RUWAIDAH

By Mumseeyama

16.6K 757 218

Labari ne mai cike da soyayya ma rikitarwa da kuma makirci wanda duk yanda kaso ka hana abinda Allah ya tsara... More

Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 13
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35

Chapter 21

499 29 26
By Mumseeyama

*RUWAIDAH*

'''Love And Romantinc Story💋'''

*Salon Na Daban Ne.👌🏻*

~*Free Book*~

            _*NA*_
        
_Real Ladingo Oummu Fareesa😘_
 
*Ƴar Mutan  Niger🤙🏻*

'''Wattpad@Rahamaummufareesa'''





*Bismillahir Rahmanir Raheem*


*Chapter 21*

Mummy tace ɗasu islam“Kai kun ishemu da surutu, sai kace ba maras lfy garemu ba haba.” ta faɗa tana shafa bayan Ruwaida jin yanda take ajiyar zuciya ajere.   Sani dai driving ɗinsa yake, haka ya ɗauki hanyar gida.
             Ɓangaransu Rahma kuwa, bayan sun fita sun samu me napep Asma'u wanda zai kaita gidanta ta shiga, Rahma da Zainab suka nufi gida.  Suna zuwa suka tara da innah ta ɗora girkin.   Rahma ɗaki taje ta cire kayan jikinta ta dawo, nan ta zauna kusan uwar tana kama mata aiki.  Innah ta kalleta tace“To su Rahma manya anje an dawo hankali ya kwanta ko? Ke kuma Zainabu baki mana wuff da wani matashin ba? Dan naga wajan cike yake da manyan jami'an tsaro, amman kunyi dare salon malam ya gama faɗansa akaina.” Rahma tace“Haba innah me yasa kike haka ne dan Allah?” Zainab tace“Innah karki damu zanyi ai bamu gama zuwa ba.”ta faɗa tana dariya.   Rahma tace“Oh kina nufi...”Zainab ta gifta mata ido alamar tayi shiru.   Innah tace“Rahma zaki gane me nake nufi nan gaba sakara banza tashi maza je ki fara ƙoƙarin gyara kanki.” Malam Ɗahiru ya shigo da sallama.  Rahma ta amsa tana masa sannu.   Malam yace“Rahma sai yanzu kukazo? Ya mai jikin?”  Rahma tace “Da sauƙi Baba suna gaisheku.” Innah tace“Ai ko baice Rahma zaki faɗa na sani ai, tashi kije kiyi aikin gabanki.” Zainab tace“Baba sannu anty tace acema ta wuce gidanta. Malam yace“Yauwa Zainabu Abu, to madallah.” Innah ta taɓe baki tace“Allah ka mana mekyau ga aure yazo ba mazaunin kirki, inaga jibi fa ake kawo akwatina ga ciwo ya samu, da abari ya warke ayi kome a tsari...”Malam yace“Duba Zinaru ki iya bakinki ba ƙarawar da zamuyi sai ɗai idan sune suka nemi hakan.”Inna tace“Uhummm nayi shiru abu yazo ga manya, nayi shiru.” Rahma miƙewa tayi tana dariya, sosai take jin daɗin yanda Babansu yake takama innar tasu burki.   Bayan Rahma  taje tayi duk abinda take ta dawo ta zauna suna hira da Babansu haka har sukaci abincin dare sukaci gaba da hirasu, Rahma tayi ta ƙiran Acp bata samesa ba wayarsa akashe ita kuma da wuri tayi bacci dan lokacin da Abbah ya kunna wayar tashi ɗaya har yayi bacci.    Su Ruwaida suna zuwa gida taje tayi wanka ta saka riga maras nauyi, dakyat Mummy ta lallaɓata taci abinci kaɗan, taje ta kwanta.    Kwance  Ruwaida take saman gado ta naɗe cikin blanket, bacci ya fara ɗaukarta, Widaad na ɗaukar karatu, islam na kwance tana game.  Wayar ta ta ɗauki ringing, islam ta zumburo baki tace“Wayyo yaya Musaddiq ka rasa wa zaka ƙira ina game ɗina  sai ni dan Allah!”  Widaad tace“Wlh gobe muna zuwa hospital idan mun taso daga school se na faɗawa Ya Safuwan bakya karatu sai tsinanna game, Ruwaida ki tuna min na faɗa masa.”   islam tai picking ɗin call ɗin, tana manna wayar akunnenta.   Daga can Musaddiq yace“Ke!! Islam maza taso buɗemin ƙofar parlo wai ina Mummy inata ƙiranta bata ɗauka, wayar Acp akashe?”Islam ta gwalo idanu tana mamakin wai ba'a ma faɗa ma Ya Musaddiq Abbaye ba lfy.  Islam tace“Ya Musaddiq to wa ya kawoka daga Airport ɗin.”Musaddiq yace“Dallah zo buɗemin a texi nazo.”islam ta miƙe tana faɗin“Sorry Yayana ganinan zuwa.” tana faɗa ta zare wayar akunneta taga yama  kashe ƙiran ta ɗauki hijab ta saka ta nufi ƙofa.  Ta kama handle ɗin ƙofar zata buɗe wani ƙiran ya shigo, idanunwa ta waro waje ganin sunan Abbaye na yawo tace“Na shiga uku Ya Abbaye!” Ta faɗa tana ɗaga ƙiran cikin rawar jiki, ta masa sallama.  Daga can ya muskuta kaɗan cikin isarsa da izzar da ta gama ratsa jikinsa, yace“Ke!! Uban me kike bakiyi bacci ba? Ina Ruwaida bani ita.”Islam cikin tsoro tace“Yaya daman Ya Musaddiq ne yazo yanzu har nayi bacci ƙiransa ya tayar dani.”  Abbaye yace“Munafuka muryaki batayi kama da me bacci ba... Sanna karki ce masa banida lfy ki barshi se da safe....” ya faɗa yana jan dogon numfashi, ya tsani jan mgn bai sake mgn ba ya dafe kansa.
