🌳 *QADDARAR RAYUWA* 🌳
Written by 🌺 *CUTTIEEMEERAH* 😘
5⃣2⃣
🌳🌺😘
Three months bayan aurensu suna zaune chikin kwanchiyar hankali da farinchiki, kana kallan ma'auratan kasan babu abunda ke chikin zuchiyoyinsu illa soyayya da fahimtar juna, ah 6angaren shukuriyya ma ita batasan chewar tana san haiydar sosai haka ba sai bayan sunyi aure, wani irin qaunarshi takeji kullum yana qara shiga chikin zuchiyarta,,, she can't even imaging how her lyf would be without him,,,, endless love take mishi which she nvr thought xata ma wani irinshi, shikuwa haiydar kullum yana zuwa wurin kasuwanchinshi, including asabar da lahadi, saboda shi yana ganin wad'anda sukachi suka tada kai sune suke za6an ranar zuwa kasuwa, shi kuwa dayake da burika kala-kala baya tunanin ze zauna yanzu, dan haka kullum yake zuwa kasuwa......
Shukuriyya batada wani matsala yanxu ah rayuwarta, siblings d'inta suna yawan ziyartar ta, kuma ko basuxo ba they are always in touch with each other on phone, gashi mijinta yana bata kulawa daidai gwargwado,, saidai wani lokachin takan kasa fahimtar haiydar, wani bin saitaga kamar komi dayake mata kamar yana forcing kanshi nerh, saitaga kaman pretending kawai yakeyi, bcoux tana iya gano ainahinshi ah wani 6angare na zuchiyarta, he don't actually cares about anything, he just pretend to,, amma ahaka dai take binshi suke zaune, tunda dai bawai koyaushene yake nuna halin ko inkula d'inshi bah....
🌳🌺😘
Yau lahadi nerh, tun sassafe shukuriyya ta tashi kamar kullum, ta gyara ko ina ah chikin gidanta chikin mintuna qalilan dan daman gidan ba wani wahalar gyarashi takeyi ba dan bashida wani girma sosai, tana gama kintsa ko ina taje ta fara ferayar doya, tagama tsaf sannan ta kad'a kwai ta soya tazuba ah container takai parlour ta ajje sannan ta dafa tea tazuba ah flask shima takai ta ajje, wanka taje tayi sannan tafito ta kintsa kanta tayi light makeup, ready made d'in doguwar riga tasaka which is armless blue in colour, sannan tasaka black d'in hula me blue stones ajiki, baqaramun kyau tayi ahakan ba, tana shirin fitowa daga dakinta taga haiydar yafito daga nashi d'akin, qarasawa tayi tad'anyi side hugging nashi sannan suka gaisa, ganin beyi shirin fita kasuwa ba yasata fad'in
"Yau baxakaje kasuwar bane?"
"Banjin dad'in jikina sosai nerh, zanzauna ind'an huta"
"Eyyer sorry swt lurv, Allah yabaka lafiya,,,, kaima Kaine ai bakasan hutawa ko kad'an"
Tafad'a chikin shagwaba
"Bagashinan na zauna zan huta d'inba"
Yafad'a yana Jan hanchinta
Murmushi tamishi sannan tajashi parlour suka zauna, sai kallanta yake ganin yanda ta mishi kyau, amma yakasa furtamata, ita sosai take mamakin wani hali na haiydar wanda baxe ta6a kallanka yache kayi kyau bah, duk iya kwalliyar daxatayi baxe ta6a furta mata tayi kyau bah, saidai kawai ya kalla yad'auke idonshi kaman bega komai bah, abun yana matuqar damunta kuma tarasa yanda zata 6ullowa al"'amarin, dafari ta d'auka zata iya jurewa amma zuwa yanxu abun ya dameta sosai,,,,,
Sauka tayi ah kan kujerar tahad'a mishi tea sannan tafara feeding dinshi dakanta as usual, tana saka mishi yam d'in abakinshi taga ya fito dashi, dagowa tayi tad'an kalleshi ad'an tsorache ganin yanda ya firzar da doyar daga bakinshi
"Meyafaru?"
Shukuriyya ta tambaya
"Haba shukuriyya!! Sau nawa zan gaya miki kidaina dafa doyar nan kafin ki soya?,, umnn"
Chikin fad'a fad'a yake mata maganar, itakuwa sanin batada gaskiya yasata tayi shiru kawai batache komi bah
"Magana nake miki fah"
Yaqara commanding
"Kayi haquri, am sorry, namantane wallahi"
Tafad'a hawaye sirara yana gangaro mata dan batasan fadan haiydar ko kadan, ganin tafara hawayen yasashi furta "shikenan ai", sannan yad'auka cup d'in tea yafara sha, shanyewa yayi tas batareda yachi doyar bah, ganin yashanshe shayin kuma yana shirin miqewa yasata furta
"Baxakachi bane?"
