WATA FUSKA

By 68Billygaladanchi

200K 17.2K 1.2K

Sosai take a tsorace, ganin komai take tamkar a mafarki ji takeyi tamkar ma ace bata rayuwa a doron qasar, se... More

page 2
page 3
page 4
page 5
page 6
page 7
page 8
page 9
page 10
page 11
page 12
page 13
page 14
page 15
page 16
page 17
page 18
page 19
page 20
page 21
page 22
page 23
page 24
page 25
page 26
page 27
page 28
page 29
page 30
page 31
page 32
page 33
page 34
page 35
page 36
page 37
page 38
page 39
page 40
page 41
page 42
page 43
page 44
page 45
46
page 47
page 48
page 49
page 50

page 1

12.8K 612 41
By 68Billygaladanchi

*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*

*🗿WATA FUSKA🗿*

🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉

*Billy galadanchi*

*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*

01

Cikeda nutsuwarta take tafiya dukda yake yanayin ta kad'ai ya isa ya sanar dakai cewar lallai a gajiye take kuma kallon farko dazakawa fuskarta zaka tabbatar cewar lallai tana tattare da yunwa matsananciya.....batada sukuni batada cikakkiyar lapia tamkar wacce qwai ya fashewa aciki.... Iyakar inda aka direta bakin first gate na jami'ar usman d'anfodio d'in batada ko sisi!!! Batasan se yaushe zata isa gidansu ba dake low-cost.....Mataccen agogon dake wutsiyar hannunta daduk fatarshi ta gama tashi ta wurgawa kallo qarfe bakwai ta kusa....magrib kenan fa ta doso kai idan hakane tashiga ukunta da Baba iro...... Cira kafarta tayi taci gaba da tafiya sauri da sauri......se gab da isha ta isa k'ofar gidansu Babur d'in Baba iro ta wurgawa kallo ta tabbatar yau kashinta ya bushe batasan me aka gaya masa ba,batasan qazafin da za'a mata ba....batasan me ze mata ba!!!! Cikin dokawar qirji ta shura qafarta zuwa cikin gidan had'e da wara Bakinta dasunan yin sallam amma jin muryar Baba Azumi ne ya dakatar da ita....

"Ban isa in gayawa Nanuwa tajiba malam, Ban isa na hanata fita yawonta na banza ba, d'ari biyar daka bayar na basu yanda na baiwa Ummul haka itama na bata amma tunda tafice gidannan da safe har yanzu bata shigo ba nime zance?" Kwafa tajiyo shi yayi kanyace

"Yau sena wulaqanta rayuwarta kuwa agidannan wlhy, badai burinta ta b'atan suna da sunan gida ba wlhy bata isaba aiba gidan ubanta bane nan d'in" girjinta ne ya doka amma a haka murya na rawa tae sallama, da sauri Baba azumi tazo gunta

"Nanuwa lapia kuwa meya tsaidaki se yanzu kika shigo? Gashi kuma Baban ku se fad'a yakeyi,mesa bakyajine wai?" K'wallan datake qoqarin tarewa ne ya silalo mata tace

"Baba Azumi a qafa fa na dawo" wara ido tae da mamaki

"Kud'in motarki fad'uwa yae ne?" Mamakinta ya sanya Nanuwa kasa magana ta bita da kallo kurun kan wani yae magana har Baba iro ya taso yae kanta ya hauta da duka baji ba gani seda tae lilis ga yunwa sannan Baba Azumi ta qwaceta ta kaita d'akin dayake mallakinsu itada ummul, dariya tae bayan ta wurgar da ita kan matacciyar katifarta tace

"Wahalalliya er iska, idan kina numfashi sekin bar gidannan wlhy" batace komai ba tayita kuka tana mayarda numfarfashi sama sama......Ummul ce ta kalleta ta girgiza kai tace

"Mesa baki mun wayaba Nanuwa? Dasena bi ta departments d'nku na d'akkoki ai tare da mahal muka dawo" bata kulataba ita d'inma bawai dad'inta takejiba sedai takan kwatanta mata adalci wasu lokutan. da qyar ta iya miqewa zuwa ban dakin dake cikin dakin nasu tae wanka da ruwan d'imi dayike akwai heater jonawa kurun tae ta watso ta fito tae sallan magrib da isha sannan tafita ta ebo abinci tazo tanaci tana hawaye....

**************

Washe gari tunda safe tana idar da sallan asuba taje gun Baba iro,har qasa ta duqa

"Baba ina kwana?" Kallon takaici ya mata

"Lapia lau Nanuwa, lapia dai?"