                    Dam islam ta isa bakin gadon da sassarfa ta beƙa hannunta tana tashin Ruwaida.       Ruwaida ahakanli ta buɗe manyan dara-daran idanunta tana miƙa, dan baccin ya fara mata daɗi sosai.  Islam ta manna mata wayar a kunnta tace“Ki riƙe Ya Acp ne.”Ruwaida ta sanya hannu ta riƙe wayar tana zumburo baki tana lumshe idanunta.   Islam da sassarfa tabar wajan tana isa ƙofar ta murza key ta buɗe ƙofar ta fice.    Acp ya hurama Ruwaida iskar bakinsa ta wayar cikin kunnenta, can ƙasan maƙoshi cikin siririyar murya ya ƙirata.  Ruwaida!”Ruwaida wani zirrrrrr yarrrr taji acikin dukan jikinta, sbd yanda Acp ya ƙirata yaja sunanta sosai, runtse idanunta tayi tana jin yanda yake mata huci ta cikin wayar akunnenta.   Abbaye ya sake ƙiranta, cikin wata irin murya wacce sam baima san yanada ita ba.    “Ruwaida! Kinyi Addu'a kafin ki kwanta?”   Ruwaida ta ƙamƙame jikinta waje ɗaya tana zumburo baki, tana gunguni, alamar tana mgn.    Abbaye ya shafi sumar kansa yace“Ok maza ki tashi kiyi alwola kiyi sallar nafila raka'a 2 kiyi duk irin Addu'ar da kika san kin iya, sanna maza tashi kije part ɗina..... Yaja dogon numfashi yana lumshe idanunsa, ya buɗesu tar yana kallon iyayan nashi suna kwance, suna hirasu, ba wanda yaji yo me yake faɗa, sbd yanda yake mgn can ƙasa, tamkar me raɗa.    Ruwaida ta lumshe idanunta tana ƙara maƙale wayar akunneta, tana gunguni irin “Uhm uhm.”  Abbaye ya muskuta dakyat yace“ uhm uhm me? Oya tashi maza kije saman bed ɗina ki ɗaga pillow  zakiga wayarki..... Yaja numfashi ya ƙarasa faɗin“Ki ɗaukota sai ki kuna (Suratul Baqarah)  oya tashi mana.” Ruwaida ta shagwaɓe fuska kamar tana gaban Acp ta fara gunjin kukan sangarta tana bubbuga ƙafafunta saman gado.  Abbaye yace“Idan na kilga 3 baki tashi kina wani min shagwaɓa, gobe karki zo wajena to...” ya faɗa yana jan dogon numfashi, baya ƙaunar mgn amman Ruwaida nason saka shi mgn, gashi ita bayi take ba.   Ruwaida ta fara gujin kukan shagwaɓa, ta miƙe zaune ta diro daga saman bed ɗin tana masa gunguninta, riga da wando ne na bacci farare masu samtsi ajikinta, sun mata kyau sosai, sai wular bacci ta rufe dogon gashinta ruf, haka ta nufi ƙofa tana gunguni wayar manne kunnenta. 
              Widaad ta ƙura mata ido ta riƙe haɓa tace“Kamtsin nana, wai daman Ya Safuwan haka yake iya mgn? Dan da halamu hira yake mata take wani masa shagwaɓa, uhmmm.” Ruwaida ta waigo ta kalli Widaad ta mata gwalo ta juya ta buɗe ƙofar ta wuce.
                   Abbaye bai sake magana ba bai kashe wayar ba, yana jin Ruwaida na tafiya bata fasa gungunin sangartar ba.    Islam tana zuwa key ɗin na jikin ƙofar ta buɗema Musaddiq.   Tsaye yake sanye wasu hadadɗun kaya, yasha kyau yana riƙe da madedeciyar trolley ɗinsa.    Islam ta faɗa jikinsa cikin murna tana faɗin“Oyoyo Ya Musaddiq i miss u so much.” Musaddiq ya rungumeta yana faɗin“Me too my sister!”Islam ta janye jikinta tana amsar trolley'n nasa suka nufo falon.   Ruwaida  tafiya take jikinta na motsawa tamkar tarwaɗa, haka ko inanta juyawa yake, wayar tana  manne a kunneta, Acp baice ƙalaba, haka itama tayi shiru, tana jin yanda yake sauke mata numfashi cikin kunnenta.   “Uhmm” kawai ta iya.   Safuwan yaji wani yammmm yanda taja uhmmm ɗin, ya lumshe idanunsa, yaja dogon numfashi.       
