🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
🌐 *ZÃN RAYU DA KAI*
Story_*oum zahra*
*Written$edit__pheeymarrh*
*MRS NOOUR*
Pheeymarrh@gmail.com
Wattpad me *@pheeymarrh*
بسم الله الرحمن الرحيم
2⃣7⃣➕2⃣8⃣
Ko kuwa shima yana kaunar ta tamkar yadda take kaunar shi har dashi yazo neman auren ta da kanshi cikin kankanin lokaci,,juyi ta sake yi ba tareda ta bude idanuwanta a hankali ta kira suna Aisha wacce ke zaune gefe ta zuba mata idanu cike da tausayawa irin halin da kawar tata take ciki,,
Wallahi friend koda wannan auren da wata manufa yayi ko kuwa ince miki daukar fansa toh tabbas ina bai tabbatar miki wallahi zan zauna zan yi hakuri zan jure duk wani damuwa da bacin rai da zan shiga,,
Domin banajin akwai abunda zai yi mun a duniya komai muninsa soyayyar da kaunar sa ta ragu cikin zuciya ta burina a duniya shine in rayu da shi in kuwa har ya aure ni wallahi zan rayu da shi har karshen rayuwa koda kuwa hakan yan nufin zai jefani a wani hali,,ganinsa yafi komai sanya rayuwa ta cikin farin ciki,,
""Zan rayu da kai,,""
"" zan rayu da kai ""
Zan rayu da kai""har karshen rayuwa ta ta karashe maganar cikin sanyi da fitar da wasu zafafan hawaye zuciyarta na zafi yadda ta kamo da ciwon sonsa yana chan tareda matarsa ba tareda yasan da hakan ba,,
Share hawayen Aisha tayi cike da tausayin kawar tata ta ruko hannuwanta duka tana kallonta bakinta ya Gaza furtawa Zahra komai,,
Bude idanuwan ta tayi wadanda suka chanza kala sukayi jajur saboda damuwa kallon Aishan tayi cikin ido a hankali ta soma fadin mai yasa baba zai ki amincewa be?
Meye aibu ko laifin shi,,?
Wallahi ina son shi haka,,zan aure shi koda kuwa hakan na nufin karshen tawa rayuwar……
Da sauri Aisha ta sanya hannu ta akan labban Zahra tana girgiza mata kai murya cike da tausayawa ta hadiye nata kukan ta soma fadin please ki daina fadin haka don Allah kina addua Zahra nima ina tayaki insha Allah adduar mu zata zamo karbabbiya saidai banason kina yiwa kanki mugun fata insha Allah zaku rayu da juna cikin farin ciki da kauna hade da soyayya mai ban mamaki har karshen rayuwarku,,nayi miki alkawari ninkawa fiyeda da akoyaushe zan tayaki rokon ubangiji ya cika miki burinki in har alhairi ne gareki domin bazan so idanuwanki su rufe akan soyayya ba Wanda vazai zamto alkhairi gareki ba,,
Komarda kanta tayi ta kwantar akan pillow hawayen har lokacin yana zubowa daga idanunta murmushi yake tayi tace bazaki gane bane Aisha shidin tabbas Alkhairi ne a koyaushe ina ji ajikina shidin alkhairi ne,,
Akoyaushe nayi tsayuwar dare akan rokon zabin ubangiji soyayyar sa mai karfi ke sake lullubemin dukkan magudanar jini da zuciyarta ,,
★★★★★★★★★
Tare suka tashi baccin safen daya koma suka nufi toilet tana makale dashi sukayi wanka tare suka fito shirin ma kusan tare sukayi shi don ita ta gyare masa gashin kansa yayinda shi kuma yayi mata shafa kananan kaya ya sanya riga da wando milk color marasa nauyi itama kwalliya tayi sosai cikin doguwar Riga gown light blue wacce ta kamata daga sama zuwa kugu ta nude anyi mata kwalliya sosai a jikinta tamkar wacce zata je party hula ta sanya a kanta wacce take tamkar set din kayan ta bazo gashin dokin ta zuwa bayanta sosai sun yi matukar kyau suka nufi bangaren Ammyn hannun su sagale dana juna cike da so da kauna,,
Tunda suka shiga ta kimtse fuskar take shan kanshi koda Afnan din ta gaidata a dan dakile ta amsa saida ta zauna kan kujera saanan ta gaida Ammy ba tareda wani girmamawa ba ita kuwa cike da kulawa da so ta amsa tamkar batajin zafin abunda tayi ba,,
Kwantar da kansa yayi gefen kafadar Ammyn yana fadin Ammyna antashi lafiya yana lumshe idanu a hankali,,
Saida ta sanya hannu ta shafo gefen fuskar sa tace lafiya lau son da fatan kun tashi lafiya,,gyada mata kai yayi kawai ba tareda ya amsa ba har lokacin fuskar sa dauke take da murmushi,,,
