Addu'ar Mash'arul Haram Jabir, Allah ya yarda da shi, ya ce: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya hau taguwarsa mai suna Al-Kaswa har ya zo Mash'arul haram, sai ya fuskanci alkibla ya yi addu'a ga Allah, ya yi kabbara, ya yi hailala, ya kadaita Allah. Bai gushe ba a tsaye yana addu'a har sai da gari ya waye sosai, sannan ya dauki hanya kafin rana ta fito.
HISNUL MUSLIM
By Oumzaynab
Littafin Hisnul Muslim, Addi'o'i da suka dace da Sunnar Annabi. FALALAR ZIKIRI Allah Madaukakin Sarki ya ce: ... More