MUNAFUKIN MIJI

By nimcyluv

65.8K 3.6K 1K

Na kasa fahimta da gasgata abinda zuciyata ke ayyana mini a kansa, SO ne ko BIRGEWA?. Komai nasa birgeni yake... More

Author's Note
Shimfiɗa
1 Asibiti
2 Caca
3 Dare
Announcement!
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9
Page 10
Page 11
page 12
Page 13
Page 14
page 15
Page 16
Page 18
Page 19
Page 20
Page 21
Page 22
Page 23
Introduction.
Page 24
Page 25
Page 26
Page 27
Page 28
Page 29
Page 30
Page 31
Page 32
Page 33
Page 34
Page 35
Page 36
Page 37
Chapter 38
Page 39
Page 40
Chapter 41
chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49-50

Page 17

592 33 5
By nimcyluv

Mami ta tsare Baffa da kallo zuciyarta na yi mata soya, ta girgiza kai tare da miƙewa zata fice. Baffa ya tare ta faɗin "Yawwa na ce ki tattara dukkan furnitures ɗin dana siya miki, na bar wa  Ammi su" Maganar ta doki zuciyar Mami ta juya a sanyaye ta ce "Ban gane na tattara kayan ɗakina na bar wa kishiyata su ba, explanation please?" Cike da faɗa Baffa ya ce
  "Ba wani explanation Hausa ce dai na san kina ji ko Fatima?" Ta jinjina kai alamar E, kafin ta ce
  "Bana tunanin akwai wani yare da ka iya wanda ban iya shi ba, ma'ana da hujjar tattara furnitures ɗina na bawa wata ne ban wani ba Alhji Mansur, cikakken bayani"
Kamar zai make ta haka ya tunzura ya ce"Maryam ɗin ce wata? Abokiyar zaman ki ce fa. Ok fine zan maimaita ki tattara komai na ki na bar wa Maryam su ina nufin Ammi, kawai yanzu nake ganin ita ta cancanta da kayan bake ba, kuskure na yi wajan siya miki su wallahi tallahi" Mami ta dinga kallon Baffa ta kasa cewa komai ta fice idanunta na cika da hawayen baƙin ciki.

  Mami na komawa bedroom ɗinta ta fashe da matsanancin kuka mai cin rai, damuwar zuciyarta gabaɗaya ta addabe ta, duk yadda tasu ta yi sharing ɗinta ta wani ta gagara, gashi babbar damuwarta a duk sanda ta buɗe baki da nufin yin addu'a wajan faɗawa Ubangiji halin da take ciki, sai ta ji kamar an rufe mata baki ta kasa ambaton sunan Allah da nufin neman taimako. Ga wani irin masifaffen yanayi da cikin ya saka ta, na buƙatar mace zuwa ga mijinta babu abinda take so irin kasancewa da Alhji Mansur da shaƙar ƙamshin turaren shi. Ta share hawayenta komai yaƙi ƙare wa kamar cin ƙwan makauniyya.
Washegari da sassafe ta kwashe komai nata, ta ce a zo a kwashe Alhji Mansur Rano wato Baffa da kansa ya kira yara suka kwashe tas, ya ce ita kuma a mayar mata da furnitures ɗin Ammi ta ce ta gode. Kwana biyu da yin haka aka shigo da sabbin kaya ƴan Turkiyya masu masifar kyau lokacin suna zaune a parlour Umma ta shigo.
   Ammi ta dinga kallon zubin kayan da tunanin ko Baffa ne ya siya masa sabo fil tana girgiza ƙafa cike da taƙama  ta ce "Kayan ne?" Wani matashin saurayi ne ya ce "E, Hajiya sune ina za a saka" Ya ce yana danne dariyar data kama shi

  "Ok ku haura da su upstairs" cewar Ammi.  Mami ta dinga murmushi kafin ta juya ta ce "Hilal har kun ƙarasu?" Ya ce "E Mami, Mimi na gaishe ki ma" Mami ta miƙe tana murmushi har lokacin ta ce

"Zan kira ta kam, amma kayan sun yi ma sha Allah". "Mami a wajan fa kaf babu irin su kin san kuɗin da Grandfather ya tura? Ai arziƙi ya yi idan kana da kuɗi ka shige duk wani raini da wulaƙanci wlh Mami"
Murmushi kawai Mami ta yi Hilal ya ce "Talk Mami, ai gaskiya ce duk wata mugunta a wajan ɗan talaka aka santa musamman idan ka samu gidan miji ba fus ba ass sai dai a shimfiɗa dugwayen ƙafafuwan na cin banza da damfara, ga mugun abu kamar haihuwar Katsinawa"

  "Wallahi Allah ya shirya ka Hilal Yaya A'isha bata gasa maka baki ba halan?" Ya ɗan kashe murya ya ce "Surprise....."

