TASNEEM 1 in TASNEEM Seriesโœ…

By ameeiyrah87

23.1K 3K 569

"Wallahi Amina in dai har Tasneem ta auri Maheer to a bakin auren ki"๐Ÿ˜“ "So nake yi ka auri Ameerah" ๐Ÿ˜ณ "Kafi... More

1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50 Appreciation And Thanksgiving
Apology and Announcement

36

341 50 20
By ameeiyrah87

Daga bayi na fito bayan na idar da wanka na 'daura alwala, sallar isha'i nayi sannan na karanta qur'ani, bayan na gama na duba waya ta na ga Jabeer yayi mun message cewa nan da minti 30 ze zo, doguwar rigar atamfa na 'dauko na sa, atamfan milk colour ne tana da flowers brown a jikin ta, hijabi brown na 'dakko na aje akan gado, under wears 'dina na saka sannan na sa doguwar rigar, turare na fesa ka'dan saboda bana so aji shi, powder ka'dai da kwalli da lipstick na shafa a fuska na, 'dan kunne da agogo na saka, sannan na chaje gashi na na sa ribbon na 'daura dankwali na, Ina cikin shiri na Noorie ta shigo 'dakin tana cewa

"Mami! Mami! jo ci ga shofia tayi shabon qawa (Mami! Mami! Zo ki ga Sofia tayi sabuwar qawa)"

Hannu na ta fara ja alamun inzo muje, cewa nayi da ita

"Tsaya tsaya Bibinuyi, shiryawa nake yi"

Cigaba tayi da ja na, da na ga ta matsu se na tsayar da ita na duqa na 'dafa ta nace

"Sofia The First ce tayi sabuwar qawa?"

Gya'da mun kai tayi, hannun ta ta sa a baki ta fara sha, cire mata hannun nayi a baki nace

"Stop it, ba na hana shan hannu ba? "

"Eh" tace

Sannan ta aje hannun nata, qara gyarawa nayi sannan na 'dauki waya ta da hijabi na, takalmi na sa sannan nace mata mu je in gani, muna kaiwa bakin qofa ta saki hannu na ta ruga da gudu ta barni a tsaye, girgiza kai nayi sannan na koma cikin 'daki na, qara gyarawa nayi sannan na sake fitowa, muryar Noorie naji tana cewa

"Ni bana washa da Ayaan juka na yakeyi (ni bana wasa da Ayaan duka na yakeyi), amma ti Ayiyan baya juka na tine aboci na (Amma shi Aryan baya duka na shine aboki na)"

Abba kuma yana ce mata

"To meyasa kike tsokanan Ayaan 'din?"

Cewa ta qara yi

"Wai jan nace miti baybeya iyin yadda Mami tate te mai (wai dan nace mishi barbela irin yadda Mami take ce mai)"

Dariya Umma da Abba suka kwashe da shi gaba 'daya, nima da murmushi na nazo nace

"Baby Noorie Sarkin Surutu"

Umma ce tace

"Jabeer 'din yazo ne?"

"Eh yazo" nace mata

Sannan Abba yace

"Ki gaida shi toh"

Cewa nayi

"Toh Abba ze ji Inn Sha Allah "

Noorie ce tace

"Mami ina da ti (Mami ina zaki)"

Cewa nayi

"Zanje waje ne Bibinuyi zaki je ne"

Girgiza kai tayi alamar A'a, se na ce mata

"Zo muje yanzu zaki dawo"

"To" tace sannan ta saki hannun Abba ta zo ta riqe mun hannu na, ce ma Umma nayi

"Umma Ina Ameerah?"

"Tana 'daki yanzu zanje in duba ta ma gara da kika tuna mun"

Fita nayi na samu Jabeer a mota, gaisawa muka yi sannan nayi mai iso cikin qaramin parlor, yana zama yace ma Noorie tazo wurin shi, hannun ta a baki taje ta same shi, cewa nayi

"Noorie remove that finger from your mouth"

Cire hannun tayi a baki sannan Jabeer yace mata

"What's your name?  Ya sunan ki?"

Cewa tayi

"My yem ishh Hashsha Ajeel Bibinuyi"

Kallo na yayi yace

"Me tace?"

Dariya nayi na ce mai

"Cewa tayi My Name is Hafsah Adeel Baby Noorie "

Shima dariyar yayi yace

"Ai nasan Bibinuyi 'din tinda naji haka kike kiranta, ashe shima sunan ainihin nata haka take kiran shi"

Dariya nayi nace

"Ina ruwan Noorie, sunan ya bita fa yanzu Bibinuyi, nima na kasa daina kiranta da sunan"

Murmushi yayi yace

"Ina ruwan yara"

Ku'di ya ciro ya miqa mata, se ta amsa tana ta kallon ku'din, ce mata nayi

"Bibinuyi what do we say?"