"Dama Baba kud'in handout ne da akace mu siya nace barin maka magana" murmushi yae yace

"Dad'in abin gadon ubanki kikrta cinyewa, nawane kud'in?" Sadda kanta tae qasa tace

"Zekai dubu da d'ari biyu ga kud'in xuwa makaranta kuma" zaro dubu biyu yae ya miqa mata......

"Ni Nanuwa duk karuwancin nan dakikeyi ace wai ko sisi bazaki iya ajiyewa kiyi laluran makarantar ki, Allah ya wadaran naka ya lalace an tsotsi mugun hali a nonon uwa" qwallane ya gangaro mata ta miqe tana me ganin jiri na ebarta, idan bata karb'i kud'i a hannun Baba iro da kanta ba,Baba Azumi bawai batan zatayi ba....idan kuma tazo karb'a a gunsa seya zageta tatas ta uwa ta uba tukunna yake bata kudin.....shirinta tae kaman yanda ta saba acikin doguwar rigar yadin hijabi kalar ja, wacce take had'e da hijabinta da d'ankwalinta tayi kyau daidai nata irin kyawun irinna jan buzu!!! Hartakai qofar Baba Azumi ta kirata,tasan kwanan zancen karb'e kud'in data karb'a zatayi ita kuwa bata had'a komai da karatunta ba, bazata tab'a bari a ruguza mata abinda take ganin shikad'aine abinda zatayi ta taimaki kanta ba,wannan ya sanya tayi biris da kiran ta qarawa kafanta gudu har tana hard'ewa ta ruga da gudu tabar gidan har layinsu ma da gudu tabarshi ta nemai adaidaita ya d'auketa kan naira d'ari da hamsin zuwa dandima (Bus stop).....

     Kai tsaye hall d'in dazatayi lecture ta wuce,ta tarar da qawarta Islam tana zaune tana bitar handout d'in ta,dafa tae tace

"En mata Dr. Tahir d'in ya makara ko yau ko?" Murmushi tae

"Bari kawai Nancy ai takaici ya ishen tun safe se'a rena maka wayau ka dako sakko ka fito kuma ka tafi empty ba karatun" zama tae kusa da ita

"Kaine a qasa ya zakayi? Bakada zab'in daya wuce ka hakura" tsaki islam taja me tsayi

"Idan kuma bakazo ba suka zo su karta rashin mutunci dan isa" murmushin ta qara yi

"Kiyi hakuri islam wataran se labari" tab'e bakinta tae tace

"Wai jiya se naseer ke gayan sun had'u dake kina tafiya da qafa zuwa gida, gaskia bakyawa kanki adalci Nancy, kina mace cikakkiya ma acikin matan! Ishasshiya meji da kanta da cikar zatin halitta da haiba fara kyakyawa Nancy  ga diri son kowa qin maqiyin Allah zaki zauna dari biyu kacal ta gagareki, koni islam da bankaiki kyauba nafi qarfin mallakar miliyan biyu yanzu haka, bareke kyakyawa ki riqa turbud'e fuska a niqab kina cutar kanki, wlhy Nancy kullum ina gaya miki kiyiwa kanki fad'a, ni abu mafi bani takaici ma befi yanda kike cewa wai bazaki kyautar kud'i naba na haram ne, ina zinar bajikinki nake kaiwa ba nawa ne kuma bake kikai ba, amma ace kina qawata kina tafiya da qafa, ko Naseer yace akan babur suke susu uku daya wuce dake" murmushi tae tace

"Islam koke fatana Allah ya shiryar dake babu wani kalar matsatsi na rayuwa dazan shiga na aikata zina ba, musamman irin wacce kukeyi, islam  kefa intnl karuwa shine sunan ki!!! Kina wofintar da darajarki ta 'ya mace kina wulaqanta suturar da Allah  yae miki kina kaiwa mazajen bariki jikinki, suna amfana da ni'imomin jikinki  suna halllakar dake, suna amfani da 'dan abinda Allah ya basu na dukiya suna dulmiyar dake suna rud'ar dake....yayinda 'ya'yayensu suna cen suna cikin gidajen a garqame auren daze gagareki anan gaba su na gata suke yiwa 'ya'ya yensu wanda dan gwamna se er gwamna!! Er councilor kuma se d'an kantoman qaramar hukuma d'an shugaban qasa kuma se er minister!!! Yayinda ke kuwa aure ze gagareki koda dame shayin layin kune sabida wanda suke b'atancin dake sune dai zasu koma su zageki, wlhy koda yaron abokanansu sukaji zasu aureki zasuce er bariki ce!!!! Er Bariki shine sunan dazaki samu daga bakunansu amaimakon Islam!!! Kiwa kanki fad'a qawata ki saisaita nustuwarki" tab'e baki Islam tae tace