                           A tsakiyar parlon suka haɗu da Ruwaida.  Musaddiq yace“Ƙanwar Acp!”  Ruwaida ta waigo ta kalli Musaddiq, ta saki guntun murmushi ta zare wayar akunneta ta iso tana masa sannu da zuwa da hannunta.    Musaddiq yace“Ina zaki ne?”  Ruwaida ta masa nuni bedroom ɗin Abbaye, ta juya ta tafi, tana maida wayar kunneta.   Suka iso falon islma ta nufi ɓangaran Musaddiq tana jaye da trolley ɗinsa.   Musaddiq yabi Ruwaida da kallo yana shafa kansa, yarinyar na mugun burgeshi sosai.   Bayan islam yabi domin yayi wanka, yana faɗin“islam wai ina su Abbah da Mummy ko sunyi bacci ne?”  islam batayi mgn ba.   Tsaye tayi a ƙofar har ya iso ya saka key ya buɗe ƙofar, yana faɗin ba tambayarki nake ba?”islam ta kalleshi tace“Ya Musaddiq kaga yamin kashe kar na faɗa amman faɗa zanyi, wlh wajan kama wani ƙazurgumin ɗan mafiya ya harbeshi a kafaɗa, amman bai wani jimu sosai ba, wayane fa suke da Ruwaida yanzu...”Musaddiq yace“Subahanallahi amman aka rasa me ƙirana badan nazo ba kenan? Yanzu har Mummy suna hospital ɗin ne?”islam taja trolley ɗin ta shige ɗakin nasa tana faɗin“ A'a Mummy ta kwanta Abbah ne da kawu acan wajansa, kayi wanka kaci abinci sai ka tafi...”  Musaddiq ya juya yana faɗin“Aa sai naje naga lafiyar ɗan uwana, bari na ƙira sani ya kaini asibitin.” ya faɗa yana ficewa.     Islam ta fito tace“To sai ka dawo” ta nufi ɗakinsu.   Ruwaida kuwa tana zuwa ɓangaran Acp ta murɗa ƙofar ta buɗe, ta sanyo kanta haɗadɗan falon nashi,  wani ni'mataccan  ƙamshine ya daki hancinta, ta lumshe idanunta tana bubbuɗe hancinta ta shaƙi ƙamshin, wayar na manne a kunnenta ta fara gunguninta“Uhmm-uhmmm.” Ashgwaɓe.   Acp yace“Ruwaida!   Shiga bedroom ki ɗauko wayar mana.” da sauri ta buɗe idanunta ta fara tafiya ta nufi bedroom ɗin.  Nan ma saida ta murɗa ƙofar ta sanya kanta, sak ƙamshin Abbaye ɗakin yake, ga wani sanyi tamkar an kunna Ac.  Ruwaida ta nufi saman bed ɗin ta sanya lallausan hannunta, ta janye pillow ɗin taga wayarta a ajiye, ɗan murmushi ta saki na farin ciki, ɗaukar wayar tayi tana murmushi ta danna taga akunne, chaji saura 20% ta buɗe pasaword ɗin ta shiga whatsapp ta kunna data, taga sako ya shigo na Acp tin ranar da suka tafi police tation, mamaki tayi ya aka samu data, ko aiki yake da wayar?   Wani murmushin jin daɗi ta saki na farin ciki, ta ƙurama pic ɗinsa ido wanda ya tura mata ranar, yana zauna a office, unform ɗin ta kamshi sosai cikar zatinsa ta fito ba murmushi a fuskarshu, amman yayi mugun kyau kamar kasace shi.....     Acp wani irin daɗi murmushin ya masa ya ɗan ciza pink lips ɗinsa yace“ Angel Duk daɗin ganin wayar ne? Oya to jeki kiyi sallar se ki kunna karatun ki kwanta.” ya faɗa yana dafe kansa, yana runtse fitinannun kyawawan idanunsa, yana fesar da zazzafar iskar bakinsa waje, baya ƙaunar mgn ta wuce kalma.2 zuwa 3 yanada lfy ma.
                   Ruwaida jin daddaɗar murya Abbaye da yanda yake lanƙwashe mata harshe yasa bata san lokacin da ta faɗa saman bed ɗin Acp ba, ta lumshe manyan idanunta ta shagwaɓe fuska tana gunguninta“Uhmm-uhmm.” 
                              Acp ya gintse fuska kamar tana ganinsa ganin idan baiyi da gaske ba, bazata yi abinda ya sata ba, yace“Ke!! Malama tashi maza ki fice kwanciyar me kikayi?”Ruwaida ta zaro manyan fararan idanunta cike da mamaki ta miƙe zaune tana rarraba idanu ta sauƙo tana gunguni ta nufi ƙofar fita.   Abbaye yayi murmushi yanda baza taji ba ya tsinke ƙiran ya ajiye wayar gefensa ya lumshe idanunsa sbd baccin da yake ji.