Se tace

"Chenchu (thank you)"

Murmushi yayi mata yace

"You are welcome "

Ce mishi nayi bari in rakata babban parlor in dawo, hannun ta na ja na kai ta babban parlor, muna isa ta shige ciki ni kuma na dawo wurin Jabeer, gaisawa mukayi sannan na tambaye shi ya su Mama da Jiddarh, cewa yayi duk suna nan lafia, nan dai mukayi ta hirar mu, bayan mun 'dan da'de mukayi sallama na raka shi sannan na shigo gida.

Ina shiga gida na samu Ameerah a parlor tana zaune Noorie tana kwance a kan cinyar ta tayi bacci, murmushi nayi mata sannan na zauna kusa da ita, cewa nayi

"Sannu da zama"

Ita kuma tace mun

"Yauwa sannu"

Bayan kamar minti goma se ga Umma ta fito , nan dai muka yi ta kallo sannan na ce mata zanje in kwanta, sallama nayi masu sannan na 'dauki Noorie muka tafi, kaya na chanja ma Noorie sannan na kwantar da ita na lullube ta, bayan na sa kayan bacci na kwanta a gado se waya ta ta fara ringing, number 'dinda ban sani ba na gani, kamar bazan 'dauka se kuma na dauka , muryar Maheer ta daki kunne na , cewa yayi

"Assalamu Alaikum "

"Waalaikummusalam"

"Tasneem kina lafia "

"Lafia lau Ina wuni"

"Lafia lau Alhamdulillah, ya gida, ya su Umma"

"Lafia lau"

"Kin gane wa ke magana ?"

"Aa ban gane ba"

"Maheer ne "

"Ok ya ka ke"

"Lafia lau"

"Kinyi mamakin kira na ko?"

"Gaskia kam Allah dai yasa lafia"

"Lafia lau, na kira ne mu gaisa"

"Okay Nagode "

"Dan Allah Akwai maganar da zanyi da ke in bazaki damu ba Tasneem"

"Tohm Ina jin ka "

"Dan Allah in bazaki damu ba in kika samu lokaci akwai maganar da zamuyi"

"Ina jin ka, zaka iya maganar ka yanzu"

"Aa in da hali ina so mu ha'du a gidan Fadeelah dan nasan Abba ba ze bari in zo wurin ki ba"

"Hmm gaskia bana tunanin zan iya maka wannan alfarmar"

"Ki taimaka dan Allah Tasneem"

"Zan duba in gani, in zan iya zan fa'da maka"

"Nagode Allah ya saka da alheri "

"Babu komai"

"Toh se da safe"

"Allah ya bamu alheri"

"Take care of yourself "

Ban amsa mishi ba se na kashe wayar, mamakin yadda Maheer ya kira ni nake yi, saqe saqe nake ta yi har bacci ya 'dauke ni.

#Team Maheer

#Team Jabeer

#Team MaNeem

#Team TasBeer

Ni dai Ina Team........

Tell Me Yours😁

Dedicated To Chuchujay

Continue Reading

You'll Also Like

1.9K 92 23
Once, a young girl wandered the desolate streets, her eyes sunken from the weight of her own misery. Orphaned, with her three year old sister, No fam...
5.4K 253 6
Yadda ya daga kai yana kallonta ne yasa ta shiga taitayinta babu shiri. Ya fara dumfararta gadan-gadan, kamar wanda yake shirin cinyeta danyarta. Duk...
3.8K 288 29
The story is a long journey of twisted fate, humiliation, sacrifice, betrayal, victory, Epilogize...INFERTILITY gajeriyar kalma ce me ฦ™unshe da ma'an...
19.5K 689 14
โ๐˜ฏ๐˜ฐ ๐˜ฎ๐˜ข๐˜ต๐˜ต๐˜ฆ๐˜ณ ๐˜ธ๐˜ฉ๐˜ข๐˜ต ๐˜ฉ๐˜ข๐˜ฑ๐˜ฑ๐˜ฆ๐˜ฏ๐˜ด, ๐˜ช ๐˜ธ๐˜ช๐˜ญ๐˜ญ ๐˜ข๐˜ญ๐˜ธ๐˜ข๐˜บ๐˜ด ๐˜ฃ๐˜ฆ ๐˜จ๐˜ญ๐˜ข๐˜ฅ ๐˜ต๐˜ฐ ๐˜ฌ๐˜ฏ๐˜ฐ๐˜ธ ๐˜ต๐˜ฉ๐˜ข๐˜ต ๐˜บ๐˜ฐ๐˜ถ ๐˜ฆ๐˜น๐˜ช๐˜ด๐˜ต. ๐˜ด๐˜ฐ๐˜ฎ๐˜ฆ๐˜ธ๐˜ฉ๐˜ฆ๐˜ณ๐˜ฆ ๐˜ช๐˜ฏ...