_Page 3_
*TUKUICIN SO*💞
*NA*
*BILLY S FARI*💎
*HASKE WRITTER'S ASS..💡*
*Free Book*
*G* udu yakeyi sosai d'auke da Razina ba tare da yasan dalilinsa nayin hakan ba har saida yakai bakin wani shago inda wata mata ke saida abinci, cikin muryar dake nuna tsantsar gajiya da yunwar dake tare dashi yace, "Don Allah hajia ki taimakamun da abinci na bawa qanwata" juyowa matar dake miqawa wani saurayin abincin dake cikin takeaway ansa cikin baqar leda daya siya tayi had'e da cewa,
"Kawo kudi.." da yake ba bahausa bace amma taji hausa sosai, goge zufan dake tsiyayo masa afuska yayi tare da guntayen hawayen da suka zubo a idanuwansa sannan yace,
"Banida kud'i, kitaimaka mani don ALLAH..." Bai qarasa rufe baki ba wani saurayi da take qoqarin miqawa abinci yana miqo mata kud'i yasa hannu ya turasa gefe suka fad'i qasa Yana fad'in,
"Kai gafara can, ku bazaku tashi kuje ku nemi na kanku ba iyayenku duk sunbi sun kashe maku zuciya da bara da roqo..." Bai rufe baki ba shima matar ta karb'e abincinta daya siya tamiqa masa yanzu had'e da turesa shima sannan ta watsa masa kud'insa data karb'a a fuska taje ta duqa kusa da Muhriz dake qoqarin d'ago Razina dake kuka yana kakkab'e mata jiki ta miqa masa,
"Sorry, kiyi hakuri kinji? Ina Mama naki take?" tana shafa kansa tare da goge masa gefen fuska, cike da rashin damuwa da halin da yake ciki ya karb'e abincin ya bud'e, lafiyayyar shinkafa da miya ne hadda naman kaza da salad ya ture naman agefe ya shiga yamutse abincin yana d'iba yana bawa Razina abaki ba tare daya damu da bawa matar amsar tambayar da tayi masa ba balle har ya godewa abunda tayi masu, ganin haka yasa tamiqe tsaye tana jifar saurayin da yayi tsaye bud'e da baki da harara, shafa kansa yayi tare da cewa "sorry madam" Yana sake miqo mata kud'in don tabashi abincin, kamar jiransa takeyi ta balbalesa da masifa ta inda take shiga ba nan take fita ba har saida mutane suka taru wajen, fad'a takeyi masa sosai akan abunda yayi tare da illar yin hakan wanda sai a sannan hankalin mutanen ya koma gasu Muhriz dake qasa zauna yana Ida qarasa sauran abincin da Razina ta rage, don kuwa taci sosai saboda ba qaramar yunwa take jiba, ga abincin saye dama shima bawani afkine dashi ba, kallo d'aya zaka yimasu kafahimci suna buqatar taimako saboda yanda suke awani hargitse, nan mutane suka taso masa suma da matar ta fad'a masu abunda ke faruwa suna fad'in be kyauta ba, daga qarshe kuma ta buga kai ga qasa tace bazata sayar masa da abincinta ba koda shikadai be customer daya rage mata aduniya, yayi magiyar duniya amma ta hanasa dole ya haqura yabar wajen cike da nadamar abunda yayi kafin sauran mutanen dake wajen suma sufara watsewa,
Ledar ruwa qwaya d'aya ta d'auko ta miqawa Muhriz ganin sun gama cin abincin yasa hannu biyu ya karb'a tare dayi mata godiya murmushi ta sakar masa tana yaba kyawon da ALLAH yayi masa shida 'yar uwarsa, har lokacin fuskarta cunkushe ba walwala saboda abunda saurayin nan yayi masu, babu abunda ta tsana aduniya irin taga ana walaqanta mabuqaci musamman yara duk da irin tarin tuhuma da laifin iyayensu da take gani idan ta ganesu cikin wannan yanayin, shiyasa a kullum batada buri irin taga ta gina yaronta qwaya d'aya da ALLAH ya bata aduniya ta kuma tsaya masa yasamu ingantacciyar rayuwar da bazai lalace mata ba, tana wannan tunanin Muhriz ya d'auki qanwarsa suka koma can gefe yana yimata wasa tana dariya, dama shi yaro matsalarsa lokacin da yake cikin damuwa amma data kau zaka gansa tamkar ma baisan meya faru ba ko halin da ake ciki, to haka ta kasance ga Razina sab'anin shi Muhriz da babu abunda ke zuciyarsa a yanzu kamar ina suka nufa idan dare yayi? Ina zasu je? Shine abunda kawai keyi masa kaida kawo a qwaqwalwa da kuma zuciya,
Har aka kira sallar magrib suna awajen, su basu tafi ba su basu tsaya waje d'aya ba, in yayi nan da ita aguje tana dariya yabita can da gudu sunata wasarsu, can dubara ta fad'o masa ganin matar tafara har had'a kayanta alamun ta tashi, da sauri ya kamo Razina data ruga tayi bakin titi ya d'aukota ya nufo wajen matar.
