Page Thirteen- Flashback 2

Start from the beginning
                                    

Umma tafito daga ɗaki tashigo parlourn tana kallon Hafiz tace "Hafiz ka'iso kenan?" murmushi Hafiz yasaki sannan yasamu guri yazauna yace "na'iso Umma. Ina wuni" Umma tace "Lafiya Lau ya Ummanka?" Hafiz yace "lafiyanta lau Umma tanama gaisheki" Umma tace "Ayya ai dazu ma nashiga gidannaku lokacin baka dawo daga makaranta ba" Hafiz kanshi na ƙasa yace "Eh itace ma take faɗamin kina nemana innataso daga islamiya inbiyo tanan" Umma tace "Allah sarki. daman tambaya zanyi maka akan Lamiɗo" Hafiz yace "Toh Umma" Umma tace "nikam wani abu yahaɗa ku faɗane kwanannan bana ganinku tare?" Hafiz yace "A'a babu abunda yahaɗamu Umma. koyau tare muka zauna dashi a Islamiya" Umma na kallon Hafiz tace "kunyi sabbin abokanaine?" Hafiz yace "bamuyiba Umma" Umma tace "shifah? baka ganinsa da sabbin abokanai?" nanma Hafiz yace "kullum muna tare a both Boko da islamiya Umma. nidai bangayayi sabbin abokanaiba" wannan karan cikeda tuhuma Umma tace "tare kuke skipping classes da missing test ɗin kenan?" cikin sauri Hafiz yagirgiza kai alamar a'a.

Umma tace "shikaɗai yakeyi kenan?" shiru Hafiz yayi baice komai ba, Umma tace "kayi shiru Hafiz?" jiki sanyaye Hafiz yace "Umma kinsan Lamiɗo bayason karatu daman tuncan" Umma tace "Tara Ƴan mata dayakeyi kumafa? dama tuncan yanayine?" cikin sauri Hafiz yace "Tara ƴan mata kuma?" Umma tace "Eh haka principal ɗinku yace. wai yana skipping classes yaje yana soyayya da Ƴan Mata" Hafiz yace "nidai ban taɓajin Lamiɗo na soyayya ba Umma. nadaisan yanada friends mata sosai kuma duk su suke binshi wallahi bashi yake fara kulasuba. Umma kinkuma san shi bayida wulakanci kowa nashine and quite sure nasan yana missing classes amma bada zummar yaje yayi hira dasu baneba. sune dasuka gane hakan shine suke zuwa su sameshi suyita hira to which duk baiwuce akan normal life ɗinmu bane ba bawai dasunan soyayya ba" hararan Hafiz Umma tayi tace "Kare abokin ka kakeyi kenan?" Hafiz da iyakar gaskiyarsa yace "wallahi ba ƙarya nakeyi ba Umma" Umma tace "shine kuma ni yake zuwa yasameni yacemin Yayi budurwa?" dariya Hafiz yayi yace "Umma sekace bakisan Lamiɗo ba? Yana faɗa ne danyaji bakinki kawai and nothing else" Umma tace "naji nakuma yarda anma kai amatsayinka na abokinshi yakamata ace kana faɗa masa gaskiya bawai kazuba masa idanu yana abubuwan dabai dace ba inbahaka ba toh miye amfanin abotar daman? Inka faɗa mai bai ɗauka ba gidannan wurin zuwan ka ne daman sekazo kafaɗamin ni zansan matakin dazan ɗauka akansa" Hafiz yace "kiyi hakuri Umma za'a gyara in Allah ya yarda" Umma tace "toshikenan taji kaje. nagode" Hafiz yace "toh Umma se anjima" kafin yafice agidan yaje yasamu Lamiɗo dake zaune kan dakali yayi tsuru tsuru da idanu yana tunanin wani laifin yama Ummarsa da Hafiz yajima har haka. Lamiɗo na kallon Hafiz cikin sauri yatashi tsaye yace "menayi Hafiz?" Hafiz yayi dariya yace "wallahi Principal ya kulla maka kulalliya gwanda kaje ka warware kanka yanzunnan" Lamiɗo cikeda damuwa yace "toh ai baka faɗamin menayiba,ta'ina zan warware kaina toh?" Hafiz yace "mekake ci nabaka nazuba? yanzu zanfaɗa maka ai" Lamiɗo yace "toh faɗamin inaji" take Hafiz yazayyana masa yanda sukayi da Umma kafin daga karshe Hafiz yace "kajeciki kasameta kasan yanda zakayi ka warware kanka nikaga tafiyata kuma nan gaba in kasake wani laifin dakaina zanzo in faɗa ma Umma tunda tafara zargin I'm not a good friend to you. Ina tsoron ranar dazatace zata rabamu" Hafiz yakarashe maganar cikeda zolaya.

