Chapter 125

173 18 0
                                    

Ammabuwa dake kwance a uwar daka taji motsi kamar Ammi ta shigo, mikewa tayi daga kwancen da take jiki babu kwari ta lalaba ta fito. A kan kujera ta hango Ammi a kwance ko motsi batayi, wani irin harbawa kirjinta yayi tayo kanta a guje tana kiran "Ammi! Ammi!!"

Amma Ammi inaaaa, ganin Ammi ko motsi batayi yasa ta mike a guje ta nufi waje, ta soma kiran makwabta ta suzo su kawo mata doki, nan fa aka shishigo aka soma taimakawa a fita da Ammi sai asibiti.

Ammabuwa sai faman kuka takeyi, Suna isa asibiti straight aka wuce da Ammi emergency room, luckily Ashraf yana asibitin don dr Dangora yana tafiya aka dawo dashi yayi resuming aikinsa, hankalin Ashraf a tashe ya soma tambayar Ammabuwa meya faru, tana kuka tace itama bata sani ba, dawowan Ammi kenan ta fito ta taddata a hakan"Ashraf dan Allah Ku taimaka ku ceto mun Ammi kar na rasa ta please, ya Allah gani gareka wayo ni". Sai faman kuka take tamkar ranta zai fita.

Anty Rakata ranta a bace ta mike ta fita don ta kira Huda don tasan daga wajenta Ammi ta fito, gudun kar Ammabuwa taji yasa tayi nesa tukuna ta soma dialing number Huda, ringing buyi ta dauka zatayi mata magana cikin gatse kamar yanda ta saba, Anty Rakata ta dakatar da ita "wai ke wace irin mutum ce, yanzu fisabilillah me kika yiwa mahaifiyarki ta dawo haka?"

"Ban gane ba, meya faru?" Huda tambayeta.

"Toh Amminki dai an kawota asibiti rai a hannun Allah, sai kiyi sauri kizo"

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, meya sameta?"

"Kinfi kowa sani". Anty Rakata ta bata ansa tana jan tsaki".

Hankalin Huda a tashe tace "wani asibitin?"

"national hospital"

"Toh gani nan zuwa".

Cikin sauri ta katse wayar, ta dauko gyalenta da makulin mota a kidime ta fito sai hanyar asibiti, a waya ta kira Muhseen ta sanar dashi halin da ake ciki, shima hankalinsa a tashe yace gashi nan zuwa.

Ammabuwa na zaune dasu maman Luba har yanzu kukan nata bai tsaya ba "Ammi fa lafiyanta kalau ta bar gida, bata fada mun inda zata ba, yanzu ya zanyi maman Luba, taya ma zamu fara biyan kudin asibiti? " ta tambaya, kuka takeyi sosai kamar ranta zai fita.

"Ammabuwa addu'a ya kamata ki dinga mata yanzu ba kuka ba, kuma batun kudin asibiti, ba Ashraf yace abar komai a hanunsa ba? Karki damu". cigaba sukayi da bata baki suna rarashinta.

Sai bayan 30 minutes tukuna Huda ta iso asibitin, tana ganinsu Ammabuwa ta karaso hankalinta a tashe ta soma tambayar Ammi, Ammabuwa ko kallonta batayi ba ta kawar da kanta gefe ta cigaba da kukanta, su Anty Rakata suka bata ansa sukace tana emergency har yanzu, bata tsaya wata wata ba ta haura sama, tana wani irin gudu kamar wata zarariya, cikin sa'a kuwa sai ga Ashraf ya fito a guje Huda ta karasa wajen shi tana fadin "Ashraf ina Ammi' na?! Dan Allah ka kaini inda take inaso ganinta! Inason na nemi gafararta i want to see her please!" .

Ashraf ya tsaya yayi shiru yana kallonta ya kasa cewa komai. fuskarsa babu walwala, kana ganinshi kasan yana cikin tsantsan tashin hankali, "Magana nake maka! Nace ka kaini wajen Ammi'na". ganin ya tsaya ya kasa bata ansa yasa ta juya  fusace zata nufa emergency room din Ashraf yazo ya sha gabanta yana fadin "i'm sorry Huda amma sai dai ki dau hakuri don Allah ya yiwa mahaifiyarki rasuwa".

Cak Huda ta tsaya, sanadiyar bugawa da kirjinta yayi daga bisani ta soma magana tana girgiza kai
"No karya ne! Ka daina mun irin wanan zancen bana so, Ammi'na bata mutu ba! Ka kaini inda take yanzun nan!".

"Kiyi hakuri Huda kafun mu shiga da ita cikin theatre ta cika, there was nothing we could do".

Matsawa da baya tayi ta jingina da jikin bango tana zaro ido don jin maganar Ashraf tayi tamkar a mafarki, cigaba da zaro ido tayi tana expecting yace mata ba gaskiya bane,  dataga yayi shiru sai faman binta da kallon tausayi yake yasa ta gasgata maganarsa ai kuwa bata san sanda ta fadi a wajen ta rushe da wani irin  kuka mai cin rai, kuka take irin wanda bata ta'ba yinsa ba cike da nadamar abunda ta aikata, Ashraf ya kasa ce da ita komai don bai ma san ta inda zai fara rarashinta ba,  a hankali ya juya jiki a sanyaye don yaje ya sanar dasu Ammabuwa, yana tunanin ma ta yanda zai fara.

HUDA🔥 BOOK 2Where stories live. Discover now