"Madam" ya fad'a kamar yanda yaji wancan saurayin ya fad'a d'azu, d'an juyo da kanta tayi jin sautin muryarsa kafin ta juyo da jikinta duka gaba d'aya tana d'an sakin fuskarta daga yanda take d'azu,
"What little boy?" Kasancewar acan qauyensu ya fara zuwa makaranta don har yakai aji d'aya na matakin secondary yasa ya fahimci me take cewa, dama can yana d'an ji kad'an kad'an mayarwar ce dai bazai iya ba,
"Don ALLAH kitaimakeni ni da qanwata, bamuda kowa nan garin an kashe mana iyaye"
Wani kallo tayi masa mai d'auke da alamomin tambaya barkatai tana nazartar cikin idanuwansa kafin tace,
"Daga ina kika zo"
"A can qauyen charanci" shiru tayi kamar mai wani nazari saiga sautin qarar redio daga wani shago dake kusa da nata na tashin labarai cewa 'yan bindiga sunkai hare hare a yankin qauyukkan dake cikin jahar da suka had'a da charanci, qanqara da kuma kakumi, inda sukayi garkuwa da qananan yara da mata kuma suka karkashe mutane masu yawan gaske, cikin damuwa ta sake tambayarsa jin abunda ke faruwa,
"To waye ya kawoku nan little boy"
"Wani drivern mota ne ya taimaka mana lokacin da muka fito daga qauyenmu"
"To ina drivern yanzu? Meyasa bakuce yataimaka maku ba kuka barshi ya ajiyeku"
"Madam, Ina tsoron kada ya cutar damu nida qanwata, shiyasa yana yin parking na b'alla marfin motar nagudo"
"No boyyyy...bakyau haka da kayi, wanda ya taimakeku acikin daji har kuka zo nan baiyi maku komai ba bazaya cutar daku ba, infact kayi kuskure wataqil ma zuciyarsa me kyau ce zai taimaka maku daka tsaya"
"Madam! kitaimaka mana zanyi maki duk aikin da kike so narantse"
"Shikenan, tunda kayarda dani zan taimakeku kafin hankali ya kwanta kaji ko, ya sunanka"
"Muhammad Muhriz, qanwata kuma Razina" ya qarasa fad'a cike da farinciki tare da ajiye Razina qasa yana qoqarin karb'a qatuwar kular dake hannunta, dariya tayi da saida haqoranta suka baiyana had'e da cewa,
"Noo.. kabarshi kaji ko?, d'auki qanwarka kaga dare ya somayi kada taje tahau kan titi, bara na taro napep sai muje gida, nasan yarona ya dawo yana can yana jira"
Tana rufe baki napep na tsayawa tace, "Yawwa thank God, kagama mun huta, kuzo ku shiga"
Gefe ya ajiye Razina ya kama mata suka shigar da kayan cikin napep suka had'e kujeru da benci n da take d'ora abincin akai suka rufe da qaton buhu (tanhol) suka saka duwatsu suka daddanne sannan ya d'auki Razina suka shiga mai napep ya ja sukabar wajen tana lakutar chicks d'in Razina data kama ta maqalqale Muhriz saboda quiya tamkar wacce za'a raba dashi,
Kyakkyawan gidane madaidaici da bazaka tab'a cewa wacce ke cikinsa sana'ar abinci takeyi ba saboda har d'an madaidaicin gate ne d'auke dashi, suna tsayawa aguje yaronta da kad'an Muhriz zai girmesa ya rugo yana yimata oyoyo tare da rungumeta, jawosa tayi ajiki tana shafa kansa,
"Oyoyo my one and only son, how was the school"
"Fine mom" ya fad'a yana sake shigewa jikinta tare da bin Muhriz da Razina da kallo,
"Mom where do you find this beautifuls?" Ya tambaya tare da d'ago kai yana kallon momynsa, dariya tayi had'e da ciro d'ari uku a jikkarta ta miqawa mai napep d'in daya gama sauke kayan,
"Muriz come in side" don haka take kiran sunan nasa, wannan karon dai bai fahimci me take cewa ba shiyasa har ta kusa shigewa baibi bayanta ba har saida yaron nata daya bisu da kallo yace,
"Kashiga ciki tace" shi kuma yafara qoqarin kwasar kayan kamar yanda ya saba akoda yaushe ba tare daya sake cewa komai ba, ajiye Razina Muhriz yai ya taimaka masa suka d'auki kayan tare suka shiga dasu ciki Razina na biye dasu abaya.
