BAYA DA ƘURA 21-22

16 2 0
                                    

Aunty haliloss: *BAYA DA K'URA*

     AUNTY HALILOSS

*End free pages*

*Alhamdulillahi Anan Free Pages ya tsaya ina fatan zaku fahimce ni,  books guda biyu zasu zo muku akan 500₦ Wa nake aure da Baya da kura*

*Zaku iya tura kuɗin ku ta Accnt Number 0045643539.Halimatu Iliyasu k. Union Bank.*

*Ko ku tura katin MTN ta 09039080909.*

*Zaku tura shedar biyan kuɗin ta layin Marubuciyar 09039080909*

21.

Cikin sauri ya juyo yana kallonta,yadda take maganar yasan tabbas batasan yaga takardai,Moh'd ya sauke hannunshi,Islam tasa hannu ta anshi takardai.

Sai lokacin tasakeshi  tana ja da baya,wani kuka take saki mai tsuma zuciya.

Moh'd ya gewaya,ya zauna kan kujerar dake gefe,Islam tasa sa hannu tana yaga takardai,wasu hawaye suna zubo mata,Moh'd ya kalleta ganin tana ketawa  yasashi fad'in "miyasa?"danshi  gaba d'aya baisan takardai miye ba,dan bai karanta ba.

Islam tayi baya kamar zata fad'i,Moh'd yayi saurin tasowa,saidai Allah yasa ta fad'a kan kujerar dake baya,Wani irin kuka tasaki,ita kadai tasa yadda takejin zuciyarta take mata,Moh'd ya durkusa yana ruko hannunta yana fad'in" ya akayi,miya sameki"

Islam ta kauda kai tana gilgizawa,zuciyarta tanayi mata zafi,yadda maganar Dad take mata yawo a kunnai,so take tasamu Wanda zata gayawa taji sanyi,sai lokacin take tunanin batada wani dangi da zata gaya ma matsalarta,da abinda taji,tunani  tafara yi ko taje Kano tagayawa Yayan Babanta,wata zuciyar tace kada ki had'a shi da Dan uwan shi.

Islam ta kalli Moh'd,Moh'd yakoma kan kujerar,yana kiran sunanta,Islam ta kara kallonshi,"tel me plzzz"

Sai kuma ta kara kuka,Moh'd yace"kinsani  banison  kuka,taya zakizo  wajena kina kuka,kinsan bani so"

Yana maganar yana mik'ewa, takardai data yaga yje,ya d'auka,kan table din ya aje yana had'a takardai,kasan cewar duka gida 4 ta rabasu.

Tambarin court yagani,ya fara karanta takardai,takardai Sammaci CE daga kotu,Moh'd ya d'ago yana kallonta,Islam ta kauda kai.

Komawa yayi ya jawo wata plastic chair,ya aje a gabanta,ranshi ya b'aci sosai,yadda Islam ta jajirce wajan saita kai k'arar mahaifinshi,ya kalleta yace"kukan namiye?bayan kinyi duk abinda kike ganin ya dace?miyasa zaki yaga takardai bayan bataje  ga Wanda aka aikamawa ba"

Islam kuka kawai take,Moh'd ya mik'e yashiga Office dinshi,sai gashi ya fito da Gum a hannunshi,yafara lik'e takardai, Islam tasa hannu ta ansa tana k'ara yagawa,Mohd ya tsaya yana kallonta,cikin kuka ta fara magana"wannn ba takardar Abba bace"

Moh'd ya kalleta, yana nazarinta"ta waye?"

Islam ta durkushe tana kuka"wannn takardai ba da Abba ta daceba"

Moh'd ya tsaya yana kare mata kallo,lokacin wani sabon kuka yazo mata,nan fa yahau rarrashinta yana son tagaya mashi saidai Islam batasan taya zata gaya mashi cewar ga abinda taji daga mahaifin taba.

Moh'd yace"it OK,tunda bazaki fadiman ba,plzz kitashi kitafi gidan,Islam bazan jure ganin kukan kiba"

Yana maganar yana shirin Mik'ewa,Islam tasa hannu tana ruko hannunshi, dan ita kanta tasan a halin yanzu batada wani Wanda yafi Moh'd, shine kawai tasan zata iya gayawa matsalar ta.

Moh'd ya kalleta,yana komawa ya zauna,Islamta saka kuka,Moh'd yace"You see?"yana maganar yana harda hannuwa,Islam tasan sarai Mohd bayason kukanta,amma a halin da ake ciki bazata iya controlling kanta ba.

BAYA DA ƘURAWhere stories live. Discover now