CHAPTER 56

2.7K 265 13
                                    

Bayan Kamar 2 mins wayan yazeed ta sake ringing dubawa yayi yaga mom ne yayi murmushi sannan ya dauka kamin yayi magana mom tace my son bari muyi video call koh? Kasan na Dade ban ganka Ba.

Ta cikin wayan yazeed yaji Jamal na Cewa mom anya shi kikeson ki gani ?mom tace Allah zanci gidanku Jamal, izhab ila sallajah wa hadirny alhaleeb wal kaub minal matbakh

"إذهب الى الثلاجة و حضرنى الحليب والكوب من المطبخ"
"Go to the fridge and bring me some milk and cup from the kitchen."

Dauko laptop dinshi yazeed yayi sannan ya kunna nan yaga mom tana kiransa ya dauka murmushi ya fara sheko mata tare da sauke ajiyan zuciya domin wani dadi yaji sosai daya ganta dukda ko Ba a zahiri bane.

Yace wow! my sweetheart kinga farin da kikayi kuwa?kin kara kyau! Turo baki yayi yace Gaskiya nima zan biyoki.

Mom tace dubaka kai baka kalli kanka bane ji yadda kayi 'kiba kayi fari har kumatu ka ajiye da Anyi magana kace "ni banasonta Gaskiya tayi yarinya" ta fadi haka tana kwaikwayon yadda yazeed din keyi.

Bata fuska yayi Kamar yadda yara keyi Idan aka bata musu rai yace ni Nayi fishi ma kuma banyi missing dinki Ba.
Tace naji dama nima zakin baki na maka baki nakeson gani Ba. Ina diyata take? Yace tana kitchen mana.

Tace yi Sauri kakai inga yadda ka miyar min da ita kuma Idan naga ta rame ka Shiga iku. Yace haba momy nifa Bana zalinci kinsani so bazan zalinceta ba. Tace ai wasa nake maka kai mata mu gaisa nagani ko jikoki na Suna kan hanya.

Girgiza kai kawai yayi yana murmushi yace you will be disappointed kuwa tace wato mai hali bata fasa halinsa yazeed yace ehm gado Ba karanbani Ba. Dariya dukansu suka kyalkyale dashi dai dai lokacin yazeed ya iso kitchen.

Ajiye laptop din nasa yayi akan kitchen island din Yanda yake hasko minal sannan yayiwa mom alamun tayi shiru.

Sansadawa ya farayi dai dai lokacin kuwa minal tana rufe flask din data juye dumamenta tana wanka Hannu a sink.

Rungumeta ta baya yayi zata zabura ya matseta tareda rada mata shh nine and mom tana kallon mu.

Zaro ido tayi tana kokarin cire hannunshi tare da fadin yaushe ta dawo?rikota yayi kem yace a laptop dinane zo muje.
Daukanta yayi cidak Kamin ya juya ya nufi wajen laptop din da ita mom kam bakinta har ya fara ciwo saboda murmushin jin dadin ganin yadda taga 'ya'yan nata. Addu'a da fata take Allah ya karesu daga Sharrin dukkan mai sharri.
Sauketa yazeed yayi tare da riko hannunta yana fadin mom ga yar taki karki kiramin Yan sanda dariya mom tayi tace Gaskiya yazeed ka iya kiwo. Irin wannan kiba da daughter tayi sai kace ana hurata da iska masha Allah tabarakallah.

Minal sai lokacin a kunyace ta gaishe da mom saboda irin yanayin data ganta da yazeed ga rigar dake jikinta sai a slow.

Hira mom ta fara janta dashi yayinda yazeed ya tafi dakin zakiyya ya fara bude drowers dinta har sanda ya samo na ribbons sannan ya dauko 5 colours sannan ya dauko comb ya taho dashi. Koda ya shigo kitchen din ya zamu minal tadan saki jiki Suna hira da mom.
Comb din daya dauko ya fara yaje mata kai shareshi tayi taci gaba da hiransu.

Baki ya fara tsoma musu yayinda yaketa fafutikan daure mata gashin dai dai lokacin Jamal yazo yana lekowa yace wow bro masha Allah matarka badai kyau Ba Allah nima yar naija zan aura.

Hararansa yazeed yayi tareda matsar da minal Daga gaban cameran yace ayi Hiran a haka. Dariya Jamal ya kyalkyale dashi yace fadi Lanka tsaye kishi kake. yazeed yace ai bisa hakkina nakeyi.
Mom tace kai Jamal banson iskanci me yakai idonta kan matarsa nan dai sukayi sallama.

Yazeed ya kalli minal yace baby me kika Daga mana ne ?yunwa nakeji tace dumamen tuwo ne. Yamutsa fuska yayi yace dumamen tuwo kuma ? Tace eh yace please ki mana wani Abu mana tace anjima zan maka sounding serious dole yazeed ya bada gari. Zama su kayi akan island tasa Hannu ta fara fita masa tuwo. Mayan loma take tura masa yace na koshi, hararan sa tayi irin yadda kiyaye keyiwa yaransu Idan sunki cin abinci shiru yayi taci gaba dashi. Mutumin ka kan ace me ya lunkume Mara daya.  Wasa wasa kan minal taci nata loman ya cinye nashi. Daga karshe ya tsoma Hannu. Bayan sun gama ci yace mata zaije asibiti Daga nan zasu fara Shirye Shirye gyara guest side na gidan ind a su lukman zasu zauna.

Har kofa ta rakashi baiyi tsammanin zatayi pecking dinshi Ba to his surprise tayi pecking lips dinsa sannan ta buya zata tafi rungumeta yayi yace please karkiyi fushi dani! Tace banyi fushi dakai Ba ai. Yace kin tabbata ?ta gyada kai.

Neme neme ya farayi tare da waige waige tace me kake nema ne? Yace matsa kiga, matsawa tayi can ganin neme nemen bazai kareba tace Wai me kake nema ne yazzy baby? Duk ta kidime saboda yadda taga yana cube cube da alamu Abu mai mahimmanci ne.

Hannu yasa ya tallafo kumatunta tare da pecking goshinta murmushi tayi yace shi nake nema tace me? Yace murmushin ki! Shi nake nema tun dazu kika daina min murmushi sai mom kika yiwa kuma ya sokeni har cikin zuciya. Ya karasa magana yana Daga saitin zuciyar sa.

Dukansa tayi tace shine duk kabi ka rudar dani na dauka ma wani abinne me muhimmanci.
Hannu yasa a kunkuminta ya janyota tare da farin murmushin ki abune me muhimmanci da tsada a gareni. Duk Wanda ya rabaki dashi zan rabashi da farin ciki sannan duk Wanda ya saki murmushi to zan faranta mai.

Hannun sa guda daya ta kamo da hannayenta biyu tace na gode sosai kuma Insha Allah nima zanyi iya kokarina wajen ganin na faranta maka.

Rungumeta juna sukayi Suna masu jin dadi yazeed ya dauko wayansa yace selfie!

Nan suka dinga watsa pictures tare da yin fuskoki iri iri abin gwanin ban sha'awa kamin yazeed ya fita badan ranshi yaso Ba.

Sorry masoyana Nasan babu yawa amma Kuyi manage.

Karku manta Ku latsa wannan star din sannan Kiyi commenting.

Love you all😘

Takuce karamarsu babbarsu

Miss untichlobanty💕

15th December, 2019.

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now