"What?" Ya mirgina kai ya ce "Na ba ki gari" Ta girgiza kai ta ce "I'm not good da cankar Surprise but i like surprises, just giss me" Hilal ya ce

"Aure zan yi" sai ya ɓata fuska ya ce "Mimi ta ce na yi ƙanƙanta don Allah mene abin ƙanƙanta a nan? Shi aure ai raya sunan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ne, kinga haihuwar fari sai na saka sunan Mamina" Mami ta ce "Kuma kana da gaskiya, amma auren RUƊIN ƘURUCIYA ne"

"Mami Ridayya fa?" A wannan lokacin ita kan ta Umma mahaifiyar Ustaz kallon Mami ta yi tana jira ta ji me za ta ce? Amma ta haɗe rai kamar bata taɓa dariya ba, ganin hakan yasa Hilal yin shiru.
Ammi kunya ta kama ta ganin yadda ya kwafsa, a ranta tana mamakin kuɗi irin na mahaifin Hajja Fatima wato Mami.

Hilal suka fara gyara kaya, Mami kuma ta haɗa musu lunch. Hira suke sosai da Umma tana mata murnar kayan data siya ta ce "Hajja Fatima yaushe  aka zuba miki kaya har kika sauya wasu?" Caraf Ammi ta ce "Lallai fa, cewa ta yi bata so tunda kinga ai haihuwa za ta yi shi ne Baffa ya ce ta bar mini su, da gudu na karɓa ina godiya" Girgiza kai kawai Mami ta yi tana jinjina munafurcin Alhji Mansur Rano. A ranta tana mamakin yadda Ammi ta gane tana da ciki domin kullum cikin hijab take a gidan, kamar wacce take duba?

Ustaz Bilal sai raba Idanu yake a harabar makarantar su Ridayya, a hankali ya dubi a gogon hannunsa ganin ai tuni lokacin tashi ya yi wasu sun jima a gida ma. Ya miƙe daga jinginen da yake a hankali cikin nutsuwa da kamala, tare da zallar haiba da nagartar dake siffanta ainahin Ustazancin shi, ya nufi office ɗin Headmaster a ransa yana ayyana rashin dacewar haɗa mata da maza a makaranta. Da fara'a Headmaster ɗin ya tarbi Ustaz Bilal.
"Irin wannan zuwan bazata haka? Fatan lafiya" Ustaz ya yi shiru yana haɗa kalaman da zai faɗa a gajarce. "Kamar kullum karatun Ridayya sai addu'a, domin tafi gane naka karatun fiye da na mu, babbar damuwar ma kullum cikin bacci take a aji, bata wasa da yara she feels uncomfortable" Ya fiddo da duka littafan ta na makaranta wanda ya amsa wajan class teacher ɗin su, ya nuna wa Ustaz kana ya ce
"Za a Iya magance matsalar ta, ta hanyar cire mata tsoran dake addabar zuciyarta a saka son karatu da nuna mata itama ƴar ce kamar kowa mai gata da ƴan cin zama duk abinda take da buri a duniya, a nuna mata watarana ita uwa ce a nuna mata cewa Ubangiji ke yin halitta ba kuɗi ake bayar wa a kasuwa a siyi mutum ba, buwaya da ƙudirar Allah da girman zati da kaɗaitar shi ce, a nuna mata Ubangiji yana son duka bayinsa kuma babu mummuna a cikin halittun daya halitta, a saka mata ya ƙini da hope na cimma buri, a nuna mata cewa ko wanne mutum yana da nasa raunin cikakken mutum mai asalin kyau shi ne wanda ya yarda da Ubangiji ya kuma yar da ƙaddara. Dukda ba lallai ta gane yanzu ba, amma ya zama na wannan shi ne nata karatun kafin mu ga mai zai faru next"