               Ruwaida tana fitowa ta rufe masa ƙofar tana tafe cikin nutsuwa.  Islam tana shiga ta cire hijab ta kwanta, Widaad tace“Ina yayan?” islam tace“Yafa tafi asibiti wajan yaya uhmm su Aneesa gobe take amarya.”  Ruwaida ce ta buɗe ƙofar ta shigo.  Kallonta suka yi suna murmushi Widad tace“Anya Ruwaida ba love kuke da Ya Abbaye ba? Tab irin wannan sangarta?” Ruwaida ta dafe ƙirjinta ta waro idanunta waje tana nuni da hannu harda rantsuwa babu soyayya tsakaninsu.     Islam tace“Karki biyata fa, zo yi kwanciyarki.” Ruwaida ta ɓata rai sosai ta iso taba islam wayarta, ta jona tata a chaji, kafin ta gama sallah.   Widaad tace“Ƙanwar Acp yi haƙuri kaina bisa wuyana.”Ruwaida ta mata nuni da hannunta sun ɓata tinda ta ƙulla mata sharri.     Ta shige bathroom, ta ɗauro alwalla ta fita ta saka abaya kan kanyan baccinta, ta shamfiɗa dadduma, ta tayar da sallar nafila.      Musaddiq yana fita kai tsaye yaje ya taso Sani direba suka tafi hospital.   Acp cikin bacci yaji ana knocking ƙofar nasu.  Abbah ya miƙe yana murza idanu yace“Waye amman dai ba Nadeer bane shida nace ya bari da safe ya dawo?” ya faɗa yana miƙewa.
                     Karaf a kunnan Acp dan bai fiye nauyin bacci ba.   Abbaye ya buɗe tsaumammun idanunsa yana kallon mahaifin nashi, ya nufi ƙofar domin ya buɗe.    Yana buɗewa yaga Musaddiq a tsaye, Abbah yace“Musaddiq a daren nan haka?  To sannu.” Musaddiq ya rungume Abbah yace“Abbah shine akaƙi faɗamin ɗan uwana ba lafiya?” ya saki Abbah ya nufi wajan Acp wanda ya masu ƙurr da idanunsa.   Musaddiq ya zauna bakin gadon ya rankwafo ya rungume ɗan uwan nasa da sharan guda yace“My Acp namu sannu a Allah ya kiyaye gaba.” Abbaye yace“Amin my bro sannu yaushe ka iso?”  Musaddiq yace“Wlh yanzu ko wanka banba.” ya faɗa yana kwanciya saman gadon na Acp.   Abbah yace“Kaga tashi kaje gida gobe kazo ai da sauƙi kaje kayi wanka kaci abinci.”  Hamza yana baccinsa baima san me ake ba.   Musaddiq yace“A'a anan zan kwana da safe na tafi.” Abbah ya kwanta yana faɗin“Kai ka sani.    Acp yace“To ka tashi kaci abinci pls.” Musaddiq baisan musuba ganin jikin nasa ba wata matsala sosai ya buɗe abincin da su Mummy suka kawo yaci kaɗan yasha ruwa ya raɓa jikin ɗan uwansa suna hira har suka yi bacci.     Ruwaida Kafin ta kammala har su islam sunyi bacci, rigar ta cire ta linke daddumar, ta ciro wayarta a chaji ta kunna (suratul Baqarah) ta kwanta tana bi a zuciyarta har bacci ya ɗauketa, asubah ta gari.
                         Washegari tinda asubah Musaddiq ya dawo gida yayi wanka ya shirya ya ɗan kwanta kaɗan, kafin zuwa 10 ya koma hospital.    bayan  islam ta shirya Fu'ad shirin school itama ta shirya Widad ta shirya  suka yi breakfast Sani direba ya  kaisu makaranta.    Ruwaida nata baccinta, Mummy 8 cif ta gama shirin zuwa hospital har mom ɗin su Aneesa ta biyo mata zata kai masu farfesun da Hamza yace ta dafa masu na kan rago. 
             Ganin Ruwaida na bacci yasa ta barta suka tafi.   Nazifa tana zaune kan dining area tana shan tea  tayi kyau sosai cikun shirin zuwa school tanayi tana kallon wayarta ƙarfe 9 suke shiga lecture.   Giɗaɗo ne ya fito cikin shiri yana waya, yana faɗin“Wai ɗan gambo da gaske ne ko wasa, ai gwamma dai gudu??  Ƴar libah kuwa nayi mutuwa maras kyau, Innalillshi wa'inna ilaihir raji'un!!  “Amman na tausa masu, ya Allah kasa mu cika da imani, kai duniya mutum yaji tsoronta fa zanyi iya ƙoƙarina wajan temaka mata, kafin A shigar da ita kotu, ina zuwa zan ƙiraka anjima musan yanda za'ayi.”kitt ya tsinke ƙiran ya zauna.   Nazifa tace“Ya giɗaɗo kaida wa?”giɗaɗo yace“Nida me gulma.” bai sake kulata ba, ya zauna yana ƙiran“Mom kina ina ne?” Nazifa ta zumburo baki ta miƙe tana ɗaukar jakarta tace“Ya na tafi school.” bata jira ba ta nufi bedroom ɗin mom ɗinsu ta mata sallama ta fice.   Nazifa tana zuwa makaranta taji abinda ya ɗaga mata hankali wajan ƙawarta an harbi Acp jiya, yana hospital hankalinta yayi mummunar tashi ta matsu su gama lecture ta tafi ganinsa.       Ƙarfe 10 am Ruwaida ta farka tana naɗe cikin blanket sai mutsu-mutsu take.  A hanakali ta ware manyan idanunta tana miƙa haɗi da salati aranta, ta janye blanket ɗin ta fito da kanta waje, a inda ta ɗora idanunta ne yasa ta zaburo a mugun tsorace ta zauna ta ɗora hannunta akai tayi narai² da idanunta...!!!  _*Rahma ladingo ce😘 Oummu Fareesa*_

