SO KO WAHALA? PAGE 38

44 2 0
                                    

*HAƊAKA WRITER'S ASSO...🖊️*

*❤️😭SO KO WAHALA?😭❤️*

                 NA

MARYAM MUHAMMAD SANI (Mum Amnash)

11/Almuharram/1443 - 20/8/2021

               3️⃣8️⃣

Duk yanda ta yi ƙoƙarin ƙwacewa abun ya faskara, kakari kawai ta ke tana neman mai ƙwatarta. Sai da ta kusa sumewa sannan Baban Mama ya tunkuɗe ta, Allah ya taimaketa ta yi zaman ƴan bori daɓas, raɗaɗin da ya ratsata yasa ta fashe da wani marayan kuka.

Shima kukan ya sa ya rasa mai zai cewa Hadiza, kawai sai ya ɗebi silifas ɗinsa ya fice daga gidan ya na kuka, har ya isa gidan Hindu bai ci karo da kowa ba.

  A fusace ya fara buga ƙofar, da sauri Hindu ta buɗe ƙofar. Bai ce mata komai ba ya matsar da ita gefe ya shiga gidan, da sauri ta bishi bayan ta mayar da sakatar ƙofar.

   A tsaye ta ganshi ya na kuka shaɓe-shaɓe, a take zuciyarta ta ɗan sosu, duk da bata san dalilin kukanshi ba, amma tasan koma me ye yana da alaƙa da Leema.

Kai tsaye ta ƙarasa kusa da shi don ta bashi haƙuri, ba zato ta ji ya rungume ta, gaba ɗaya tausayinshi ya lulluɓe ta. A hankali ta ja shi bakin kujera suka zauna, har lokacin ya na jikinta, hannu ta sa ta fara share masa hawayenshi, sannan ta fara ɗan bubbuga bayanshi a hankali tamkar ƙaramin yaro.

     A hankali raɗaɗin da zuciyarshi take yi masa ya ragu, da taimakon addu'o'in da ya ke yi. Tsam ya miƙe ya nufi banɗaki ya wanko fuskarsa tas, sannan ya dubi Hindu yace "Kina da sauran kayan kari?" Kafin ya rufe baki ta nufi kichin (Madafa) da sauri ta ɗauko masa kunun tsamiya da fanke ta ajje a gabanshi. Kunun ta tsiyaya masa a kofi, har za ta zuba suga yace "Kar ki saka min suga," miƙa masa ta yi kai tsaye ya fara kurɓa yana lumshe ido, ɗan tsami tsamin na ratsa bakinshi a haka har ya shanye.

A kusa da ƙafafunshi Hindu ta zauna, ta fara ɗan mammatsa masa ƙafafun, cikin hikima ta fara yi masa nasiha "Mijina a jiya na yi alfahari da kai, da ka kasance mai haƙuri juriya da dangana a kan abun da ya faru. Na sani akwai ciwo rabuwa da masoyi, amma duk abinda Allah ya yi shi ne daidai. Ina son ka ƙara kwantar da hankalinka, ka cigaba da addu'a, idan kuma auren ka ke so ka nemi wani, zan baka goyon baya ɗari bisa ɗari, ba wai don ba na kishinka ba, a'a sai don ina son duk abinda ka ke so. Allah ya sa hakan shi yafi zama alkhairi, amma..."

Kama hannunta ya yi ya zaunar da ita a gefenshi sannan yace "Kar ki damu uwar Ƴaƴa, na riga na fauwalawa Allah dukkan lamurana. Na kuma godewa wadda ta sabbaba lalata auren, duk da da mummunar niyya ta yi hakan. Hindatu ina mai tabbatar miki za ta girbi abinda ta shuka, haƙiƙa za ta ɗebi kashinta a hannu..."

Bugun gidan a ke kamar za a ɓalla ƙofar, da sauri Hindu ta miƙe ta je ta buɗe, tiris ta yi ganin Hadiza amma sai ta matsa ta bata hanya ta shiga ciki, sai da ta rufe ƙofar sannan ta bi bayanta da sauri.

******

Yana Isa gida ya shiga ɗakinshi, akwatinshi ya ja ya loda kayanshi ya kinkima da sauri ya kai maƙotansu gidan Hajiya ya ajje. Bai tarar da Hajiyar ba sai Khamis abokinshi kawai a gidan, wai sun tafi ɗorayi an yi musu rasuwa. A ɗakin Khamis ya baje, duk yanda ya dameshi da tambaya ƙin faɗa masa me ya ke damunshi ya yi tilas ya ƙyale shi. Ko minti talatin bai yi da kwanciya ba, barci mai nauyi ya ɗauke shi.

Duk da tafiyar ba nisa gareta ba amma a gajiye  tiɓis suka ƙaraso, ko da ya ke ansha kacaniyar biki.

Aunty ce ta buɗe gate ɗin da mukullinta, duk suka ɗuru ciki. Baba na riƙe da Leema suka shiga, zuwa lokacin hawayenta sun tsaya cak, zuciyarta ta kangare a ganinta tunda ta rasa Masoyinta ai rayuwa ta ƙare, tamkar an kasheta da ranta ne.

SO KO WAHALAWhere stories live. Discover now