  "Yaa Rabb"
Ustaz ya furta a taushashe yana lumshe idanunsa, Headmaster baya iya tantance yanayin sauyin fuskar Ustaz Bilal don haka bai fahimci damuwa ko akasarin hakan ba ya ce "Karka damu fa, ina ji a jikina Ridayya zata zama wata a nan gidan duniya, yawanci yara irin wannan suna da baiwa ta musamman" Jinjina kai kawai Ustaz ya yi da ƙyar ya iya buɗe bakinsa ya ce "Ta na ina?" Da mamaki ya ce "Ai mun tashi, ka duba za ka ga babu students a compound" hankalinsu ya tashi a ka shiga neman Ridayya babu ita babu mai kama da ita, har class teacher ɗin su sai da aka kira.

A ɓangaren Ridayya sai rarraba manyan fararen idanunta take yi tana jin me suke faɗa.
"To ko dai Aljana ce ke ko kuma babanki kika gado a muni ko?" Ridayya ta kalli Nimra wacce ta kasance class mate ɗinta a makarantar masu kuɗin dake nan unguwar Darmanawa.
Ɗaya daga cikin students ta fashe da dariya ta ce
"Help me as Nimra, oh oh muni ko wahala?" Nimra ta yi fari da idanu tana riƙe maƙalallen ƙugu idanunta kamar ya fado cike da azaba ta ce

"Yapp, ga idanu kamar na mujiya gata daƙiƙiya sai tsinanen bacci kamar kasa, kullum sai ta yi mana fitsari a class"

"Ohh Goodness! Fitsari?"
Jidda ta faɗa a ruɗe. "Ai yawan sai na ci uwar ta wallahi, baƙa mummuna mai baƙin zunubi ji Idanu kila mayya ce" A sanyaye Ridayya ta ce "Ai dai ɗakin Allah ma baƙi ne"
Da sauri Nimra ta doke bakin Ridayya ta ce"Uban me kika sani? Ke ina kika taɓa ganin ɗakin Allah ɗin? Wannan dama gidan zoo aka kai ma da ita da sallah mu je mu ga daƙiƙiya" Idanun Ridayya ya yi rau rau sai ya fidda wani shiny.

"Ai dabbobi ake sawa a zoo road" Jidda tana dariya sosai ta ce

"To ke ɗin me ce? Wallahi dabba ce ki je ki tambayi Babanki ki ce a dabbobi da wacce kike kama zai faɗa miki" Suka haɗu sukai mata dukan tsiya da bulala wai ba za su saka hannu ba kar su shafi baƙin zunubi. Haka kurum suka tsane ta. Ridayya na son wasa da zarar ta nufe su idan an fita break sai kowa ya daka mata tsawa ya ce ta tafi, daga nan sai ta fi wajan bishiyoyin makarantar ta dinga wasa Ita ɗaya, a lokacin kuma sai ta dinga karatu ita ɗaya ita bata iya gani ta karanta muddin zaka takura mata ta yi karatu to ba zata iyi ba ko a exam ne. Idan ita kaɗai ce kuma sai ta dinga yi tiryen-tiryen a nutse take komai nata.

"Shalele" Da sauri ta ɗaga kai tana kallonsa dukda hawayen dake idanunta bai hana Ridayya sauke ajjiyar zuciya ba, ta nufi wajansa da gudu kafin ta ƙarasa ya ware hannayensa tana zuwa ya ɗauketa ya cira ta sama yana furta "Shalelen Abbiye, You scread me" Ta yi shiru. Jikinta ya ji zafi sosai yana ɗaga rigarta ya ga shatin bulala duka jikinta, ya kalleta tambayar duniya taƙi faɗa masa waɗanda suka dake ta.

Kamar kullum yau ma Ustaz da kansa ya yi wa Ridayya wanka bayan ya naɗe ta da towel ya shirya ta cif cikin wasu sabbin kaya ƴan kanti daya siya mata, ya ɗaure tulin sumar da ribbon yana hakki, yana gamawa ya yi baya tare da kwanciya ta haye ruwan cikinsa tana dariya ta ce "Abbiye gajiya" Idanunsa rufe domin yanzu Ridayya ta zama ƴar lukuta saboda kulawar da yake bata. Ya yi murmushi ta ƙura masa ido,  ganin kumatunsa ya loɓa _Beauty points_ ta danna yatsa a wajan ya ce "Shhhh, Shalale mu je ki yi bacci ko?" Ta maƙale kafaɗa ya rufe ido tana zaune bacci ya ɗauke shi da sauri ta fice ta nufi part ɗin iyayenta.

