chapter 35

374 44 0
By Seemahwrites

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

      🌹HAR ABADA🌹
          (bazamu rabeba)

       LOVE & FRIENDSHIP

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

  
Vote me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         RUBUTAWA

        UMMU NAJMA
   
DEDICATED TO
MAMAN MAMY SHALELE AND BEELAT SARAUNIYA

Kaman an rubuta min sunanki*✍🏼
A cikin zuciya taaa*💝
Kece saraunya ta yarinya*👸🏽
And I have to let you know oh*👩🏼‍🎤
Fatima...fatyma..fatima fatyma............🤩💓

Honeymoon pages naki ne ke kadai fatymarh isma'il Aka amaryan ahmadulle🤭 idan kinga dama kada ki san musu ko kadan😅

35🍎

A tare suka juyo idanun su ya sauqa Akan fiskan Ayrah dake ta faman zabga murmushi, kallo Feenah take qare Mata tun daga sama har qasa, doguwa ce kuma kyakkyawar baturiya gata da grey eyes gashin kanta Mai haske sosai Wanda ake Kira da blonde hair, tana sanye da gypsy top da mini flowy skirt.

Tabe baki Feenah tayi cikin ranta tace 'mun baro jaraba a 9ja gashi munzo mun hadu da Wanda yafi wancan, Allah ya tsari wata shegiya damun wargi taga Yanda zanci qaniyar ta no mercy' a fili tayi qwafa.

Sai a lokacin Ayrah ta lura da ita, fuska a sake ta miqo ma Feenah hannu sukayi shaking
"I'm Ayrah Felix from L.A what about you?"

Bata jira amsan Feenah ba ta juya wurin Ahmad take
" It's great to have you here Sir, who is she? Is she a relative?"

" She is my wife, her name is Feenah"

A take fara'an Amrah ya bace batt, ta qaqalo murmushin yaqe tace
"Nice to meet you Mrs L" ta maida duban ta wurin Ahmad tace
" sir, shall we leave? The convoy is waiting"

" Ok" yace ya ja hannun Feenah suka tafi.

Suna Isa gidan suka samu komai a gyare an canza abubuwa da yawa, ba qaramin kyau gyaran da yayi ma Ahmad ba, ya kalli Ayrah hade da sake Mata murmushi yace
"Good job Miss Felix, the place looks good I like it"

Har cikin ranta taji dadin yabon ta da Ahmad yayi, gashi har da kyautan murmushin shi Mai tsada.

Feenah Kam ta sake Baki ne tana kallon tsaruwa na wannan tamfatsetsen gida yayi girman duplex dinsu na 9ja guda 3 wajen tsaruwa kuwa ba'a magana don duk wani Kayan qyale_qyale na bature an saka shi, kusan 30% na gidan tinted glass ne.

Maganar Ayrah ce ya dawo da Feenah daga duniyar lissafin da ta tafi, tana tambayar izinin Ahmad da ya barta ta zauna tare dasu don Daman ita ba Yar garin bane aiki ne yake kawo ta Chicago Amman mahaifin ta na Los Angeles mahaifiyar ta kuma ta rasu tun tana shekaru 14.

Ahmad Bai nuna damuwa ba ya Bata izinin zama tare dasu Daman dalilin da yasa yake Hana ta zama babu mace ne cikin gidan.

Kallon shi Feenah take yi da mamakin qarfin Hali irin na Mr arrogant, Bai tambayi izinin ta ba a matsayin ta na matar gida dai bar wannan ta zauna tare dasu? Zanyi maganin ka ne, ta fada cikin ranta.

Dakunan su suka shiga suka yi wanka suka huta, Basu suka fito ba sai dare, sallah ma a daki Ahmad yayi domin masallaci nada nisa daga gidan Kuma Nan ba Nigeria bane ballantana kowa ya samu ikon gina nashi masallacin.

Tunda suka fara dinner ta lura hankalin Ahmad gabaki daya na Kan Ayrah, ita Kuma ta sake sai zuba surutu take yi, gaba Daya Feenah jinta take yi uncomfortable, lokaci Daya kewar Nigeria ya shige ta don tun da suka baro gida Ahmad ya daina Mata dogon magana ballantana ya kula shirmen ta.

Yana cikin cin abinci ya shaqe da yaji ya fara tari, da sauri Ayrah da dauki ruwa ta nufe shi tana shrin bashi Feenah ta buge glass cup din ya Fadi qasa ya tawarwatse, ta dauki nata glass din ta bashi yasha tana patting dinshi a baya har ta samu ya dawo normal kafin ta koma ta zauna taci gaba da cin abincin ta.