Lamiɗo yace "kaidai zamuyi magana gobe. Principal ɗinnan kuwa seyasan ya taɓa Lamiɗo da mahaifiyarsa alqu'an" daganan Lamiɗo yayi kwafa yashige gida.

A parlour yasamu Umma zaune danhar lokacin bata tashi daga inda take zaune ba ko bayan dasuka gama magana da Hafiz. Umma naganin yashigo parlourn tayi maza ta tsuke fuskarta. karasawa inda take zaune Lamiɗo yayi yazauna shima sannan yace "Umma I'm sorry" amma ko kallonshi batayiba bare yasa ran zata kulashi,kamar me shirin yin kuka yasa hannu yakamo hannunta yasaka cikin nashi yace "yanzu Umma shiru zakiyitayi bazakicemin komai ba? your silence is killing me. gwanda ki dakeni,gwanda kiyimin duka akan laifuffukan danayi than keeping quiet sabida hakan yafi azabtar dani" Umma kwace hannunta tayi still batace masa komaiba.

Lamiɗo yasauke kansa ƙasa jiki sanyaye yace "Hafiz yafaɗa min komai Umma and I'm sorry for causing you alot of troubles but you should've atleast ask me kiji ta bakina. nasandai bakiyi trusting Malaman makarantar mu kamar yanda kika yarda daniba" Umma dasai yanzu taga daman yimasa magana tace "ada kenan ba" Lamiɗo yace "akan wannan laifin dasukace nayi yasa kika yarda dasu over ni?" Umma dai batace masa komai ba Lamiɗo yace "nasan nayi laifi daban bi umarnin ki ba,banyi abunda kikeso ba amma aini bantaba ɓoye miki komaina ba Umma,tunbayau ba kinsan banason karatu,nasha faɗa miki acireni a makaranta anma kinki bin abunda nikeso shiyasa nayi taking wannan step ɗin. batun Ƴan mata kuma da akace inadashi wallahi ƙarya akayimin. niban taba budurwa ba inbanda friendship dake tsakanina dasu, shiɗinma su suka nema, maganar hira da akace inayi dasu inasasu suyi skipping classes niban taɓa cewa watarsu tazo tasameni a Inda nake zamaba suda kansu suka fara bina Umma anma insha Allahu tunda haryakai ga ana zuwa ana tadar miki da hankali bazan sake ba. Kiyi hakuri kiyafe mun don Allah,fushin ki wallahi azabtar dani yakeyi" Umma kallonshi tayi sannan tace "Uhmmm! nidama nace banyafe maka bane? yana iya dakai daman inbanyi hakuriba tunda kanuna kafi karfina,kafi karfin in faɗa maka kayi,kafi karfin kataimakamin incika ma mahaifinka burinsa nason kazama mutum kamar kowa" Lamiɗo dayagama gane Umma faɗa masa magana takeyi a fakaice yasashi cewa "Wallahi Umma bahaka bane" Umma tace "Hakane mana Lamiɗo. kuma tunda kanuna kafi karfina semu tattara mukoma Kwami kawai gaba ɗaya,kannen naka ma dasun kara wayau duk aure zanyi musu tunda konace suyi karatun zasu iya kinyi tunda sunga Yayansu ma bai maida hankali ba sabida haka kafara shiri,kazuba ruwa akasa kasha zakabar karatun Boko kaje kayi abunda ranka yakeso,inkaga dama ma kaje kacigaba da haɗa temple kana tara mata suna zuwa kallon kyawun da Allah yayi maka" daganan Umma tatashi tabarshi zaune gurin kamar wani gunki.

QADRWhere stories live. Discover now