Lokacin data shiga ba kowa a parlour sai Mami wacce cikinta ya girma kawo yanzu kuma kowa ya san da zamansa hatta shi mai gayya da aiki Alhji Mansur Rano. Jin motsi ya saka Mami juyawa idanunta ya sauka akan Ridayya itama Mamin ta ke kallo. "Lafiya ke kuma?" Ridayya ta girgiza kai sai kuma ta juya zata fita aka ce "Daughter come back" Ammi ta faɗa cike da fara'a da sauri Ridayya ta juya tana murmushi don yanzu ta daina jin tsoran Ammi tunda ta fara nuna mata kulawa da soyayya.

"Yawwa ƴar baba mai iyaye maza biyu ta gaban goshin Abbiey ɗinta Muhammad-Bilal Ustaz" Ridayya ta yi murmushi ta ce "Zauna na baki abin daɗi daughter na"
Mami dai ko motsi ba ta yi ba, Kwata-kwata bata damu da Ridayya ɗin ba, bata taɓa ɗaukar ta ba, tunda take a duniya bata taɓa hira da ita ba ki na seconds ba, sai magana sama-sama. Farfesun nama ta zubo mata hakan ya yi wa Ridayya daɗi tana son nama kuma gashi yanzu Ustaz ya saba mata kullum sai ya siya mata balango ko tsire ko kaza.
Ta cinye tas kana Ammi ta ce "To zo mu je na baki ɗaya abin daɗin"

Hannunta ta kama suka nufi cikin bedroom ɗinta, a zuciyarta tana tsinewa Ridayya tana kuma jin daɗin yadda Mami ke nuna rashin kulawa a kan Ridayya ɗin. Maganin mayen da take bata a kullum, yanzu ma shi ta ɗauka. "Yawwa ungu wannan shanye tas kin ji ko?" Ridayya ta jinjina kai kana ta amsa ta shanye tas kusan cikin kwalba ɗin, kama hannunta ta yi ta ce "Kinga yadda nake son ki ko? Ko me kika ce ina miki haka ne? To Mami da kike gani ba ƙaunar ki take ba, cillar dake ta yi ta ce bata son ki ni kuma na ɗauke ki, ki daina ko gaishe ta kina ji?" Ridayya ta jinjina kai ta ce "Ai shi ne take mini haka...,"

Ta yi maganar tana yin harara da taɓe baki ta ce "Yaya sunan wannan abin Ammi?"Ammi ta ce "Yana nufin na tsane ki, kuma sai na kashe ki"

"Ta kashe ni na bar ganin Abbiey?" Ammi ta ɓata fuska ta ce "Abbiey kawai bani?" Ta yi shiru kan ta a ƙasa can ta ce "Ni ma na tsane ta, zan ɗauki wuƙa na caka mata"

  BATSARI /KATSINA.
  Yanayin duhun samaniyya da yadda daddaɗar iska ke kaɗawa, gari ya yi shiru sai kukan tsuntsaye da tashin ledoji zuwa sama zai tabbatar maka a tsakiyar watan Agusta ake. Yau ruwa gobe ruwa, hakan ya yi dab da shigowar watan azumin Ramadan. Yau ma kamar kullum garin ya yi baƙiƙƙirin gajimare sai gudu yake, ana wata kalar walƙiyya da iska mai ƙarfi dake tashi tana yaye gutsirarrun rufin saman wani gidan mai ƙarar kwana. Hankulan jama'ar ƙauyen Nahuta dake yankin ƙaramar hukumar Batsari, ya fara tashi ganin hadarin yau na musamman ne, wanda suke gonaki suka fara shirin dawowa gida, wanda suka fita bara suka fara tattaro tarkacansu suna ɗaukar hanyar gida, matan da suka fita garuwa suma duk suka yo hanyar gida, aka dinga kama awakai da shanu ana ɗaure su.