Tana gamawa ta miqe ta tattara dining din ta wuce dakin ta tayi Shirin bacci sannan ta tafi dakin shi tayi kwanciyar ta ba tare da ta jira shi ba Dan ta lura Yana enjoying hira da Ayrah dukda yawanci maganar su Akan aiki ne.

Washe gari da sassafe suka yi shirin office, bayan sun Gama breakfast tai musu rakiya har qofa tana gani Ayrah ta shiga bayan motan da yake ciki suka tafi.

Komawa ciki tayi tanajin wani Sabon kadaici ta taso a cikin babban gida Mai cike da jama'a Amman gashi yau ita kadai a gida sai Kuma masu aikin da duk cikin su babu Mai ikon Mata magana ballantana ta samu Mai debe Mata kewa, daukan wayan ta tayi ta dinga Kiran Yan gida a haka har bacci ya dauke ta a parlon.

**********

"Friend gaskiya bakayi ma yarinyan Nan adalci ba, a Kan idon ta fa aka Kai muku honeymoon tickets Amman ka dauke ta ka tafi aiki da ita?"

Gyara zama yayi akan seat dinshi Yana kallon screen din system dinshi da suke video call da Imran yace

"Kafi kowa sanin bani da lokacin batawa, contract dinnan 4 months kawai ya rage Mana and akwai abubuwan da ba'ayi ba da yawa, zamu dauki kusan 6 months bamu Gama ba idan muka yi wasa Kuma kasan hakan zai jawo Mana asara Mai yawa, we will lose millions of dollars friend, babu Kai anan babu ni babu dad Sannan wancan mahaukaciyar yarinyan Amrah da na turo ta babu abin da tayi, gaba Daya aikin yayi ma Ayrah yawa har ramewa tayi Kuma kasan ba responsibilityn ta bane kula da komai da komai "

" Gaskiya ne, Amman ita Feenah meye laifin ta a ciki da har abin dai shafe ta? Ita matar kace tana da rights a Kan ka Wanda babu wani Abu da ya Isa ya tauye su, abun Nan sau Daya akeyi a rayuwa idan kuka je yanzu HAR ABADA ba zaku sake komawa ba, duk dadewa ba zaku fi one month ba Kun dawo, inyaso sai ka koma Kan aikin ka ba shikkenan ba?"

Dariya Ahmad yayi yace
" Imran kenan, idan mun tafi kamar Yanda ka fada Mai zaku honeymo?
Ko ka manta deal din dake tsakanin mu ne? Zuwa ma Bata kudi ne da lokaci"

" To shikkenan tunda haka kace, Daman Ina so na fada maka an bani izini gobe na tura gidan su Aisha, Nima na kusa zama ango Amman ba irin ka ba"

Dariya Ahmad ya sake yi yace
" Nidin daban daban ne ba irin sauran ba?"

" Kwarai kuwa, Kai sunan ka muna ango ne, ni Kuma angon gaskiya nake so na zamo, very loving and caring husband"

" Hmm to shikkenan ango Mai jiran gado, sai anjima aiki nake yi".

Bai jira cewar Imran ba yayi disconnecting call din sannan ya ci gaba da aikin gaban shi.

**********
Farkawa tayi daga barci ta duba agogon dake daure a hannun ta taga 2:00pm zaro Ido tayi hade da salati ganin har lokacin sallah ya wuce Kuma anytime Ahmad zai iya dawowa gashi Bata yi abinci ba.

Cikin hanzari ta shiga dakin ta tayi wanka tayi sallah sannan ta shiga kitchen suka hada abinci Mai sauqi, Amman har bayan sallan la'asar babu Ahmad babu labarin shi gashi yunwa take ji saidai tana tsoron taci abinci ba tare da su ba ya disga ta a gaban wannan baturiyan.

Qarfe 6:00 suka shigo gidan gaba Daya a gajiye yake har idanun shi sun fada, ta qarasa wurin shi ta Masa sannu da dawowa sannan ta karbi briefcase dinshi tayi hanyar dakin shi Yana biye da ita a baya Ayrah ma tayi nata dakin.

Suna shiga ya zuba a arm chair hade furta "washh" Yana matsa qafafunsa sa yanda suke Masa zogi saboda zama.

Tana ganin haka ta ajiye jakar sannan ta qaraso ta cire Masa rigan suit dinshi ta warware Masa necktie kafin ta zuguna ta cire takalmin da socks din dake qafan shi tana matsa Masa qafan a hankali.

