32.

1K 118 13
                                    

MADUBIN GOBE  32.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

***

Kawu Muhammad sauraran bayanin Mami yake har ta gama ya sauƙe numfashi yana cewa.

"Sadiya anya Alhaji Mamman kan shi ɗaya."

"Ni ma ban sani ba Yaya Muhammadu, ni dai ga Nuratu dan Allah ta zauna zuwa nan da wani lokaci."
Mami tace ta ɓangaren ta.

"Shikenan amma kar ki damu, kinyi dabara da ki ka turo ta, sannan kar ki damu wannan lokaci ba zamu barshi ba."

Sun jima suna waya kafin ya kashe ya miƙawa Nuratu wayar ta karɓa ta shige ɗaki bayan dogon nasiha da Kawu Muhammadu ya mata akan kar ta damu komai zai wuce.

Da safe ƙarfe tara Dr Awwab ya shirya zai wuce, bayan ya yiwa su Kawu Muhammadu sallama tare da godiya suka ce sune da godiyar dawainiya da yayi da Nuratu. Har ƙofar gida suka suka rakoshi kowa ya koma ciki aka barshi da Nuratu.

Yana zaune cikin motar, ƙofar a buɗe Nuratu ta riƙe murfin motar, duk yanda ya so su haɗa ido ta ƙi yarda.

"Babyna."

Yace yana riƙe da wayarshi ya saita dai-dai fuskarta yana ɗaukar hotanta da bata ma san mai yake ba. Jin abin da ya faɗa yasa Nuratu haɗa rai ta watsa mishi harara.

"Ni ba Baby bace, bana so."

"To Babyn waye? Mami? Kin ma Mami girma. Babyna ce ke soon za ki yarda da hakan Noor."

"Ni dai ka gaishe da Hanan da Ummi sai anjima, Allah ya kiyaye hanya."
Tace ta rufe motar.

"Ameen Babyna za su ji."
Yace ya kunna motar yana barin gurin ta juya cikin gidan cike da kewa. Haka kawai ta ji kewar rashinsa kusa, yana sakata nishaɗi.

Tana komawa gida wanka tayi ta kimtsa jikinta ta canza kaya ta ɗauki wayarta ta ƙira Col. Ahmad, yana shirin tafiya duk ya harhaɗa kayansa zai koma Ibadan ya samu ƙiranta suna tare da Umma tana mishi faɗan da har jiya ta kasa dai masa akan ya rabu da Nuratu ko ta ɓata masa rai, kuma aure ne ta bashi nan da sati biyu in ba haka ba zata aura masa ƴar uwarsa ƴar ƙanwar babanshi.

Col. Ahmad bayan ya gama sauraran faɗan Umma yace.

"Mami maganar gaskiya ba zan miki ƙarya ba bazan iya rabuwa da ita ba amma maganar aure na janye tsakanin mu da ita. Kallon ƙanwata nake mata Umma, abin a tausaya mata ne wallahi, tana buƙatar taimako da kulawan uba ko yaya, dan Allah kar ki rabani da ita. Maganar aure kuma na amince in har hakan zai saka ki yarda da ni."

"Ka amince har ranka, kuma ka min alƙawari ba zaka taɓa kawo min maganar auren wannan yarinya ba ko gaba, in har kayi hakan ka tabbatar zan nuna maka ni na haifa ka."

"Na amince Umma in har za ki barni in taimaki rayuwar Nuratu."

Col. Ahmad yace har cikin ranshi.
Shi ba wai auren bane baya so yawan canje-canje wajen aiki da yake samu ba zai iya yawo da iyalai ba. Rashin aurenshi da Nuratu ya riga ya amince cewa babu aure tsakaninsu sai dai wani ikon Allah. Ko kuma Alhaji Mamman ya janye kudirin shi na auren Mufid da Nuratu.

          

Ganin ƙiran lambar Nijar ya san daga Nuratu ne, ya sashi miƙewa tsaye.
"Umma zan wuce ku gama magana da su Baba."

"To yaushe za ka dawo? Kar fa ka tafi ka ƙi dawowa kamar kullum."

"Zan dawo Umma inshaAllah zuwa nan da wata ɗaya da kwanaki."
Yace ya ja akwatin shi ya fita a falon.

Driver ne ya kai shi airport, jirgi zai bi ya tafi, bayan ya sauƙe shi ya ƙira Nuratu da tana waje tana ta ya Nazifa aiki da duk yanda taso ta hanata taƙi. Jin ƙarar wayar ya sata miƙewa daga wanke wanke da take yi ta shiga ɗaki tana ɗauka.

"Col. Ina kwana? Na ƙira baka kusa, na isa lafiya ƙalau tun jiya da yamma."

"Ya hanya ƙanwata, to allahamdulillahi, kin same su lafiya?"
Ya faɗa ta ɓangaren shi yana taka matakalar hawa jirgi.

"Eh ya mutanen gida?"

"Lafiya ƙalau, nima ina hanyar komawa Ibadan."

"Allah ya kiyaye hanya, sai anjima aiki nake."

"To shikenan ki gaishe da mutanen gida in na dawo zan zo."

To ta amsa dashi ta kashe wayar ta fita taci gaba da aikinta.

***

Waya suke da Yayan marigayin mijin matarshi yana shaida masa akan zai shigo zuwa nan da kwana biyu dan tattauna wani magana.
Alhaji Mamman sauraron shi kawai yake har ya gama kamar yana son fahimtar mai yake shirin zuwa yi yace.

"Amma Alhaji da ka sanar da ni dalilin zuwan dan zan yi tafiya zuwa Gombe."
Alhaji Mamman yace dan son sanin dalilin shi kawai na zuwa.

"Laa ba wani abu bane, ƴar wajen tsohuwar matar ka Al'ameen yake neman aure, shine za mu zo muyi maganar."

Dama yaji hakan a ranshi in ba haka ba menene zai neme shi abinda bai taɓa faruwa tsakanin su ba.
Murmushi taƙaici yayi yace.
"Ita Nuratu ce ta turo shi bata sanar daku na mata miji ba. To aurenta saura sati bakwai ba sai kun zo ba Alhaji."

Da mamaki Baba yace.

"Ikon Allah wallahi bamu da labari ina tsammani ko shi Al-ameen ɗin bai sani ba."

"Ai yanzu kun sani."
Alhaji Mamman yace ya kashe wayarshi yana buga tsaki. Wannan yarinya na gaza mishi maganganu.

...

Ɓangaren Baba yaji wani iri sosai jin wacce Al'ameen yake nema an mata miji, da ma bai fita aiki ba ya leƙa ɗakin matar shi ya sanar da ita yadda su kayi da Alhaji Mamman ya ce ta sanar Al'ameen shima za suyi maganar da shi.

"Wallahi kamar ya san bama son auren nan."
Tace cikin farin ciki.

"Zan wuce aiki sai anjima."
Yace ya fita sai yaji gaba ɗaya bai ji daɗin haka ba ko dan yanda Al'ameen ya so aurenta duk da abin da ya faru da ita.

...

Bugun ƙofar gidan yayi ya ji shuru babu kowa ya shiga kai tsaye cikin falon gidan kamar yanda ya saba.

"Wai ke Sadiya wace irin ƴa kika haifa? Anya yarinyar nan jinina ce? Ko dai aljana ce ba mutum ba ce?"

Mami da ke zaune tana bin Alhaji Mamman da kallo yana wannan maganganun, huci yake kamar zaki da zai ci babu.

MADUBIN GOBEWhere stories live. Discover now