Bayan sun idar da Sallah sun gaisa da Hajiya, sun tab'a hira, sai Mahwish ta ja Xulaihah daki, suka zauna, su na fuskantar juna, Xulaihah cikin zumud'i ta ce,"Na matsu na ji, ya akai har ki ka fara kiran Yah Sa'eed, da Yah Sa'eed, domin a iya sani na, rabon ki da ki kira shi da yaya tun kafin ya furta maki kalmar so, tun su na zuwa da Baffah Sageer gidan nan"
"Hummm Xulaihah labarin mai tasho ne, kuma Yah Sa'eed ya ce na daukar masa alqawarin ba zan sanar da kowa me ya faru ba a lokacin da Yah Salim ya kawon ziyara gidan mu, abinda kawai zan iya ce maki shi ne, Yah Salim ya barar da soyayyar shi, ya sa na tsane shi, na zare shi a zuciya ta, a yanzu ina qoqarin na ba wa miji na dama ne, ko Allah zai taimaka min na so abinda yake halal dina, kuma mallaki na, Xulaihah na gane cewa bayan ku 'yan uwa na, bani da masoyi sama da Yah Sa'eed, dan haka zan ci gaba da bashi girman shi da Allah ya bashi, zan kuma ci gaba da mutunta shi, har Allah ya yi ikon sa akan mu"
A guje Xulaihah ta bar gadon ta, ta fad'a jikin Mahwish ta na murna, ta na ihu, tare da hamdala, Hajiyar su ce ta shiga dakin ta ce,
"Lafiya? Ku ba kwa girma ko?"
Da sauri Xulaihah ta labarta wa Hajiya abinda Mahwish ta sanar da ita, na hakura da soyayyar Salim,da qoqarin ba wa Sa'eed dama da take yi, nan fa suka zauna su na ta murna, Hajiya ta zauna a tsakiyar su suka jingina da ita kamar yanda suka saba a baya,
"Mahwish Allah ya miki albarka, na ji dad'i sosai da 'ya ta ta dawo, waccan mara kunyar ta tafi, inshaa Allahu ba za ki yi dana sani ba a rayuwar ki, sannan ki sani, mu na nan a ko da yaushe ki ke da buqatar mu, za mu zo, ko da ta waya ne za mu baki lokacin mu, kar ki nemi taimako a wajen kowa sai Allah, kuma kar ki nemi shawara a wajen kowa sai iyayen ki, ko 'yar uwar ki, mu kad'ai ne mutanen da ba za mu guje ki ba, ko da duniya ta juya maki baya, Allah ya albarkaci rayuwar auren ku, da zuri'a muminai salihai, ai Sa'eed d'in ya shiga mun gaisa, Abban ku ya dawo, ki je ku gaisa"
"To Hajiya inshaa Allahu ba zan baki kunya ba, zan ajiye duk wani abu da ya faru a baya, na fuskanci gaba, Allah ya shige mana gaba kar ya bar mu da iyawar mu"
"Ameeen Yah Mahwish, kin ga yanzu tunda kin amince gidan auren ki ne, zan iya kawo ziyara ko?"
"Kwarai da gaske,"
Su na ta hira su na dariya suka isa parlour, Sa'eed na cin abinci da surukin shi, duk ya takura ya na jin kunya, su na had'a ido da masoyiyar shi, ya faki idon mutane ya kanne mata ido d'aya, tare da alamun kiss, da sauri ta rufe bakin ta, ta na zaro ido, ta hau kalle kalle ko da wanda ya gan shi, ba wanda ya gani sai Xulaihah da ta kasa ta tsare, gaba daya sun gama tafiya da ita, sun burge ta ainun, nan da nan ta fara nazarin Yah Mahwish wanne shirme ne ya sa ta son Salim dama tun farko ga Sa'eed?
Mahaifin ta ya ji dad'in ganin ta sosai,kuma ya nuna mata hakan, sun sha hira har akai la'asar sannan Hajiya ta shiga d'aki, ta debar wa 'yar tata humrar HUMKAM fara da baqa,da su turaren wutar HUMKAM, ta debar mata su daddawa dakakkiya, kuka, kub'ewa busasshiya, yaji dakakke da ya sha garlic ,da dai sauran abubuwan buqata da ta san bata da su.
Godiya suka dinga yi wa Hajiya, su kuma suka raka su har bakin mota, Xulaihah na alqawarin zuwa in ta gama jarabawa.
"Ina ganin in za ki zo ki sanar da mu, dan wataqila za mu yi tafiya,"
"Inyeee su Yah Mahwish za a bar garin Kano, tun da ki ke ba inda ki ka taba zuwa a Nigeria fa,"
"Qarya ki ke yarinya, in da na zaga tun kan a haife ki da yawa,"
Dariya suka dinga yi, dan shekara biyu kawai ta bawa Xulaihah, ba wasu shekaru masu yawa cancan ba.
Ko da suka isa gida sun tarar da bangaren Tasneem da takalma da yawa, da alama ta yi baqi, bude wajen su suka yi, suka shige, a gajiye ta zauna ta na fad'in,
YOU ARE READING
MAHWISH
Romance.....She is very stubborn like a rock, she is yarning for love, she is beautiful like the moon......