Ammy na mai kika dafa min ne am hungry,, ya fada yana daga kansa ya jinginar akan kujerar,,
Kuje daining yana chan an shirya muku,,,
OK ya mike yana kallon Nasreen din da kallon bazaki ciba,,
Saida ta kyabe baki kafin tace noo kasan ba komai nake iya ciba jeka kawai,,
Dage kafadar yayi ya wuce yana mamakin hali irin na Nasreen a koyaushe taya zakaso mutum amma yan uwansa kaki su akan wani shirme nata shidai akoyaushe yanajin sonta cikin zuciyarshi domin yadda take matukar kaunar sa amma wadannan halayen nata suma daga masa hankali da sanyashi damuwa ji yadda ta koma tamkar ba itace Nasreen din da suka fito tare ba,,a haka ya karasa ya hada coffee da kansa ya bude foood flask din ya zuba Irish da miyar kwai da allayahu kadan ya fara ci a hankali tamkar Wanda akayiwa dole,,
Yayinda Nasreen ta dauki wayata ta soma latsa wa ta dage kafafunta ta dora saman center table din dake parlon,,
Uwar hararar Afnan din ta doka mata tana dage hanci sama,,
Kallon Ammyn tayi mata mai cike da gargadi akan abunda tayin, Wanda Nasreen din ma batasan tanayi ba saboda dukar da kanta datayi ga waya don inba gaisuwa ba dawuya kiga tana hira da Ammyn ko Afnan wacce take ganin tamkar yin hakan raini ne zata janyo ma kanta,,
Mikewa Afnan din tayi tana tunzuro baki gaba sai dai komai ta tuna sai kuma ta saki lallausan murmushi ta wuce cikin sauri tana dariya,,
Nasreen Ammyn ta kira sunan ta,,
Dagowa tayi tana fadin yes Ammy tana kallon cikin idanun Ammyn Wanda sai ita ce taji nauyin hakan ta kauda nata idanun ta mike tana fadin ki sameni a bedroom dina,,
Okay ta fada tana cigaba da duba wayarta,,
Saida ta karasa karanta abunda takeyi kafin ta mike tabi bayan Ammyn,,
Koda ya gama tsintar zuciyar sa tyayi da son ganin ta wayar sa ya dauko daga aljihun wandon sa ya kunna hotonsu da Nasreen ne ya bayyana suna rungume da juna na biki sunyi matukar kyau murmushi yayi har cikin ransa yana kaunar hoton nan saboda shigar hausawa datayi atampa ce a jikinta harda mayafi Wanda kusan inba Karyane zaiyi ba saiyace bai sake ganinta da kaya irin haka ba,,
Inda ya boye hotunan ta ya Shiga ya bude gasunan kala kala na Zahran wadanda aka sauke su ranar,,
Kurawa idanun ta zuwa fuskarta ido yayi ya rasa mai yasa yake jin zuciyar shi nayi masa zafi inya kalli hutunan ta sai dai hawayen dake kwance cikin idanunta sunan sanya shi Shiga rudu da tunanin akan ko tanada wata damuwa ne,,
Baisan ya dauki tsahon lokaci da shagala akan kallon idanun ta ba saida ya tsinkayi muryar Afnan din a dai dai kunnen sa tana fadin wallahi bro jaid itace nasake gani jiya tana baka abinci a baki taliyar da bakaso ita ka cinye tass kana kallonta ba tareda ka sani ba kuna kallon juna cikeda so da kauna,,
Dagowa yayi cikin hanzari yayainda ita kuma ta juya da gudu ta hadu sama tana dariya lumshe idanu yayi cikeda kunya mai yasa ma ya tsaya bata lokacin shi akan wannan yarinyar da lokaci daya ya kusa maida ta abun tausayi tsaki yayi yana jin haushin kanshi ya kashe wayar ya mike zuwa sama don kar Afnan din ta jika mai aiki kadan daga aikin ta ta fadi maganar nan a gaban Nasreen din,,
Sosai Ammyn tayi mata nasiha cikin Hikima yadda zata lura ta dage da kuma hakuri akan mijinta da maganar airen Bayan sin Shiga dakin,,
Allah yasa tanaji bata maida wani Abu ba saidia zucoyarta tafasa takeyi akan ganin kamar an raina mata hankali ne hadin baki ne kawai,,
Nayi magana da son yace min ya sanar miki komai kafin yayiwa zanchen auren nashi,,
Murmushi tayi Wanda iyakacin sa labbanta a dage ta ce Ammyn kenan yo meye amfanin sanar min din Bayan kun gama tsara yaddda zakuyi din tun kafin zuwan……
Shigowar Afnan din ce ta katse mata maganar da tayi niyyar yaba ma Ammyn inda Afnan fin ta soma ba Ammyn labari abunda ya faru ba tareda tasan ni ko tunanin Nasreen din na dakin ba,,