Tafad'a tana pointing doyar
"Banachi"
Yafad'a yana miqewa daka wurin dan zuwa wanke bakinshi, binshi kawai tayi da ido tana kallo, kullum masifarshi qaruwa takeyi, kuma komai zatayi agidan yunqurin burgeshi takeyi amma ta lura sam ba'a mishi gwaninta shi....
Juyawa tayi tachigaba da chin abinchinta har tagama sannan ta kwashe komai tayi kitchen dashi, haka ta wanke su duka sannan tadawo parlour taxauna....
Yana zaune akan kujera yamiqe qafarshi yana kallan ceiling, kallanta kawai yad'anyi yamata murmushi kaman bashine yamata fad'a yanxu bah sannan yajuyarda kanshi,,,,
abun mamakin haiydar ma yawadai gareshi, gashi zeyi maka laifi amma baxai ta6a baka haquri bah, sannan kokaine kamishi laifi kabashi haquri to baxai kwantar da kanshi ku rarrashi juna tare bah, hali guda d'aya dayake dashi wanda yake burgeta shine bashida riqo ko kad'an, daxarar tamishi laifi kafin tabar wurinma ya wuche awurinshi, to wannan nerh kad'ai zatayi shaidarshi akai....
Ganin yanda yaketa karkad'a qafa yana chije la6e yasa taje ta d'auko mishi pain killer tabashi yasha, tambayarshi tayi kozasuje asibiti amma sam yache babu inda zaije, sai kawai ta qyaleshi taxauna tana mishi messaging tana mishi hira, tasan yanaso shiyasa take yawan yi mishi, yaud'in ganin yanata basar da hirar tata baya tankata yasata yin shiru kawai tadaina mishi hirar saidai messaging d'in data chigaba da mishi,,, saida taga bacchi yafara d'aukarshi sannan ta tashi ta koma daki tayi zamanta....
Sotakeyi tayi tunani amma tarasa tunanin me zatayi, gaba d'aya haiydar ya chanja mata kwana biyunnan, saiya dunga ignoring d'inta, amma aranta saitakejin qila wahalhalun kasuwane kawai suka fara mishi yawa, sai kawai ta kawar da zanche daga zuchiyarta ta kwanta tayi barchinta....
Bata farkaba sai wurin 1:40, tana farkawa idanta yasauka akan agogon dake dakinta, dasaurinta ta miqe ta nufi toilet tayi wanka tayi alwala sannan tafito tasaka doguwar rigan atamfa ta tayarda sallah, tana idarwa tafito parlour, ganin haiydar baya wurin yasata nufar dakinsa, baya chikin d'akin dan haka tayi tunanin qila yafita nerh, kitchen ta nufah tayi Sauri ta d'aura taliya, dukda ma haiydar yahanata yawan dafamishi taliya datakeyi saboda shi bayaso, amma ganin lokachi ya qure dayawa yasata kawai tadafa mishi taliyar, tana gamawa tajuye ah flask tafito ta ajje, daman tanada miya sai kawai tayi warming sannan ta juye taxo ta ajjemishi ah parlour,,,
Sai bayan la'asar yashigo gidan lokachin tagama komi, sannu daxuwa tachemishi sannan ta kar6i ledan dayake hannunshi, tayi kitchen dashi sannan ta dawo parlorn
"Da yunwata na dawo"
Yafad'a yana yatsina fuska
"Ina kaje kaid'in toh? Kaida ba lafiya bah"
Ta tambaya da damuwa ah fuskarta
"Naje gaisheda abba nerh fah"
Yamutsa fuska shukuriyya tayi kaman zatayi kuka kafin tache
"Shine baka tafi dani bah"
"Keda kike bacchi tayaya xan tasheki"
Yafad'a yana mata dariyar qeta
Aikuwa taqara 6ata fuskanta, ganin zata mishi kuka yasa yache tabari any time soon ze kaita itama, saida yafad'i haka sannan tasaki ranta
"Zozo ki zubamun abinchinnan"
Yafad'a yana zama aqasa, dan yunwa yakeji
Qarasawa tayi ta zauna gaban abinchin sannan ta dauko plate d'in ta bud'e flask d'in, tana bud'ewa haiydar ya 6ata ranshi, danshifah yatsani ko ganin taliya nerh, danshi be d'auketa ah matsayin abinchi bah, itama kanta shukuriyya tana zuba mishi tana satar kallan fuskanshi, dan so takeyi taga reaction d'inshi, tana gama zubawa tasaka mishi miya akai sannan ta miqa mishi gabanshi ta ajje
"Kayi haquri, ban tashi dawuri bane kuma naga lokachi yaqure idan nache zan dafa wani abun me wahala, bansan kadawo kanajin yunwa bangama abinchinba shiyasa na dafa taliyan buh am sorry"
Tagaya tana kallan fingers d'inta
"Shikenan ai"
Yafurta yana Jan kwanan gabanshi, kafin yafarachi yache
"Kije ki yankomun fruits d'in danaxo dasu yanxu"
Yana gama fad'a tamiqe tayi hanyar kitchen, tana shiga ta d'auko ledar dayashigo dashi yanxu d'in, kafin ta ta6a komai achiki taji yana kwala mata kira
"Shukuriyya!!! Shukuriyya!!'