Kamar yadda Hausawa ke yin lakabi da sunan “Katsinawan Dikko, kunya gare ku ba dai tsoro ba” Gefe guda kuma wasu su ce “Ta Dikko ɗakin kara" Hakan ɗin ce ta kasance a cikin wani fafakeken gida, wanda zubi da tsarin shi bashi da mara da gidan gandu. Gida ne mai rangwamen ƙarfi, ga tarin yara manya da ƙanana kasancewar mata huɗu ne a gidan, idan ka ɗauke surukansu da duk suke tare waje guda. A daidai sanda ruwan saman ya fara sauka a sannan ne ya fito daga ɗan ƙaramin ɗakin da take ciki mai kama da Bukkar Fulani mita take kamar ta ari baki

"Ni wannan masifa da bala'in na cikin gidan nan ya ishe ni, masifa kamar ana tuttula mata man fetir, hoɗijam!" Ta faɗa tana yin turken awakai tare da kama gudu wacce ta kifo mata da ƙazon data shanya,sai ta yi wa akuyar dokan kawo wuƙa kana ta ɗaure. Ta kalli sama ganin yadda cita ke ta gudu ta ce

"Ko a ina Gaaji ta samu gindin zama?" Kafin ta shige ɗaki yariyar ta shigo da gudu tana haki saboda ruwan daya fara dukan ta. Kallon tsaf ta yi mata kafin ta ce "Hala kin kwana turo? Hakin ga na lafiya?" Gaaji ta ce "Iya don ki ji Gidaɗo ya zo, ya dawo daga birni" A guje sauran yaran suka fito daga ɗaki suna murna yau za su ci abu mai daɗi da kyau. Iya ta ce "Ke ƙarya, Gidaɗo nawa? Yaushe ya zo babu labari"
"Yana bisa hanya" Rufe bakin Gaaji kenan ya faɗo gidan yana cin magani sai taɓe baki yake yana kakkabe jikinsa. Jikin Gaaji na rawa ta ce "Ina taimaka maka kawo jakar tafiyar" Tana zuwa ya saka hannu ya sakar mata ranƙwashi ya ce "Kina ƙara taɓa mini kaya sai na ci ubanki, ƴar ƙauyen banza" Da sauri ta matsa tana sosa kan ta. Iya ta ce "Sannu lale me ka zo mana da shi? Kawo jakar naga?" Ya haɗe fuska tamau ya ce "Ke Iya nan kamar kin bani ajjiya, wai karatu na je yi ne ko neman kuɗi?" Ta riƙe baki
"Kake faɗa mini haka Gidaɗo?" Ya ce "Gaskiya ce ai, ba ki ce Gidaɗo ya karatu ba sai me na zo da shi, ko tunanin na mutu a can bakwa yi kun kai ni gari kun zube babu mai zuwa, sai ni nima daga sallah sai sallah ko idan na yi wata ƙaryar"

"To zage ni ka huta Gidaɗo, ni dai bani burodi" Ya ƙara yin kicin-kicin da rai ya ce "Point of correction, biredi ake cewa Iya"

"Bari na je na faɗawa Hanne ka zo" Iya ta ce "Maza ki faɗa mata, a zo a yi maganar aurenku" Gidaɗo ya kalli Gaaji ya ce "Wallahi kika fita kika gaya mata sai na yi miki shegen duka ƴar banza da baki kamar na aku" Haka daga shigowarsa suka fara yi da baki daman babu kowa namiji a gidan sai Jafar shekarar shi Bakwai shirin kai shi Maiduguri ake wajan sauran yayyensu da suke can.
"Ka je gona, lokacin girbi ya kusa za mu samu albakar noma na hatsi sosai" Gidaɗo ya miƙe ya ce "Ku za ku iya cin hantsi ni na yi hannun riga da shi, noma kuma a yanzu gaskiya Iya sai dai ku yi haƙuri na fi ƙarfinta" Kafin Iya ta yi magana an tsuge da ruwan saman, da gudu Gaaji ta fice daga cikin gidan ta nufi gidan su Hanne ta shaida mata Gidaɗo ya dawo.