Baki Muhriz ya saki yana qarewa gidan kallo saboda kyansa duk da bawai wani tsaruwa sosai yayi ba amma daidai gwargwado rufin asiri babu abunda zaka nema aciki karasa sai abunda ba'a rasa ba,
Saida suka gama kwashe kayan kaf lokacin harta watso ruwa ta dawo falo ta zauna tana qirgar kud'ad'en data samu na cinakin da tayi yau tana so ta fitar da riba da uwa ta bawa wacce ke tayata aiki taje ta siyo sauran abubuwan da babu na abincin gobe,
"Momy! Who are those people pls" yaron ya sake tambayarta akaro na biyu, ajiye kud'in tayi tare da kallon gefen da yake tace,
"Ha'a! Jabeer, what's wrong with you, bazaka bari na fara hutawa bane? Go and bring my food kaji ko"
"Yes Momy, am Sorry" ya fad'a kamar zaiyi kuka yana tangalar kai sannan yawuce kitchen, yayinda shi kuwa Muhriz yayi zaune qasan kujera yana fama da Razina data haye saman kujerar tana tsalle tsalle data sauko,
"Kabarta Muriz, kazo ka shiga ciki Jabir zai gwada maka toilet kayi arwala kuje kuyi SALLAH"
Daidai lokacin Jabir yakawo mata abinci ya ajiye agabanta yana kumbura fuska irin na shagwab'ab'b'in yaran nan dake samun kulawar uwa d'ari bisa d'ari, murmushi tayi ba tare data bi takansa ba tace,
"Thank you darling, je ka kaisa toilet yayo arwala kaima kayi kuje masallaci kuyi sallah"
Razina na ganin ya tashi sun shiga wani d'aki ta sauko kan kujerar tabi bayansa tana kuka, har madam zata kai spoon d'in abinci abakinta ta ajiye taje ta d'aukota,
"Sorry Razi..bari su dawo wajen sallah ko" taqare maganar tana kaimata spoon d'in abincin abaki, qin karb'a tayi sai qoqarin zillewa takeyi daga jikinta tana kallon qofar d'akin da suka shiga, basu jima ba da shiga ba sai gashi yafito da sauri jikinsa jiqe da ruwa alamun yayo arwalar ya nufo wajen da sauri yana goge hannayensa ga riga zai karb'eta don jin kukan nata yakeyi har cikin qoqon ransa,
"Kaje mana kayi Sallah, ko zaka fasa ne don tana kuka?, Jeka mana zatayi shiru.."
Madam bata rufe baki ba Razina ta kwatsa wani irin kukan ganin ya juya zaibar wajen, runtse idanuwansa yayi tare da bin bayan Jabir daya fito da sauri suka wuce masallaci, ita kuma Razina madam ta shiga rarrashinta, da taga taqiyin shiru sai kawai taje ta kunna mata tv ta saka mata catoon, da farko qin ko kallon wajen tayi har saida taji sautin qarar maganar catoon d'in da madam ta qara murya, a hankali ta juyo tana kallo, kan kace me tayi shiru sai dai ajiyar zuciya, Saida madam taga hankalinta ya d'auku sosai sannan ta ajiyeta, bata koma bi takan abincinta ba sedai tawuce d'akinta itama tayo arwala ta d'auko carpet d'in sallar ta ajiye kusa ga Razina ta kabbarta itama tayi sallar,
Ba qaramin dad'i yaji ba lokacin da suka dawo ya riski qanwar tasa tayi shiru har tana kallo tana tafi da hannuwa ga kuma madam agefenta tana sallah, sai yaji wata irin qaunar matar marar misaltuwa ta dirar masa azuciya.
