SHA TAKWAS.
MAINA.
"Fad'i dukkan sharad'inka a shirye nake domin cika maka su ko da kuwa fansar raina ne, indai zaka amince da bukata ta".
Tsaraki ya yi gajeriyar dariya kafin ya sake daidaita tsayuwarsa yakai dubansa fuskar Dan Zabuwa a karo na kusan hudu, kafin ya fara magana da fadin.
"Tabbas zan amince da Manya ya auri Mairamu idan har zaka dawo da kambun tsarafi gare ni, zan yarda na sadaukar da fansar gaba idan har ka amince ka damka kambun sarautar ahalin mu guda biyu a hannuna, wanda kakanmu ya kwace daga hannun Mahaifina, zan yarda da auren ne kawai idan ya kasance ka durkusar da karfi da iko na Manya, idan har ka aminta da wadan nan sharadin to shirye nake ko yanzu basai anjiba ba ko gobe a daura wannan aure".
Dan zabuwa ya zubawa Tsaraki idanuwa tsayin wasu dakikai yana nazartar gaskiyar al'amarin daya zo masa da su wanda bai yi tunanin hakan daga Tsaraki ba, domin abin da ya bukata abubuwa ne masu matukar wahala, amma da ya tuna da gudan jininsa tilo daya tal a duniya mafi soyuwa a gareshi sai ya ji a shirye yake ya sadaukar da komai daya mallaka domin samun lafiyarsa, dago kai ya yi yakai dubansa ga Tsaraki wanda shima kallon nasa yake yi fuskarsa fal murmushi domin yasan ko babu komai ya yi abin da zai wulakantar da Dan Zabuwa a kauyen Maina, shi kuwa Dan Zabuwa ba tare da sake nazartar yanayin Tsaraki ba ya cigaba da fadin.
"Zan baka dukkan abin da ka ambata, amma akan sharadi guda daya".
"Ina jinka".
"Sai idan ka yi alkawari da kambun tsafi ba zaka cutar dani da yarona ba*.
"Na yi alkwari, kuma kasan nasan girman alkawari zan rike kalmar da yakininta, bazan canja abin da na fada ba".
"Shi kenan zuwa daren yau ka zo gidana zan baka dukkan abin da ka bukata"
"An gama"
Da ga haka suka yi sallama kowa ya yi hanyarsa, Tsaraki cike da dumbin farin ciki da murnar cin galaba akan Dan Zabuwa, Dan Zabuwa kuwa abin duniya ya yi masa yawa, yana ganin zai aikata babban kuskure ne zunubi mai girma, amma idan ya tuna lafiyar yaronsa sai ya ji a ransa hakan ba komai ba ne.
KANO.
WASHE GARI.
Bayan ta idar sallar asuba tana zaune kan abin sallar tana addu'o'inta, saboda sabo da tashi a gidan su Salima, har ta soma zame mata jiki, bacci ne ya sace ta anan inda take zaune, kamar daga sama taji yo tashin bugun kofar dakin nata, firgigit ta farka tare da murje ido ta nufi bakin kofar da fad'in.
"Waye ne?".
"Hafsy ce".
Ta bata amsa a daidai sanda ta bude kofar, da murmushi suka dubi juna Ishatu na fad'in.
"Bismillah shigo mana".
Hafsy ta sanya kai cikin dakin tana mai cigaba da fad'in.
"Kin jini shiru sai yanzu Allah ya yi dawowar mu, kai amma dakin naki ya yi kyau wallahi".
Ta kare maganar tana mai ajiye manyan ledojin data shigo da su kafin ta nemi gefan katifa ta zauna, ta sake duban Ishatu dake tsaye tana binta da kallon mamakin jin cewar tun daren jiya sai yanzu ta dawo.
"Ishatu lafiya kuwa?".
Ishatu ta dawo daga duniyar tunanin da murmushi shimfide saman fuskarta kafin ta ce.
"Kenan ba gida kika kwana ba?".
Hafsy ta yi dariya ba tare da ta bata amsa ba ta cigaba da magana.
"Kin ga duba cikin waccan karamar locker akwai plate da sauran kayayyaki kitchen dauko nan mu yi breakfast dan wallahi da yunwa na dawo, wannan shegiyar dinner a bushe basu tanadi abincin kirki ba sai kayan shaye-shaye na banza".
Ita dai Ishatu tuni ta dauko mata abin da ta bukata ba tare da ta damu da son jin inda zancen nata ya nufa ba, ta ajiye mata kayan a gabanta tana cewa.
"Yunwa tun yanzu Hafsy?".
Baki sake Hafsyn ke dubanta da mamaki kafin ta daga kai takai dubanta jikin bangon dakin inda agogo yake kafe lokaci guda ta dawo da kallonta ga Ishatu da fadin.
"Kika san yanzu karfe nawa?".
Sai lokacin Ishatu takai dubanta wajen agogon karfe tara har da wani mintuna lokacin, Ishatu ta zaro ido da fadin.
"Ikon Allah ashe bacci na yi sosai haka?".
Hafsy ta girgiza kai da murmushi ba tare da ta sake magana ba, ta cigaba da juye musu kayan makulashe kala-kala wanda Kamal ya biya ya siya Mata, saboda mitar yunwa data cika shi da ita suna hanya.
"Ya kamata a ce an kawo miki kayan tea fa? Babu wanda ya shigo wajenki ne?".
"Aa Aunty ta shigo tun jiya da dare".
"Ok may be ina jin ta yi aike kina bacci, dan nasan ba zata bari a tashe ki ba".