  Gidaɗo na zaune a ƙofar gidansu ya ci wani uban yadi yellow ful da shi, da ƙaton takalmi ga wani irin glasses daya saka a fuskarsa ya haɗe rai, kasancewar fari ne jajur da shi irin farin Fulanin usul kuma Katsinawa ya yi wani irin kyau da shi, yara sun zagaye shi ƴan mata nata leƙo katanga suna kallo Giɗaɗon birni, hatta matan aure kallonsa suke wasu da alwashin tattara yaransu sukai su Almajiranci don kallo ɗaya za ka yi wa Giɗaɗo kasan yana saurarawa.
"Giɗaɗona" Ya cira kai da ƙyar yana kallonta, haka kawai ya ji ransa ya ɓaci tas, saboda kwalliyar da yaga ta yi ta ci uban jambaki har ƙasan leɓe haƙoranta jajur nan da nan ya ji zuciyarsa na tashi. Hanne ta washe baki ta ce "Giɗaɗo ni ce Hannenka, ta Giɗaɗo ikon Allah dole mu saka maƙiyanmu dariya" Ya ɗaga kafaɗa a dole shi wani shege ne ya ce "Ni daman na jima da saka su kukan, tunda na je birni ko ba kiga yadda ake ta kallona ba, saboda na celeborotin a ƙauyen Nahutun Batsari" Hanne ta yi fari da ido sosai ta ce "Sai ni Hannen Giɗaɗo, mijina da izinin Allah, na haifa maka ƴa ƴa kallo su karime su Baɗejo duk an yi musu aure don ka ji" Giɗaɗo ya taɓe baki sosai yana kallon Hanne sosai da ne take burge shi yake mutuwar son ta amma tunda ya fahimci inda mata suke ya gane Hanne ba komai bace
  "Dube ki da kyau Hannen Nahutun Batsari, gaskiya bana miki kallon mace a yanzu, infat ma ba zan iya auren ki ba" Shi a dole a iya turanci haka Giɗaɗo yake jin kansa, babu shakka da sarauniyar Ingila za ta jisa sai ta yi masa kukan baƙin ciki.
  "Me kake nufi? Ni ce Hannenka fa? Ka manta kalle ni" Ta faɗa tana jujjuya wa. Tas ya kalleta sai ya yi miskilin murmushi ya ce "Hanne ƙuruciya, Hanne kwaila, Hanne wawta, Hanne ƙauyanci, Hanne daƙiƙanci, Hanne no no no kai Hanne ba zan iya ba" Idanunta ya cika da hawaye gabaɗaya shekarunta Goma sha biyu ne a duniya amma tana da jiki kyakkawa da ita, amma tasan soyayya ta san aure tunda tun suna yara ake aurar da su."Ban fahimta ba?"
Giɗaɗo ya ce "Kalli ƙirjinki, idan na haɗa na cure su a tafin hannu ba su fi curin tumatir ɗan biyu biyar ba a birni, mazaunanki kam sai addu'a, ina taɓe su ba zai shige yankan biredi ɗan hamsin ba, ki je kiga matan birni yadda suke da kaya murguza murguza kamar sun ɗora ai zan nemi wata kawai"
Kuka Hanne ta fashe da shi don a duniya ba wanda take ƙauna sama da Giɗaɗo fari ɗan kyakkawan saurayinta haka tana kiran sunansa ya yi burus yana ji a ransa yanzu Hanne ba tsarar auren shi ba ce.

  Haihuwar Mami ta yi daidai da samun aikin da Muhammad-Bilal Ustaz ya samu a wani Lagos. Aikin banki ne a Fidelity bank plc, dake Kofo Abayomi street victoria Island Lagos. Haihuwar Mami ya ƙara kawowa Alhji Mansur Rano buɗi, sosai ya nuna farin ciki da samun fara yarinya mai tsananin kama da Mami, kyakkawa asalin kyau na ban mamaki fari kamar ya yi magana. Baffa ya ɗaga babyn da tuni an yi suna ya ce "Sai yanzu kika haifo kalar zuri'ar Mansur Rano, yarinya kalar kyau ina alfahari da samun Zainura ita ɗin cikon farin cikina ce" Ridayya dake gefe ta yi zuru da Idanu ya kalle ta ya ce
"Da an haifo mai kama da jakin dawa na gidan zoo, baƙi kamar zunubi Idanu daƙwa-daƙwa gabaɗaya suffar Aljanu ce da ita, ji nake dama ta mutu domin bata da wani amfani" Mami ta yi shiru idanunta a kan fuskar Zainura. Ammi ta ce "Haba Baffa wannan cin mutunci ne, duk lalacewar goma ai tafi biyar albarka, kafin Zainura Ridayya ce ta fara zuwa duniya" Ya yi murmushi ya ce "Maryam kenan, ke kin fi uwar yarinyar sanin ciwon ƴar banda kina son ta da tuni na cire ta daga cikin zuri'a ta don ina kokwanto da ƙyar idan ba ƴan ruwa bane suka sauya ta a ciki, domin da yaran Aljanu take kama"