Da daddare bayan sunci abinci sun gama madam ta zauna ta shiga tambayar Muhriz labarinsa dana iyayensa da 'yan uwansa, bai b'oye mata komai ba yasanar da ita har zuwa kan yanda 'yan bindiga suka shiga qauyen nasu yau suka karkashe mutane da yanda ya riski gawar iyayen nasu waje daban daban, yaqare tare da fashewa da kuka mai tab'a zuciya, ba madam kad'ai ba hatta yaronta jabir kuka yakeyi, sun matuqar tausayawa Muhriz shida 'yar uwarsa Razina tare da alwashin d'aukarsu 'yan uwan da zasu zame masu jigo suma su zame masu jigo na rayuwa,
Duk da qarancin shekarun Muhriz hakan be hana momyn Jabir zaunawa ta bashi labarin rayuwarta tun daga farkon asalinta dana iyayenta ba har zuwa lokacin data had'u da mahaifin Jabir, Wanda shine silar faruwar qaddarar dake kanta, asalinta Krista ce 'yar asalin enugu, mahaifin Jabir Jamal shiya musuluntar da ita sanadiyar soyayyar dake tsakaninsu ya kuma aureta yazo da ita anan garin katsina mahaifarsa, ko kad'an iyayensa basuji dad'in aurenta da yayi ba amma da yake babu yanda zasuyi tunda yanada halinsa dole suka haqura, bayan aurensu da shekara uku ALLAH yayi masa rasuwa, lokacin Jabir nada shekara biyu aduniya, nan fa 'yan uwan mahaifin Jabir suka tasota gaba da hantara da tsangwama ita da yaronta, wannan dalilin yasata guduwa takoma wajen iyayenta, da yake suma riqaqqin kafuraine masu mugun riqo sai sukace lalle inbata dawoma addininsu ba to tabbas babuta babu su, da taqi amincewa da haka sai suka koreta suma, babu yanda ta iya dole ta dawo nan katsina agidan mijinta, kasancewar mafiya yawansu masu arziqine yasa babu wanda ya damu da tadata daga gidan musamman ganin tanada d'a sai dai suka ja mata kunne akan matuqar tana son su ta zauna lafiya agarin tofa babusu babu ta, kada ta sake ta nuna ta sansu, dama can ita ba yarensu bace ba kuma addininsu ba, d'an uwansu ne yayi karanbanin kawota cikinsu kuma tunda yarasu shikenan babu wata sauran alaqa ko sanayya tsakankaninsu, tayi kuka sosai tayi baqincikin faruwar hakan amma da yake kyakkyawan Imani tayi saita amshi qaddararta da hannu biyu kuma ta tashi tsaye wajen neman na kanta da kuma kula da d'anta da tarbiyarsa, don tasan duk da tarin arziqin da suke dashi bazasu tab'a iya taimakawa yaronta ba daidai dana kwana d'aya, mahaifin Jabir nada wani mashin roba roba, wannan mashin d'in shi yazamo rufin asirinta tun daga lokacin har zuwa yanzu, don kuwa kud'in data siyar dashine ta fara sana'ar abinci dasu kuma sai ALLAH yasa mata albarka aciki, Sam babu ruwanta da kowa inba mutunci ya had'aku da ita ba sannan bata tab'a zuwa roqo wajen kowa ba haka kuma daidai da rana d'aya bata tab'a bari yaronta ya alaqantu da sana'arta ba balle har ta hanasa cikar burin data d'ora akansa na zamowa mai dogaro da kansa shima, tunda ya shekara uku aduniya ta sakashi makaranta both ta boko data arabi, kullum zataje wajen sana'arta shi kuma ta turasa makaranta, gwargwado tayi tsaye tsayin daka wajen bashi tarbiya iya qarfinta tare da nuna masa tsantsar soyayyarsa dake cikin ranta, wacce bako shakka tah'adu biyu ne hadda wacce takeyiwa mahaifinsa,
Duk da tarin gargadin da 'yan uwan mahaifin Jabir sukayi mata akan zuwa wajensu hakan bai hana lokacin daya shekara goma ba ta d'aukesa ta zazzagaya wajensu dashi, saidai bata tab'a sheda masa cewasune dangin mahaifinsa ba gudun kada ya tashi da tsanarsu azuciya saboda ire-iren wulaqancin da sukeyi mata aduk lokacin da suka je wajensu, duk da kasancewar Jabir baisan matsayinsu awajensu ba sai yaji sam baya sonsu ya tsanesu, a tunaninsa suna walaqntasu ne saboda sunada kud'i da tarin arziqi.