"Ai tana da kirki Aunty sosai".
Hafsy ta gimtse dariyar dake shirin kufce mata jin maganar da Ishatu ta yi akan Aunty har tana shirin kwarewa a daidai sanda takai cokali bakinta dauke da farfesun kayan jiki, a jiye cokalin ta yi tare da yafito Ishatu da hannu ta zaunar da ita gefanta da fadin.
"Zan gaya miki wani abu a game da zaman gidan nan amma kafin nan na tambayeki abu daya zuwa biyu, idan kin ga dacewar ki sanar da ni ina maraba da hakan, idan kuma abin ya kasance sirri ne a gareki to kibar abin a cikin ranki".
Ishatu ta gyada kai alamun ta gamsu da batun nata, Hafsy ta zubawa Ishatu nata naman a dayan plate din tana mai cigaba da cewa.
"Mene dalilin da ya fito dake daga gida, sannan kuma kin shiryawa zama a cikin gidan nan?".
Ishatu ta yi shiru tsayin wasu dakiku tana nazari da tunanin amsar da zata bata, kafin ta yankewa kanta hukuncin sanar da Hafsy wani abu a dangane da ita, nan dai ta fara bata labarin zuwanta gidansu Salima da shiga dakinta da ake yi da yanda aka yi ta baro gidan, Hafsy ta girgiza kai kafin ta ce.
"To ni a ganina nan din ma da kika zo duk kanwar ja ce, amma kafin na ce wani abu bani amsata ta biyu".
Ishatu ta gyara zama kafin ta cigaba da magana.
"A shirye nake na cigaba da zama anan, domin idan har nabar nan bansan inda zan nufa ba".
Hafsy ta girgiza kai da murmushi kwance saman fuskarta, kafin ta kama hannun Ishatu ta rike a cikin nata ta dubeta da kulawa kafin ta ce.
"Kinsan abin da zan fada miki da zaman gidan nan? Babu ruwanki da shiga harkar da bata shafeki ba, haka kuma duk wacce ke nemanki da rigima ki bawa banza ajiyarta, Aunty na son girma da iko, ki girmamata ki yabeta a gabanta, idan kin bi wannan zaki zauna kafiya kalau da kowa cikin gidan nan, sannan kuma a labarin da kika bani kamar kin boyemin abubuwa da dama, amma karki damu kanki nasan may be sirrinki ne, nasan kuma akwai lokacin da zaki yarda dani ki sanar dani, Bismillah muci abinci".
Tana kaiwa nan ta cigaba da cin abincinta, haka itama Shatun, amma a gefe guda tana mamakin saukin kai irin na Hafsy da yanda ta dauki rayuwa ba komai ba, tafiyar da rayuwarta take yi hankalinta kwance, alamun babu abin da yake damunta a fadin duniya, a haka suka kammala karyawa Ishatu ta kwashe kwanukan ta wanke kafin ta dawo ta nemi inda ya tashi ta zauna tana kallon Hafsy dake ta faman latse-latsen waya data gaji ta shiga daukar selfie har tana sanya Ishatu ta matso sunyi hotuna sosai masu kyau da yake wayar iPhone 11 ce ga kyau ga fidda hotuna masu kyau, Ishatu ta dubi Hafsy dake gyara kwanciya da shirin bacci tana fadin.
"Na tambayeki mana Hafsy?".
"Allah yasa na sani ina jinki".
Ta karashe maganar tana hamma alamun baccin take ji sosai, Ishatu ta gyara zama sosai kafin ta ce.
"Wai dan Allah mene Bariki ne? Kuma suwaye kadangarun Bariki kamar yanda na ji jiya suna maganar anan waje?".
Hafsy ta mike zaune tare da murje gidonta daga baccin dake fizgarta, ta kafe Ishatu da manyan idanuwanta sosai take yi mata kallon mamaki.
'Baya ga haka kuma bata zubi ga mutanen kauye bare ta kirata bakauya, kuma tasan a kauye ma yanzu yaro da babba babu wanda zai ce baisan me kalmar bariki take nufi ba amma da mamaki'
Hafsy ta gyara zama tare da fara yi mata bayani daya bayan daya ta cigaba da fad'in.
"Aunty zata yi alfahari da ke ne idan kin fita kin nemo mai yi Miki hidima tare da ita, haka kuma zata kaunace ki fiye da kowa idan farashinki ya haura na sauran matan dake gidan nan, ni nasan zaki yi kasuwa matukar kika waye a wannan harkar, sannan kuma kinsan wani abu?".
Ishatu ta girgiza kai alamu a'a.
"Na ji mamaki da kika tambaye ni game da abin da ake nufi da bariki, dama wai ba BARIKI KIKA FITO BA?".
Ishatu ta girgiza kai alamun zancen Hafsy ba haka bane.
"Shi yasa dama na tambayeki idan kin shiryawa zama anan domin babu macen da Aunty ke ciyarta da ita abanza matukar ba zata fita ta nema ba sunanta sorry, ki yi tunanin mafita Ishatu zan taimake ki da yardar Allah kin ji?".
Hafsy ta koma takwanta tabar Ishatu nan zaune zuciyarta cike da sake-sake kala-kala na neman mafita akan tudun data taka a yanzu, wanda tana ganin har kusan gara zamanta a gidan su Salima akan hanyar da rayuwarta take shirin bi yanzu, ko kusa ko da wasa bata fatan sake kazanta kanta domin Allah ya nufa ta tsabtacu akan addininta, tunani sosai take yi tare da neman mafita kamar yanda Hafsyn ta fada mata.
Ku BIYO Ni..!