  "Alhaji Mansur idan fitsari banza ne kaza ta yi mana, kana da kasuwar samun kamar Ridayya ɗin? Ko zaka iya ƙera irin ta ne? Ai ko yanzu kura ta faɗi tafi ƙarfin Allah wadai" Baffa ya ce
"Bana son kina mini haushi kamar na kura Kaltum ba ruwana dake" Ta yi murmushi ta ce "Ai kura haushi ɗaya take yi wanda ka ji yau shi zaka ji gobe, ina son ka fahimce cewa ko yanzu ka mutu babu abinda zai hana Ridayya cin gadonka, daɗin abin kai ka kawo kan ka ma, idan ka ga dama ka tafi ruwan, domin Ridayya bata ɗauke ka matsayin uba ba" Tana faɗin hakan ta miƙe ta kalli Mami ta ce "Ke kuma shasha wacce bata san daraja da kimar kanta ba, yadda kike nuna ko in kula a kan Ridayya ki sani akwai ranar da za ki yi ladamar hakan ƙwarai da gaske"

Rayuwa ta juyawa Ridayya domin har Zainura ta tashi ta fara wayo bata kula ta, cikin lallami da dabara Ammi take nunawa Zainura Ridayya ƴar tsintuwa ce a gidan kuma mayya ce kar ta yadda ta dinga kula ta wannan dalilin yasa Zainura ta kewa yayar tata kallon hadarin kaji, ba ruwanta da Ridayya wani lokacin har hana ta zuwan gidan take kullum tana part ɗin Baba ƙarami wajan Abbiey. Zahura ta yi aurenta daman ita karatun bai dame ta ba, Balkisa ta karanci ɓangaren jarida tana aiki a gidan rediyon Liberty itama haihuwarta uku.

A gajiye Ridayya ta shigo idanunta lumshe saboda gajiya shekarunta Goma sha biyar ciff a duniya amma jikinta ya buɗe saboda tsananin kulawar Abbiey komai ya samu ita komai Shalale shiga matsala da damuwa da yawa sabo da ita amma ba wanda ya sanni ya ci bashi daga wajan jama'a saboda ya kula da ita nan ma babu wanda ya sani daga shi sai Allah sai mutanen. Kasancewar ta san Abbiey baya gari ya saka ranta duka a ɓace yake ta cire hijab ɗinta gashinta ya baje ta gire skirt ɗin makarantar sai ɗan ƙaramin gajeren sabon wanda da Abbiye ya siya mata ya zauna daidai da cibiyoyinta da suke da kyalli saboda baƙi ko'ina luff da gargasa ta miƙe tsaye. Madaidaicin ƙugunta a buɗe yake zaune daram Ubangiji ya bawa Ridayya dirin da surar jiki waist ɗinta tamkar ya yi magana har yanzu dai bata fara Irgan dangi ba. Ta ƙura wa kanta Idanu ta cikin madubi sosai take kallon kamar ta sai ta yi murmushi while hawaye na zuba a idanunta a hankali tana kwaɓe fuska cikin siririyar muryarta ta ce "Da gaske dai ni mummuna ce, me ya sa duka ni kaɗai ce baƙa mummuna a gidanmu? Me ya sa na girmi Zainu amma ita fara kyakkawa,me ya sa? Me ya sa?" Ta faɗa tana fashewa da kuka. Tunda Ridayya ta samu lafiya take so da ƙaunar farar fata da kwalliya gayu da ƙwalisa mutum irin haka yana masifar burgeta tasha yin kwalliya amma ita bata yin kyau.