Dasaurinta tafito dan yarda yake qwala mata kira,,, tana fitowa taxo gabanshi dasauri ta tsaya dana warwara idanu kalar rashin gaskiya
"Kekam bakijin magana koh?, nache bakijin maganata nerh komi?, wannan miyache?"
Yafad'a yana nuna plate d'in abinchin, batareda yabari tayi magana bah yaqara mata ihu arazane
"Nache wannan miyache??, shin anya kin iya girki kuwa shukuriyya, kullum kalar dahuwar abinchinki daban take, inajin ko Maggi bakisaka achiki ba bare gishiri, meke damunkine, saunawa zanche kidaina mun abinchin yan prison achikin gidana ehhe??,,,"
"kizoki d'auke abunki banachi"
Yafad'a yana tura mata plate d'in gabanta har taliyan yana zubewa
"Wallahi bn....."
"Kar inji kinche uffan, d'auki abunki ki tafi"
Yayi interrupting nata, batache komi ba ta sunkuya ta d'auki abinchinta sannan tayi hanyar kitchen dashi, tana shiga kitchen tafashe da kukan da batasan dalilinshi bah, wannan yana d'aya daga chikin matsalolin dasuka fara samu da haiydar achikin zaman aurensu wato abinchi, shi koyaushe da yarda yakesan abinchinshi ya kasanche, itakuma yarda yakeso d'in bahaka tasaba bah, but still tana ganin zata dunga mishi yadda yakeso indai har hakan zaisa azauna lafiya,,,,,
Ajje plate d'in abinchin tayi agefe sannan tafito da fruits d'in daga ladernsu, lemo nerh da banana, sai kawai ta yanka mishi lemon tazuba ah wani bowl med'an girma sannan tazuba mishi banana ah plate d'in tafito ta kai mishi, tana ajje mishi yad'auko yafara sha dan babu komi achikinshi tun tea d'in dayasha da safe
"Kimun juice na orange d'in"
Yafad'a yana gutsirar ayabar, toh tache mishi kawai sannan takoma kitchen, tana shiga kitchen d'in ta6are orange d'in duka sannan tamishi juice d'in dashi, tana gamawa tafito dashi taje tasa ah fridge dan tasan sai dare zesha,,,,,
komawa tayi kitchen d'in ta d'aura mishi shinkafa, sannan tayi markad'en kayan miya tamishi kalar miyar da yake so, saida tagama tsaf sannan tafito lokachin har anfara kiran maghriba, tana fitowa tahangoshi yana qoqarin fita daga gate meaning zaije masallachi kenan, itama d'aki ta tafi taje tayi sallah abunta, yana idarda sallah yadawo sannan ta gabatar mishi da abinchi, tana zuba mishi yana kallanta dan qiris yake jira yaji abinchin beyibah yafara masifah, yanafarachi kuma yaji taste d'in is ok komai yaji sannan ya kwantar da hankalinshi yafara chi, zubamishi juice dinnashi tayi ah cup sannan ta miqe taje ta d'auko taliyan data dafa daxu tafarachi, kallanta kawai yad'ago yayi, harxeyi mata magana saikawai ya shareta
"Bakichi banana d'in bah fah, ko yauma baxakichi bah?"
Yafad'a yana kallanta
Daga mishi kanta kawai tayi forgetting that yahanata tadunga mishi body contact, shareta yayi sannan yache
" lemon kumafah?, koshima bakyasha?"
"Eh"
Kawai tache mishi sannan tachigaba dachin abinchinta, shima shareta yayi yachigaba da chin abinchinsa, azuchiyarshi yana mamakin kinibibi irinna shukuriyya komai batachi saboda tsabar tsurfa, banda shegen iyayi irinnata ai ko mutum bechin komai ai yanashan fruits amma ita banda ita....
Abinchinshi yachigaba dachi haryagama yashanye juice d'inshi tas, dan sosai yamishi dad'i, amma yabud'e baki yache yayi dad'i sam yakasa fad'a mata, yana gamawa ta kwashe komai takai kitchen ta wankesu sannan ta dawo,,,,,
soyakeyi yache mata tayi haquri ganin yanda taketa 6ata rai amma sam yakasa furtawa, sai kawai yakoma kusada ita yafara d'auke mata hankali da saqonninshi, dahaka ma tamanta da abunda yafaru daxun suka chigabada soyayyarsu.
*MEERAH*