Duk yadda Ammyn ke kiyimata nuni da idanu akan yin shirun ina saida ta dire aya tana fadin Ammyn kinga yadda yake kallon hotunan ta kuwa wallahi na Dade a Bayan sa baisan in……
Mugun kallon dataga yana jefo mata ne ya sanyata yin tsit da bakinta ta juta tana kallon inda yake kallon dukda tsiwar ta saida kirjinta ya buga ganin yanayin Nasreen din ,,,kasa tayi da kanta cike da nadamar abunda tayin Wanda magana zarar bunu babu damar mayarwa,,
Takowa yashiga yi zuwa gurinta ya zauna da sauri ta mike tana daga masa hannu kallon Ammyn tayi cikin bacin rai tace yanzu kin sami amsar tambayar dakikayi bakusan da magana ba tun zuwanmu kasar nan yarinyar nan ki wulakantani dayimin rashin kunya a duk lokacin dan shigo,,
Jinjina kai tayi tana fadin ni dama nasan haka zata faru yadda kuka matsa mutaho din dama akwai abunda kuka shirya,,
Keeeh Nasreen "" Amjad din ya daka mata tsawa tana mikewa tsayi wacce saida ta razana su dukkansu,,
Da sauri Ammyn tayi kokarin osar masa da sako ta hanyar idanu da girgiza masa kai,,
Kauda kai yayi cikin fushi mai yasa Ammy ke danne shi ne a duk lokacin dayayi niyyar daukan mataki akan Nasreen din,,
Malalacin murmushi tayi tana tabe baki cikin tsiwa take fadin da kayi duk abunda zakayi pjaid lokacin Kane amma kasani in kai zata sanyaka dole wallahi bandani na taso cikin rayuwar yanci haka kaima mai zai sanya mu zauna cikin karkashin ikon wani ba haka kake ba Sam pjaid muna chan sai munzo kasar nan akoyaushe kake min haka amma wallahi zan duki mataki akan hakan ta dauki wayar ta kan gadon ta fice ta bugo musu kofar,,
Sun Dade shiru dukkansu yayinda shi kuma ya rintse idanu cikin tsananin fushi zuciyar sa na yi masa suya Ammyn sa Nasreen keyiwa haka anya idan mai dauiki mummunan mataki akan Nasreen ba zaisamu farin ciki kuwa baisan Ammyn ta karaso inda yake ba saida yaji ta dafa kafadar sa ,,,kin kallon ta yayi har ta soma magana bai bude idanun Shiba,,
Kayi hakuri dole sai kayi hakuri akan duk wata matsala dazaka fuskanta gurinta dole kayi mata uzuri saboda kishiya zaayi mata ni mace ce nasan zafin hakan koda yake ni baayi min ba,,
Tashi kaje ka lallashe ta don anyi mata laifi inma fushin ne da wannan parrot din ya kamata kayi tana zuba wa Afnan hararar wacce ta sanyata mikewa da sauri ta bar dakin,,,
Da kyar ta samu ta kwantar masa da hankali tareda umartan sa da baiwa Nasreen din hakuri,,
Jinjina mata kai kawai yayi ya mike ya fice a dakin har lokacin zucoyar shi na bace,,
★★★★★★★★★★★
Maman su Aisha suka samu inda aishan ta bada shawarar hakan tunda aminiyar tace sukayi mata bayani aishan ta roketa akan taje ta baiwa Mama hakuri don Zahra batasan da maganar zuwa neman auren taba,,
Ita ma ta tausayawa Zahra tace yanzu kuwa zata shiga kafin su koma ai wanna ba tsari bane nasiha tayi musu sosai akan rayuwa dukkansu saida suka zubar da hawaye musamman zahra da dama kiris take jira,,
Suma gidan Bayan tayi sallar azahar ta shirya take gurin mama sai lokacin hankalin Zahra yadan kwanta tasan mama zata sauko daga fushin datakeyi indai hajiya taje,,
Bata wani jima ba tazo Ind tace suje maza su taya Maman aikin dare,,
Babu laifin mama ta sake mata fuskar dukda ba kamar daba amma ta danji sanyi a ranta tare suka wuni da aishan saida ta taya Zahra aiki suka gama girki dare suka sake gyara gidn,,
Sai gab da magrib suka gama inda zahra ta zuba mata tuwon miyar kubewar danya dasukayi a kula ta rakota,,
Fiowar ta tayi dai dai sa daowar Baban suka gaidashi suka wuce,,
Bata Dade ba ta yiwa aishan sallma ta wuce gida sai dai tun fitowar ta ta hango yayan mahaifin nata kawo tareda babanta Wanda ta rasa dalilin daya sanya ta mummunar faduwar gaba ,,,
*Mrs Noour ce*🥰
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