Rude Ido yayi Yana Jin dadin tausan da take Masa don jikin shi ba qaramin ciwo yake Masa ba, Saida ta tabbatar ta yabar Jin ciwon qafan kafin tace
"Yaya Ahmad"

"Uhmm"

"Please inaso na roqe ka wani Abu ne"

Still idon shi a rufe yace
"Ki fada inajin ki"

"Dan Allah ka daina zama da Ayrah cikin mota daya, nasan na maka shishshigi Amman hakan da kuke yi Bai dace ba tunda Kuna fita da motoci da yawa kusan guda 7 ta nemi wani daga ciki ta shiga ba sai naka ba"

Bude idanun shi yayi ya ware su Akan ta Daman already shi take kallo, lokaci Daya idanuwan suka sarqafe cikin na juna kowa da abin da take saqawa cikin ranshi.

A hankali Ahmad ya matso da fuskan shi kusa da nata sannan yace
"Are you jealous?"

Yamutsa fuska tayi tace
" Nooo, Akan me zanyi wani kishi, kawai dai Naga ita Ayrah arniya ne ba lallai bane ta Gane illan hakan Amman Kai musulmi ne kasan cewa Bai halarta baligai mace da namiji su zauna wuri daya ba saidai idan sun kasance Muharraman juna, Kuma kaga ni Yar uwar ka musulma ce Yana da kyau idan Naga kayi ba dai_dai ba na maka gyara"

Murmushi Mai sauti Ahmad yayi yace
" Toh hafeeza wifey, naji Kuma zan gyara, thanks for the massage"

Itama murmushi ta maida Masa tace
" my pleasure"

Yauma kamar jiya tunda suka ci abinci ya bude babin Hira tare da Ayrah suna yi suna taba aiki akan takardun da suka dawo dasu, Haka ta zauna ta jira shi har suka gama kusan qarfe 12:30 kafin suka shiga sukayi barci, don jiya ma da tayi jarumtan kwana it kadai Saida tayi ta tsorata Kuma Bata iya barci ba har Saida ya Gama abin da yake yi ya shigo.

Washe gari da safe
Bayan sun Gama breakfast ta musu rakiya zasu tafi, Ayrah ta bude motar shi zata shiga da sauri ya dakatar da ita, yace Mata tayi haquri matar gidan tace Bata so.

Ranta Baiso ba ta nufi motar dake bayan nashi, tazo shiga ta daga Ido ta kalli Feenah da har yanzu take tsaye a bakin qofa tana kallon su, tana jin wani zafi a cikin zuciyan ta, tun da take aiki tare da Ahmad kusan shekaru 7 kenan yanzu Bata taba ganin ya dauki maganar wata mace da daraja ba bayan mom da Sahar, yanzu kam tasan Feenah ta Mata nisa kullum Bata da wani burin da ya wuce ta samu matsayi Mai girma a zuciyar Ahmad Amman Feenah ta riga da ta dauki wannan matsayin.

Ganin kallon qurillan da Ayran take Mata yasa tashi murmushi ta daga hannun ta tana waving din ta bye_bye, qaqalo murmushi Ayrah tayi ta mayar Mata sannan ta shiga cikin motan, sai da Feenah taga fitan su kafin ta koma ciki.

Saida suka shafe kusan wata guda a Chicago Amman babu abin da ya canza, idan Ahmad ya fita tun safe bayi dawowa sai kusan magrib, gaba Daya kadaici ya ishi Feenah idan ta tashi tayi ayyukan da ta saba ta taya chef hada abinci ta rakasu mota shikkenan haka zata dawo ta zauna bata komai Bayan aikin tunani.

Cikin dan zaman da sukayi wani mummunan sabo ya shiga tsakanin ta da shi dukda wani abun suna yi ne don ganin idon Ayrah Amman Yana iya qoqarin shi wajen ganin ya kula da buqatun ta, don Yana Jin dadin Yanda take Masa biyayya Bata da wani matsala.

**********

"Mom Dan Allah Mai yasa Baki son na auri Yaya Saleem? Ko ya Miki wani abun ne?"

" Babu abin da yamun Amman ban lamunci wannan relationship da kuke shirin qullawa ba,
Haba Sahar duk cikin maneman ki 'ya'yan manya kuma 'ya'yan masu kudi kin kasa fidda guda daya sai wani Saleem da bayi da wani Abu Mai girma da ya riqe Wanda zai iya daukan dawainiyan ki dashi?