Momy tagama bawa Muhriz wannan labarin tare da share hawayen fuskarta, tace
"Daga yau ina so ka d'auke ni uwa, Jabir kuma d'an uwa kuma abokinka, nayi maka alqawarin zanbaka duk kulawar da zan bawa d'ana Jabir a matsayin sadaqatul jariya zuwa ga mijina Jamal mahaifin Jabir, zan kuma kula maka da qanwarka tamkar 'yar cikina kamar yanda zanyi maku, buqatata kawai ku jajirce kuyi karatu sosai, ku nunawa duniya cewa maraici ba shine rashin gata ba kuma babu maraya sai raggo, ni kuma zan tsaya ga karatunku tsayin daka har sai kowanen ku yace ya ishesa, sannan nayi maka alqawari zan tayaka neman 'yan uwanka aduk lokacin daka buqaci hakan"
Goge hawaye Muhriz yayi tare da cewa,
"Shikenan Momy, Nima nayi maki alqawari zanyi maki biyayya iya qarfina tamkar ke kika haifeni sannan zanyi duk abunda kike so matuqar zai sakaki farinciki, wannan kad'ai zanyi agareki yazamo TUKICIN SO da kika nuna mani nida qanwata"
Tun daga lolokacin momyn Jabir ta sake tashi tsaye tsayin daka wajen sana'arta ta kuma saka Muhriz makarantar da Jabir keyi ta tattare duka alhakin kula da Razina ta maida akanta da kuma wacce ke riqa mata aiki Salima, da safe zasu tafi makaranta, in sun taso zuwa la'asar su wuce islamiya, da daddare kuma da kanta takeyi masu lesson, haka rayuwarsu taci gaba da kasancewa har suka kammala secondary ta nema masu admission a alqalam university dake nan cikin katsina inda ta kashe maqudan kud'i masu yawa, saboda ba laifi yanzu kasuwancin nata ya qara bunqasa har ta bud'e qatuwar restaurant acan cikin gari sab'anin da da take da tebur, Razina ma har ta shiga makarantar gaba da primary dake mataki na farko, kasancewar yanayin karatun qasar tamu yasa gaba d'ayansu seda suka shekara biyar cikin ta shidda suka kammala jami'a, inda nan take Muhriz yasamu scholarship d'in zuwa qasar u.s qaro karatunsa na masters, da yake b'angaren pilot ya karanta, shi kuma Jabir business ya gama karatu, ko d'aya Muhriz beso tafiya ba saboda qanwarsa da kuma d'an uwansa Jabir da akoda yaushe take tunanin ya fishi cancanta ga wasu abubuwan amma Momy ta nace akan lalle lalle dole yayi amfani da wannan damar yatafi, babu yanda ya iya saboda baya son sab'a umurninta dole ya haqura lokaci nayi suka d'aga sai qasar u.s, Razina tayi kuka sosai tamkar ance sun rabu dashi kenan, haka ita kanta Mom, Jabir kawai ne ya iya jurewa amma shi kad'ai yasan yanda yake ji azuciyarsa don ba qaramin so yakeyi masa ba, sun matuqar shaquwa dashi sosai saboda basu tab'a rabuwa daidai dana rana d'aya ba sai ranar, komi tare sukeyi komai iri d'aya banbancin ra'ayi kawai ne suka samu wajen karatu, daga shi har Razina saida sukayi zazzab'in tafiyarsa, Momy ma daurewa kawai takeyi gidan ya zama duka sai a hankali,
Bayan tafiyarsa da wata d'aya Momy tafara yiwa Jabir zancen cigaba da karatu, inda yasamu gurbin cigaba da karatunsa a jami'ar b.u.k dake kano, ai kuwa ya kafe kai da fata shi babu inda zai je yabar Momy da Razina, tayi tayi dashi amma yace bazai iya ba, sai kawai ta qyaleshi don sam bata son takurasa, Muhriz kuwa daga can ya riqa turo masa 'yan kud'ad'en da ake basu na lalurori yace ya samu wata sana'a yafara kafin yadawo susan me zasu yi, nan take Jabir yafara business d'in saye da sayarwa na kayan sawa da taimakon Momy ya bud'a shagon botique dana provision, inda shike kula da na kayan sawa wani d'an maqwabcinsu kuma daya gama karatu shima ba aiki Momy tace yayi masu tsaron na provision.