"Bari kiji ko annabi dakanshi yace mu nemi tsari da talauci daga wurin mahaliccin bayi!! Kisani wlhy mahaifina dashi babu duk d'aya, mumu goma sha shida ya haifa 4 daga cikin mu sunyi aure duka matane agidan mu, sanin kanki ne yaranmu maza uku suma sune en auta, da qyar da sid'in goshi kake samun na break fast, ni yanzu Allah yamun hanyar kasuwanci bazan cuci kaina ba" girgiza kai Nancy tae kud'i masifane ta furta a sarari ta qara da cewa

"Karuwanci shine sana'a Islam?? Dan Allah ki dawo madaidaiciyar hanya kinji qawata, wlhy zina masifa ce, bafa cewa annabi yae karmui zinaba cewa yae damu mu nesanceta ma'ana karmu kusance ta, mezesa ki kira wannan da sana'a? " jingina tae da kujerar ta yatsine fuskarta alamun gajiyawa da  qosawa da zancen tace

"Nancy, banida wani zab'i daya wuce wannan idan na dena neman kud'i da jikina ke zaki ciyar damu nida mahaifiyata da en uwana? Ki sani wlhy Nancy ina sane sosai da haramcin aikata zina amma wlhy bazamu rayu da yunwa ba" lumshe idonta tae tana me qoqarin hanawa qwallan idanta zubowa

"Islam ki barwa haramcin nan dakike aikatawa suna tarihi dan Allah, ki ja jari da kudad'en dakika tara tare da addu'ar albarka ga abun sekiga kinci har kin baiwa maqota"

"Nancy mujewa wata sabga mutane sun soma taruwa" shiru tae sabida ba kowa kusa dasu ta sani sarai wlhy gujewa maganar islam keyi kurun sabida tayi nisa batajin kira,wannan ya sanya bata qara cewa komai ba ta tsuke bakinta gum!!!

  Bayan da suka kammala da morn lecture hostel suka wuce wuce,sabida suna lecture da yamma, acen  Suka qara buga sabuwar daba....

"Aa Ameena se kuma ina? an cab'a ado iya ado ana jiran isowar Alhaj Birwa Naira,tomu wai meye namu kason?" Harara ta wurgowa yusrah dake mata maganar

"Gardawan dasuke hawan ki idan sun hauki nawa kike bani idan sun biyaki?" Dafe kafada tae tace

"Allah sarki maida wuqar ni wasa nake wlhy" darewa tae itama

"Wainikam yusrah ya zancen Alhajin mamula ne? Yafa matsanta akan zancen sabon hannu, na gama zaga en level 1 d'in nan ina latsawa duk kanwar jace, yaran a lalacen su sukazo shi kuwa tear leather yakeso wacce ze b'anb'are da kansa ya yaga ledar yaci biredin ya wurgar" dariya suka kwashe dashi dukkansu,yusrah ta ce

"Ai baki sani ba, wlhy Alhajin mamula ban yarda dashiba, se kullum seyace se virgin kuma seya baki miliyan biyu kofi ifan kika had'ashi da virgin ita kuwa har miliyan goma seya iya bata, sekace abin tsafi,yo wata budurwar ai har sadakinta da lefe baze wuce dubu dari biyar ba" dariya suka qara bushewa da shi, yayinda Nanuwa ta girgiza kanta cikin qunan rai tana mamakin wannan halin ace aciki  Mata goma babu daya ta gari to meye matsalar?  Daga kuma ina abun ya samo tushe?" ......

Mom Nu'aiym

Continue Reading

You'll Also Like

117K 10.9K 29
သူကငါ့အပိုင်ဆိုတာ မင်းတို့လက်မခံချင်လည်းလက်ခံရမှာပဲ !
66.7K 5K 29
"ဘယ်က ဇယားလေးလဲ? Kim" "အကြွေးနဲ့ သိမ်းလာတာလေ မွေးစားဖို့" "ဘယ္က ဇယားေလးလဲ? Kim" "အေႂကြးနဲ႕ သိမ္းလာတာေလ ေမြးစားဖို႔"
66.9K 9.1K 35
Após a morte de seu pai Edward Teach, um dos maiores e mais respeitados piratas da região do Caribe, Mon assume como capitã do navio Concorde. Bem qu...
160K 12K 24
ကမ္ဘာပေါ်မှာ လူပေါင်း billion ချီပြီးရှိနေလည်း ကျွန်မအကြည့်တွေက ရှင့်တ​ယောက်အတွက်သာ။