Son ya auri qanwar shi ke Kuma kince kina son shi, Wai me suke dashi ne da har suke tsole muku Ido hankalin ku yake karkata wurin su? Na Bari son ya auri Nafeesah ne saboda shine mijin Amman a kanki bazan lamunta ba ki canza shawara"

Cike da bacin Rai dad da idanun shi suka kada suka yi jawur yace
"Kin bani mamaki Huda, ban taba zaton akwai ranar da dai zo ki nuna rashin qaunar ki Akan abun da nake so ba bare har ki furta da bakin ki, abun ma Mai matuqar muhimmanci ga rayuwa ta,

Huda kinfi kowa sanin waye ni Kuma kinfi kowa sanin muhimmancin Yusuf da iyalin shi cikin rayuwa ta, ba don haduwa ta da Yusuf ba da Bani raye, ko Ina rayen ma da Baki sanni ba, da yanzu bani da dukiyan da zanyi amfani dashi na dauko ki daga qasar ku na kawo ki Nan har ki aifi yaran da kike ma 'ya'yan Yusuf Gori a kansu, da yanzu Ina yawo a titi Ina roqo babu wadatatchen ilimi ko kuma Ina cikin halin shaye_shaye Wanda babu Wanda zai Soni kusa dashi, Dan zamo abun Zaki da hantara wurin Yan uwa na, Dan zamo abin wulaqanta a Kuma na zamo abin kwatan ce wurin aikin Abu marar kyau.

Huda har kin manta wa'innan wahalhalun da na tsallake su a sanadin Yusuf, Huda Baki yi ma kanki adalci ba da Kika zamo Mai saurin manta alkhairi, Yusuf shine jinin dake yawo a jikin na Kuma Ina alfahari dashi da iyalan shi, insha Allahu indai Ina raye sai Asma'a ta auri Saleem"

Cikin kuka Sahar tace
" Aa dad, wallahi na haqura na amince zan auri irin mijin da mom take so matuqar hakan zai sata farin ciki, bazan so na zamo silar bacin ranta ba" tana Gama fadan Haka tayi saurin shigewa bedroom dinta ta rufe ta fada Kan gado tana kuka Mai gunji.

Saida aka Kira sallan Isha kafin ta tashi tayi sallah tayi Shirin barci, tana gani Saleem na Kiran ta a waya Amman taqi picking, qarshe ma kashe wayan tayi gaba days ta cigaba da kuka.

9:30pm taji ana knocking qofa, tashi tayi ta bude tasan bazai wuce mom ko dad ba, kallon fiskar ta mom tayi Yanda yayi fayau gabaki daya tayi jaa kaman an watsa Mata yaji, ta karbi tray din hannun mom Wanda ke dauke da dinnern ta, tayi Mata godiya sannan ta ajiye shi a table ta koma gado ta ci gaba da zaman ta.

Zama kusa da ita mom tayi ta kwantar da kanta a jikin ta sannan ta Kira sunan ta a hankali,
"Sahar Ina so ki fadamun dalilin da yasa kike son Saleem"

Sauqe numfashi tayi tace
" Saboda Yana Sona da gaske Kuma tsakani da Allah"

" Mama na Mai yasa bazaki je gidan da Zaki huta ba gidan daula ko kuma gidan sarauta? Mai yasa kike son zaban wahala ma kanki?"

Murmushi Mai ciwo tayi Dan kwata kwata mom ta kasa fahimtan abin da take hangowa Nan gaba
"Mom ni kadai in da arziqin da zan iya jiqa Yaya Saleem shaqaf da Kuma iyayen shi, Amman farin ciki ba a cikin dukiya take ba, I just want to be happy.

Mom yawancin wa'inda suke zuwa neman aure na badan Allah suke zuwa ba they are after our wealth, sunsan idan har suka aure ni kulawa da ragamar dukiya ta zai dawo hannun su, Amman Yaya Saleem kudi na kwata kwata bayi gaban shi, Bai damu da abun hanu na ba, Kuma Yana iya qoqarin shi don ganin ya kula Dani Kuma ya saka ni farin ciki, me zan buqata bayan wannan?"

Shafa gashin kanta mom tayi tace
" Shikkenan mama na, na amince ki auri Saleem in har hakan ne zai saka ki farin ciki, Baki taba Mana musu ba Dan haka Nima bazan tauye Miki haqqin ki ba, Allah ya Miki albarka ya baku zaman lafiya..........🧚

#vote
#share
#comment.

Continue Reading

You'll Also Like

8.7K 226 13
Labarin soyayyar Aaliyah Badamasi Bulama da Sa'eed Aliyu Modibbo a shekarun 80's...
39.9K 5.3K 56
ASSALAM ALAIKUM! NAGODE SOSAI DA KUKA DUBA WANNAN LABARI FATAN ZAKU ILMANTU .WANNAN SHINE LITTAFI NA NA 4. LABARIN NAN MAI SUNA "KWARKWARAR SARKI MAT...
39K 1.7K 32
DR UMAIMAH USMAN BULAMA,Mace yar kimanin shekara ishirin da tara , Babbar surgeon A asibitin CITY TEACHING HOSPITAL , Aure Uku, ƴaƴanta uku . Mace m...
114K 10.5K 26
Hello there, I'm Afrar Massoud and I am the only daughter of a billionaire. Afrar is one of Africa's best designers, she is also half Arab and extrem...