Daga haka ya tada motar suna barin gidan suna cikin tafiya ya dube Maryama yace
"Ke kika faɗa Nafisa?"

"A'a sa idonta ne."

"Ai ko kowa sai ya sani."
Yace yana murmushi Maryama ta ƙara haɗa rai.

Yana janta da hira sama sama har suka isa gida, bayan isarsu basu tsaya ko ina ba sai part ɗin Kaku.

..

Damuwa da tashin hankali da take ciki ya hanata ci ya hanata yin abun kirki, tayi kukan tayi ta rasa mafita ta kasa ko wankan kirki balle kwalliya da gayunta da take ciki kullum.

Turo ƙofar ɗakinta da aka yi ya sata buɗe idanunta ta kalli mai shigowa taga Momy ce ta maida idonta ta rufe ta tsaneta haushinta take ji duk ita ta jawo mata haka a rayuwarta.

Zama Momy tayi kusa da Maryam tana bin ɗakin da kallo duk a hargitse ta taɓa Maryam tace.
"Tashi Maryam magana za muyi akan aurenki zan samo miki mafita."

Tashi Maryam zaune tayi tana bin Momy da kallo kafin Momy tayi magana tace.
"Ya isheni Momy komai ya fita kai na duk ke kika jawo min, kin tarwatsa min rayuwa da farin cikina kin rabani da mijina abin sona, ya kike son in yi? In ƙara yarda dake in biki ki ƙarasa sauran rayuwata ko in biki gurin mahaifiyarki da duk halinku daya, anya Momy ba ke kika kashe mahaifina?"

"Ni kike ma rashin kunya Maryam har kina zargina da kisan mahaifinki?"

Rabuwa da ita Maryam tayi tai kwanciyarta Momy nata faɗa karshe data isheta ta tashi ta faɗa bathroom ta rabu da Momy dake zauna haka ta gaji da faɗarta ta fita.

Kuka Maryam ta fashe dashi nadama yana shigarta, ta daɗe cikin bathroom ɗin kafin ta iya yin wanka ta fito ta saka kayanta ta fara haɗe haɗen kayanta wajen dangin mahaifinta zata tafi ko hankalinta zai kwanta ba zata zauna gurin Momy ko mahaifiyarta su ƙarasa ɓata mata rayuwa gaba ɗaya ba.

Sai da ta gama tsaf ta jawo akwatin ta ta fito bata ma ko Momy sallama ba ta fita ta fita a gidan gaba ɗaya ta tari taxi ta bashi address na gidan Yayan Babanta da tasan in taje zai karɓeta ta zauna ta samu kwanciyar hankali.

...

Washegari ranar Lahadi karfe sha biyu su Maryama suka wuce Abuja bayan sun ma iyayensu sallama.
Kaku sai washe baki take zata bisu bayan roƙar Abbi da tayi tai ya barta tayi kwana biyu ta dawo.

Suna komawa Maryama ta shiga kitchen ta ɗaura musu lunch da tasan zata iya ci shima Ya Faruq zai ci.

Data gama har falonta ta kai yana ta mata sannu sai dai tayi murmushi kawai.

Kaku kam hararan Ya Faruq tayi tace.
"Sai kace a kanta aka soma ciki sai jera mata sannu kake wanda randa tazo haihuwa maganarka sai ya ƙare."

"Ki rufe min baki karki ki saka min ido in dama sa ido ya kawoki to zan mai dake gida."

A

harzuƙe Kaku tace.

"To ubana nayi shuru kai ko ɗan yawon nan ma da kace zaka kai ni shuru."

"Zan kai ki ai muci abinci mu huta sai muje."

To tace tana washe baki Maryama da dariya kawai take musu ta saka musu abincin su kaci kaku tace.
"Ashe kin iya girki, irin na Sadeeya wallahi kin yi gado mai kyau."

MARYAMA MARYAMWhere stories live. Discover now