi 😜❤️ Musamman Masoyan KWARKWARAH! Ina godiya FAUZIYA MB!'''

3️⃣9️⃣
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun!"
Na shiga ambata da sauri, nutsuwa ce ta shigo min, murmushi nayi ina kallon shi.

    "Kawu kuka kake? Toh ai baka yi kome ba, don wallahi bana kaunarka! Bana sonka dole ne. Dalla kyale ni."

        Nayi wuccewa zan bar falon.
"Jannatul Fidausiiiiiiiii!" Ya ambaci sunana.

   Cak na tsaya, amma dan kar na nuna mishi kiran da yayi min ya tasirantu a zuciyata! Na kad'a kaina tare barin falon.

     Ina shiga d'akina, na fashe da kuka, tare da dafe goshina.

              Jamal ya cuci rayuwata, ya san na gama mutuwa akan kaunar shi, sai da yaja sanadin da na tsane shi.

             Goge fuskana nayi tare da murza kwalli a idanuna,  haka kawai nake jin na cab'a ado, dan na kuma bawa zuciyar Samim daman amayar da goyan sonda yake min.

        Ina gamawa, na fito a hankali. Idan ka dube ni, zaka dauka ko yar wani Hamshaqin me arziki ce, domin ko takun da nake abin girmamawa ce, balle kuma kirkirarren farar da take kwance bisa fuska na.

      Ina fitowa, na kalli Samim da yake aika min da wani Wadatacce murmushi.

     Me narke zuciyar wacce akayiwa,  kallon shi nayi tare da sake murmushi nace.
"Kayi hakuri! Na b'ata maka lokaci"

       Fad'adda murmushin sa yayi cikin nutsuwa yace.
"Ai duk lokutana, da na yanzun da kuma na baya sadaukarwa kice, zamu iya tafiya Gimbiya Janny"

            Leka kitchen nayi, na ganshi rike da kofin ruwa, mama na wanke namar da zata yi mita dashi, Aliyah da Khalid, tare da Muhsina sun tafi islamiyya.

    A hankali na shiga kitchen ɗin, na je na rungume bayanta, nace.
"Uwata me share min kuka na, zamu fita da Mim!"

      "Allah yayi miki albarka!"
"Ni kuma ya kwashe min albarkan ko?! Wallahi kika sake kika fita a gidan nan sai na lalata miki, zuciya."

    Sake mama nayi ina kallonta, idanuna cike da kwalla.
            
   "Jeki Allah ya tsare! Karku jima?!"
      Tace min,
   Tsare hanyar yayi, d'ago idanu nayi cikin nashi.

K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)Where stories live. Discover now