Kwance take a daki kan gado tana danna wayarta ,jefi jefi tana blushing daga gani chatting take yi kuma ya mata dadi, koda saurayinta take chatting din oho....murya ta ji ana qwala mata kira .... "Maryama Maryama" "Na'am Mamaa" "Wai baza ki fito zuwa kitchen bah koh, kin san karfe nawa ne?.. kin fi so kiyi aikin nan ana shan ruwa duk ki wahala ki ba mutane tausayi" Ta sauri ta aje wayar kan gado ta jawo wani dan qaramin veil ta daura a kanta sannan ta fito ta tarad da mahaifiyarta da ke tsakar gida tana jiran fitowarta. Hajiya Lubabatu wato Mamaa yadda yaranta ke kiranta ,mace ce wanda baza ta wuce shekara arba'in bah a duniya amma pha sai idan an fadama ,kallon fuskarta kawai koh tsarin jikinta ba zai sa ka gane ainihin shekarunta bah, zaka dauka iyakar ta shekara 32 a duniya. wannan kenan....