🍇🍇KƳAUTAR ƘOƊA🍓🍓
(It's all about love, scracife, hatred and destiny)*Wattpad*
@NoorEemaan*EDITING IS NOT ALLOWED*❌
Page 23_24
(Not edited)
..................... Ciƙin wata murya da amon sa ke fidda zallan tashin hankali da yake ciki yace "meƙiƙa ce?" domin sam kunnenwansa basu yarda da abinda yaji ba.
ɗaga dayan ɓangaren Elizabeth ta sake cewa
"Nace Jikin ma'am ya tashi sosai, suna asibiti, tun uku na daren yau" ta karasa cikin gurbataciyyar hausar ta.Ba tare da ya sani ba ya saki wayar kasa, kana shima ya sulale kasan, wani mugun kuka ya saki, tamkar ba namiji ba, itama Mahmah kuka take, kukan tausayin danta domin taji abinda Elizabeth tace.
Ganin kukan kara gaba yake ya sa Mahmah ta samu ta rungume shi da kyar tana cewa "my son, Fadeel! Stop all this, ka nutsu kaji mezan ce maka"
Cikin kuka yace "A'a Mahmah, bazan iya nutsuwa ba, muradin raina na k'ok'arin mutuwa, tayaya hankalina zai kwanta, mahmah ki barni, ki barni na bawa Fadeelah *koda* ta, domin ta rayu, zan kasance cikin farinciki koda a kabarina ne idan Fadeelah na raye...."
"I said stop Fadeel! Bazaka mutu yanzu ba in sha Allah, haka itama Fadeelah baza ta mutu ba, baku cancanci mutuwa yanzu ba, ku duka biyun zaku rayu cikin farinciki"
"Taya ya hakan zai yu Mahmah? dole idan ban bawa Fadeelah *koda* ta ba, mutuwa zata yi, idan kuma hakan ya kasance zan kashe kaina, sannan bazan taba yafe wa kaina ba har abada"
"Son kasani cewa ni Mahmah'n ka bazan cutar da kai ba, umarnin nake baka kada ka bayar da kodar ka, shin kana tunanin fadeelah zata ji dadi ne matuk'ar tasan cewa kai ka bada kodar ka? ita ta rayu, kai ka mutu"
Sam bazata ji dadi ba, domin ta na buk'atar ka a rayuwar ta"....Share hawaye tayi kana tace "zan je asibiti domin a duba ni, ina kara maimaita maka, kada ka bada kodar ka wa Fadeelah".
Tana gama fadin haka ta mike hadi da daukar hijab d'inta ta fice...
Kansa ya shiga bugawa da bango da k'arfin gaske, har jini ya fara bin gefen fuskar sa, sai dai ko daya bai ji zafi ba k'amar yanda zuciyarsa ke masa matsanancin zafi tamk'ar an watsa masa narkakkiyar dalma. Gaba daya ya fita hayyacin sa, tamkar wani sabon kamu...
Zaune Mahmah take cikin adaidaita sahu, ji take kamar tayi tsalle ta ganta a asbitin. Duk gudun da matukin keke napep din keyi sam bata gani.
Bayan wasu mintuna suka iso, sauka tayi hadi da mika masa kudin sa, ta nufi cikin asibitin...Tun daga hospital din taga canji mai tarin yawa, domin security, bodyguards, hadi da sojoji ke zagaye cikin asibitin. Take jikinta ya bata cewa Fadeelah na asibitin. A ranta tace " ikon Allah, ashe asibiti daya muke zuwa checkup tare da Fadeelah"
Tana shiga cikin asibitin taga wasu mutanen masu yawan gaske fuskokin su cike da damuwa, kallo daya ta musu ta fahimci cewa su din dangin Fadeel ne, sai wani magidancin mutum dake tsaye idanun sa na zubar da hawaye wani baturen likita nayi masa magana wanda bata jin me suke cewa, take jikinta ya bata cewa mahaifin Fadeelah ne domin ga kamanin nan baro_ baro...
Direct office din doctor Gabriel ta nufa, yana zaune kuwa, yana wasu rubuce _rubuce a littafin kundin marasa lafiya, dago kansa yayi kana ya amsa sallamar hadi da cewa "a'a madam, ya kika zo yau? Ai ranar checkup dinki jibi ne, have a sit please"
Murmushin k'arfin hali Mahmah tasaki, kana ta zauna K'amar yadda yace, ajiye biron hannunshi yayi hadi hade hannun nasa cikin na juna, alamar ita yake saurare.
YOU ARE READING
KYAUTAR KODA
General Fictionits all about love, sacrifices, hatred and destiny. Saboda tsananin soyaaya uwa ta Sadaukar da kodar ta (kidney) wa budurwar dan ta, sosai littafin ke cike da chakwakiyya kala² hadi da tsabtatatciyar soyaaya da babu algus a cikin ta... Still dai Sad...