Continue Reading

You'll Also Like

1.4M 41.3K 37
အငြိုးတွေအမုန်းတွေကြား ချစ်ခြင်းကသာအနိုင်ရမလားဆိုတာကို ခပ်ကြမ်းကြမ်းလေး ခံစားသွားရမှာပါ။ warinng ‼‼‼ကြိုပေးတာမို့ မကြိုက်တဲ့သူများမဖတ်လို့ရပါတယ်
2.2M 148K 70
ဤဇာတ်လမ်းပါ အကြောင်းအရာသည် စာရေးသူ၏ စိတ်ကူးယဉ် သက်သက်သာ ဖြစ်၍ မည်သည့်အဖွဲ့အစည်း၊ လူပုဂ္ဂိုလ်ကိုမှ ထိခိုက်စော်ကားလိုခြင်းမရှိပါ။ #Boylove#Romance#Maf...
2.3M 234K 161
BL
3.1M 69.2K 30
လူတိုင်းပါးစပ်ဖျားမှ ဇမ်းဆိုတဲ့ကောင်က အပေအတေကောင်လို့သမုတ်လဲ သူတို့သတ်မှတ်ချက်အတိုင်းသွားပါစေ.....ကိုယ့်ထမင်းကိုယ်စားပြီး သူများစကားတွေကိုထိုင်ခံစားန...