A hankali Kuma kafin ya gama karatu yafara siyo kayan daga can k'asar yana turowa Jabir dasu, idan an sayar sai ya sake had'a kud'in ya tura masa dasu ya turo wasu kayan, cikin shekara biyu da rabi sai gashi arziqi ya fara bud'ewa samarin momyn guda biyu wanda kashi 70 cikin d'ari duka na Muhriz ne, sun so su riqesa bayan gama karatunsa amma yaqi amincewa ya dawo qasarsa kuma cikin ikon ALLAH yana dawowa ya samu aiki anan hilin tashi da saukar jirgi dake abuja, inda wannan ya zamo silar qara bunqasar arziqinsu saboda yawace yawacen da sukeyi na tuqin jirgi daga wannan qasar zuwa waccan qasar sai ya zamana duk qasar da yaje saiya saro kaya acan yazo dasu nan suna sayarwa, lokacin Razina ta kammala karatunta na secondary har Jabir yafara nema mata gurbin karatu,
Jabir mutun ne mai saurin fushi amma yanada saurin sauka, baya son reni ko kad'an haka kuma ya tsani mai kud'i duk inda yake sam baya shiri dasu, sab'anin Muhriz da take da matuqar sauqin kai da haquri, gashi da hangen nesa da tsinkaye sosai, yanada kauda kai ga duk abunda zai b'ata masa rai da barin shiga shirgin duk abunda be shafesa ba shiyasa mutane da yawa suke yimasa kallon mutum mai miskilanci da fad'in rai, wanda kawai ya zauna dashi zai iya fahimtar irin sauqin kan da take dashi.
Watanni biyar ne da suka wuce Jabir yaga wata yarinya anan gaban anguwarsu yaje yace yana sonta ganin irin tarin arziqin da suke dashi yasa takasa fad'a masa bata sonsa yayita kashe mata kud'i, sai da lokaci yayi Jabir yazo mata da zancen aure tace bata sonsa bata qaunarsa, tayi masa wulaqanci da qasqancin da seda yasa Momy zubar da hawaye, babu kalar irin gorin da batayi masa ba ciki har dana ita bazata auri jinin kafurai ba sabuwar musulunta, wanda baza'a iya cewa ga asalin daga ina suka fito ba, ta kuma turo iyayenta wajen Momy suka qarayin wani rashin mutunci akan lalle lalle Jabir yarabar masu da 'ya ko kuma kotu ta rabasu dashi,
Aranar ran Muhriz ya b'aci ganin yanda Momy tashiga wani hali har seda hawan jinin da take dashi ya tashi, har asibiti ta kwanta tana kuka tace yayiwa Jabir magana kada yakoma neman aure anan kusa don ta tabbata babu wanda zai bashi mata matuqar ansan ita kowaye,
Wannan dalilin ne yasa Muhriz d'aukar alwashin duk macen da zai aura bazai tab'a bayyana mata koshi waye ba har sai ta san shi a matsayin baqauyensa d'an asalin qauyen charanci, kuma d'a ga matar da mutane da dama ke qyamata, ya kuma d'aukar mata alqawarin cewa Jabir zaiyi aure anan cikin garin katsina kuma da yarinyar data san koshi waye tasan asalinsa dana mahaifiyarsa ba tare da gori ko tsangwama ba.
_*Back to story😉💃*_
*SHARE*#
*COMMENT*#
*LIKE*#
*ALLAH KAJIQAN IYAYENMU👏😭*