"Ya kamata ki yi farin ciki Ridha kin kammala final exam na secondary school" Wata zuciyar ta furta hakan domin Ustaz da kansa ya saka a yi wa Ridayya tsallaken aji saboda girman jikinta kuma ya samu kwakwalwar ta buɗe tunda ya bi shawarar Headmaster ya firgitar da Ridayya ya ce ai mutuwa zai yi yau ya kwanta a gado yana kakari har ya daina motsi ranar har suma sai da ta yi sai da ya yi ladama ya rungume ta a jikinsa yana jijjigata hankali tashe. Tunda daga ranar ta samu nutsuwa idan ta tuna da zarar bata karatu Abbiey zai mutu ta miƙe sosai.

    "Abbieyna ka dawo kaga na yi karatu an bani gift ka ji Abbiey" Ta faɗa tana lumshe idanunta tana jin duk gashin kanta ya dame ta. Ba tare data damu ba ta saka slippers ta nufi parlour wajan Umma ta ce mata ta dawo yunwa take ji. Cak ta tsaya jikinta na rawa da ɓari idanunta ƙuri a kan Abbiye ɗinta wanda ya hakimce a saman kujera hannunsa riƙe da kofi yana shan black tea. Jallabiyya ce a jikinsa yau sumar kansa duk a cuccure kamar baya cikin nutsuwarsa. A hankali ya saka hannu ya mayar da sumar kan nasa zuwa baya yana ɗauke hannun ta ƙara dawowa gaban goshin, ya ɗan ɓata fuska a jikinsa ya ji ana kallonsa, yanayin yadda tsigar jikinsa ke tashi ya fahimci ba kowa ke kallonsa ba sai Shalale.

"How long will it take you to stop looking at me?" Murmushi ta yi idanunta na rufe wa sai kuma ta nufe shi da sassarfa domin mamakin ganinsa ya hanata motsi gabaɗaya kwanan shi biyu ta tafiya Lagos ɗin. Tana zuwa kusa da shi ya ajjiye kofin yana miƙewa tsaya tare da ƙoƙarin yin baya zai juya yabar parlourn. Ridayya ta yi saurin rungume Abbiey fararen haƙoranta na bayyana ta ce "Oyoyo Abbieyn Shalele i miss You mardly" A kasalance ta fara idanunta da suke cike da maye a rufe. Ustaz ji ya yi ta sakar masa nauyi ya saka hannu ya ciro ta daga jikinsa ya riƙe kafaɗunta tare da jijjigata.
"Yes Abbiey.... Yes yes Wlcm back" Ta faɗa a rarrabe ganin ko idanunta ta kasa buɗewa ya saka Ustaz taɓa kumatunta wanda yake da laushi kamar audiga da ƙyar ya ce "Ustaza, open your eyes Ustaza" Dake tunda ta yi sauka yake ce mata Ustaza.

Kafin ya yi motsi ya ji ta yi baya tare da faɗuwa ƙasa tim kamar saukar buhun siminti nan take gefen kanta ya fashe jikinta ya fara da kakkarwa ta shiga cuccure wa da kanannaɗewa tamkar maciji.

Ku yi haƙuri bisa jina shiru da kuka yi ayyuka ne sukai yawa😢🥹A yafewa Mar'atussaliha Saliha idan naga comment da yawa sosai da sosai birjik zuwa anjima za ku ga new update.

08164069385
Whatsapp only please

Continue Reading

You'll Also Like

897K 38.6K 51
Warning ⚠️ ပေးတာမို့ Sensitive ဖြစ်လျှင်ကျော်ဖတ်ပါရန် မေတ္တာရပ်ခံအပ်ပါတယ် Party တစ်ခုမှ ဆေးမိပြီး လူတစ်ယောက်နဲ့အိပ်ခဲ့မိတယ်။ အဲလူက ကျွန်တော့်အလုပ်ရှ...
203K 2.3K 36
"I'd do anything for her. I would kill every last fucking person on this planet, if she asked me to. And I wouldn't even question her about it. All s...
365K 26.6K 50
[Under editing] "Charche nashe ke chal rahe the main zikr teri aankhon ka kr aaya, jab baat sukoon ki chidi main baat t...
232K 4.5K 20
အပိုင်းအားလုံးနီးပါးမှောင်ပြီး warningတွေများမှာမို့ အမှောင်မကြိုက်သူများ အသက်မပြည့်သေးဘူးများကျော်သွားကြပါရှင့်