Tana isa gida taga harsu Husnah sun gama komai hatta Dinner sun kammala sun zuba a warmers, tuni suka saki ransu suka fara walwala jin cewar an gano abinda ke damun Ahmad, sosai suke cikin farin ciki musamman Husnah wacca jinta take kamar an mata bushara da gidan Aljanna.
Mama ce ta kallesu tace "Madalla, bari bai Sallahr Magrib sai nazo na kai musu abincin"
Husnah cikin muryar shagwaɓa tace "Haba Mama, mufa?, baza muje muga Ya Ahmad ɗin ba"
Murmushi Mama tayi itama tana cikin walwala tace "To ba komai yaran kirki kuyi Amaza kuyi Sallah sai Driver ya kaiku"
Tsalle suka buga tare da tafawa suka nufa Bedroom dan ɗauro Alwala suyi sallah.Suna Idarwa sukaje sukaima Mama sallama Driver ya jasu sai Hospital, Haajara kallan Uban Security ɗin da aka zubawa Ahmad tayi ta taɓe baki tace "Wallahi Sis nifa auran mai kaki baimin ba ko kaɗan, abi a zagaye maka gida da bindiga, dan Allah duba ki gani a asibitin ma bazasu ƙyalesu ba"
Murmushi Husnah tayi tace "Niko hakan ba ƙaramin burgeni yakeyi ba, ko banza za'a kula da lafiyarla yadda ya kamata"
Taɓe baki kawai Haajara tayi suka tura ɗakin da aka kwantar da Ahamd.
Da sallama suka shiga Safwan ya amsa tare da ɗago da kanshi, tunda suka shigo kanshi yana kan Husnah, haka kawai yarinyar take tafiyar masa da hankali duk lokacin da ya haɗa ido da ita, ya rasa mai yasa yakejinta a ranshi da yawa, kuma natsuwarta ba ƙaramin burgeshi takeyi ba" ganin sun haɗa ido yayi saurin kawar da kanshi yayinda ita kuma ta duƙar da kanta.
Kujera suka samu suka zauna suka ajiye Warmers ɗin da sukazo dashi, gaishe dashi sukayi tare da tambayar ya mai jiki, "Da sauƙi, ya Mama ta koma gida?"
Nan suka shaida masa da lafiya ƙalau.
Shirune ya biyo baya yayinda Ahmad keta baccinsa yayi wani haske ba ɗan kaɗan ba abunka da farin mutum ga wata rama datayi.
Su Husna sun ɗan daɗe a Hospital ɗin sannan suka miƙe tare da yiwa Safwan Sallama suka tafi, har sunkai bakin ƙofa Safwan yace "Husnah ɗanzo mana"
Ba musu tazo yayinda Haajarah ita kuma ta fita waje dan jiranta, tana zuwa yace "Numbernki nakeso ki ban"
Shiru tayi naɗan wani lokaci kamar bazata bashi ba, miƙa mashi wayar tayi tace "Ka samu taka saina kiraka"
Ba musu ya amsa wayar ya saka numbernshi ya kira, saiga Numbernta ta bayyana, miƙa mata wayar yayi yace "Zamuyi magana, naga Haajarah na jiranki"
"Humm" kawai tace ta juya ta tafi, ajiyar zuciya ya sauke ganin ta tafi, dawowa yayi ya zauna yana latsa wayarsa, kiran Binafa ne ya shigo wayar, murmushi yayi yana mai jin daɗik yadda Binafa ta manta da komao game da Ahmad, katse kiran yayi ya kirata, tana ɗauka cikin shagwaɓa tace "Wai Ya Safwan ina kajene haka tun safe nake nemanka amma ban ganka ba?"
Murmushi yayi yace "Tuba nake ƙanwata, tafiyace ta kamani to ban ɗauka zan kwana ba sai aka samu akasi dan haka zan kwana sai yadda hali ya yuwu"
Jim Binafa tayi tace "Ya Safwan ina kaje haka harda zaka kwana?"
Murmushi yayi mata yace "Ina Adamawa wallahi"
Gabanta ne ya yanke ya faɗi tace "Ba damuwa saika dawo Allah ya kiyaye hanya ka kula da kanka" bata jira cewarsa ba ta katse kiran, zamewa tayi daga kan gado ta sauko ƙasa tana tunanin Ahmad, tasan tabbas bataimai adalci ba ko da wasa bata taɓa gwada kiranta ba shima hakan, wayarta ta ɗauko ta ruƙe tanason ta kirashi taji lafiyarsa amma ta kasa, domin tasan muddin ta kirasa to tabbas zata fama ciwon datake fama dashine, ajiye wayar tayi kafinta farga hawaye ya fara wanke mata fuskarta, goge hawayan tayi tanajin zuciyarta na mata wani iri, yaya zatai dole tabi zaɓinta iyayanta, kuma taso abunda takeso tana ta tabbacin bazata taɓa danasani ba, kwantar da kanta tayi akan Gado soyayyar Ahmad na ƙara azabtar da zuciyarta.Mahbub ne zaune gaban mahaifinsa, yanayin yadda yake maganarsa zaka tabbatar da shiɗin sangartaccene na gasken gaske, mahaifinsa shiru yayi yana nazarin abunda yaron nasa yazo mishi dashi, kallan Mahbub yayi yace "Bana tunanin Alhaji Modibbo ya ɗauki ƴarsa guda ɗaya ya mallaka maka ita alhalin yasan kaiɗin ko waye, amma zan tuntuɓa naji ko Allah zai saka a dace"
Lumshe ido yayi yace "Dad ka taimakamin domin Binafa ta zama matata, nai maka alƙawarin daina duk abunda kasan inayi mara kyau"
Jinjina kai Madaki yayi yace "Allah yasa, shikenan baka da damuwa insha Allahu zan bincika maka...."
Bai karasa faɗan abunda yakeson faɗa ba saiga matarshi ta shigo fuskarta cike take da walwala tace "Ranka ya daɗe yanzu aka ba wani saƙo ya kawo maka" miƙa masa tulin Sweets tayi haɗe da goro da kuma wani I.V mai shegen kyau, karɓa yayi yana ƙoƙarin shan ruwa yace "Tofa wa kuma zayyi aure haka bamuji saka rana ba sai I.V ɗin biki nake gani"
Murmushi ne ya bayyana a fuskarta tace "Iyalan Modibbo ne dana Safwan zasuyi aure, abun nasu harda sonkai gabaki ɗaya sunyi masaya, kasan wannan ɗiyar tasu da aka gani kwanaki shine Safwan zai aureta Lanika kuma Mahmud..."
Bata ƙarasa ba taga ya ƙware da ruwan dayasha, tari ya farayi cikin azama ta nufa Fridge ta ɗauko Drinks ta bashi tana mishi sannu.
YOU ARE READING
CHAKWAKIYA
FantasyBinafa tana zaune a tsaƙar gida daga ita sai wani gajeren wando daya wuce gwiwarta sai wata riga wacca taɗan matseta kaɗan kanta babu ɗan kwali gashin kanta ya sauka har gadan bayanta, tana zaune tana jujjuya abincin ta kasaci, ta lula tunanin duniy...
Page 31
Start from the beginning