PAGE__24

71 7 0
                                    

💎 _page 24_💎

*SAI DAKE!*🫀
       _written by_
*BILLY S FARI💎*

© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡

_Follow me on Wattpad @Billysfari9 https://www.wattpad.com/story/281979031?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=h1hTYUDmeeoMp11b3lTkCiCDDLppuAl%2B6kbyiK4cGXQ5e2Fg7YLuARy9Dcp%2BEVPxUXJImhmoAGRg72rOwrncWtECkGHwwVNmdJ%2BFopJSUVlXXQah7ciB4BN9KGwZqXho_

    💎💎💎💎

Sista Asma'u ce ta shigo a hargitse sai sheshsheka takeyi ko mayafi babu ajikinta, kallo d'aya zaka yimata ka fahimci tsantsar tashin hankalin da take ciki musamman idan ka lura da yanda gefen fuskarta ya kumbure had'e da jini, haka ma hannuwanta da qafafuwanta da ko takalma babu duk sun guggurje alamun ba qaramar wahala ta sha ba sai fitar da numfashi takeyi daqyar, maganar ma da tayi ba qaramin qarfin hali tayi ba wajen har had'o kalmomin data fad'a ba,

Da sauri Barrister Farida ta miqe had'e da d'aukar gorar ruwan dake ajiye a gabanta ta nufo inda take tsaye takasa magana sai hawaye dake faman ratatar mata a fuska, riqota tayi ta zaunar da ita akan wani dogon benci dake can baya ta bud'e gorar ruwan ta bata tasha sosai tare da goge mata hawayen da suka jiqa mata fuska tana kallonta cike da tausayi, don ta tabbata akwai kaidin daya biyo bayansu kafin su qaraso kotun.

Barrister Hisham ne ya miqe had'e da cewa.

"Ya maigirma mai shari'a, Kamar yanda kotu ke gani da idanuwanta, waccan baiwar ALLAH data shigo  d'aya daga cikin shedun da muka tanada ne don gabatar dasu agaban kotu, Lura da yanayin da take ciki kamar yanda kowa ke gani, muna roqon wannan kotu mai alfarmar data sake bamu wasu mintuna daga cikin lokuttanta koda mintuna biyar ne har shedarmu tasamu natsuwar da zata iya gabatar da shedar abunda ta sani akan wannan shari'a kafin yanke hukunci,  muna sa ran I zuwa wannan lokacin sauran shedun namu suma samu damar qarasowa"

Saida alqalin ya cire gilashin idonsa ya d'ora akan teburin dake gabansa tare da had'e hannayensa waje d'aya ya tallabe fuskarsa dasu sannan ya kad'a kai alamun ya amince da hakan cike da mamaki,

Sai a daidai lokacin Ra'ees da tunda ya duqe kansa qasa bai sake d'agowa ba, ya d'ago yana kallon sista Asma'u data shigo cikin yanayin daya kusan firgita kowa, a ta d'ayan b'angaren zuciyarsa kuwa yana mai farincikin ganin ta bayyana a kotun, ko ba komai yasan ganinta tamkar ganin Waheedarsa ne, don duk inda take yana da yaqini akan tare zasu bayayyana a gaban kotun, amma lura da yayi ita kad'ai ta shigo cikin kotun acikin wani yanayi mai wuyar fassarawa sai yaji gabansa ya fad'i, kansa ya shiga tambaya akan, shin me hakan ke nufi?, Ina Waheedarsa?, Me yafaru da itane da bai ganesu tare ba?, Nan take yaji hankalinsa ya tashi saboda yasan halin mahaifin nasa da kuma abunda zai iya, kallonsa ya maida wajensa cike da tuhumarsa akan koma me yafaru to tabbas akwai sa hannunsa aciki, suna had'a ido dashi yayi saurin d'auke kansa gefe, hakan ya tabbatar masa da cewa lallai zargin da yakeyi akan mahaifin nasa ya tabbata gaskiya, girgiza kansa ya shigayi yana hawaye cike da takaicin yanda dadyn nasa ya kasa fahimtar kuskuren da yayi ta qoqarin hanasa aikatawa tun d'azun.

Kallon sister Asma'u Barrister Farida tayi bayan taga ta d'an samu natsuwa had'e da cewa.

"Ina Waheeda, gwaggo, habule da kuma malan shehu?."

Kafin ta bata amsa sai gasu suma sun shigo kowanensu da rauni ajiki Abban Enaya da shi kad'aine bai jimu ba yana riqe da hannun Waheeda itama ta guggurje a hannuwa ta kuma ji ciwo a goshinta don har wajen ya kumburo, kallonsu tayi had'e da yiwa Barrister Farida nuni da idanuwa a inda suke tsaye,

'Dago kai Barrister Farida tayi ta gansu a tsai-tsaye Waheeda da tuni tsoro ya dabaibayeta sai faman b'uya takeyi a bayan Abban Enaya tana qara rirriqe masa hannu had'e da raba idanuwa, da sauri tamiqe ta saki ajiyar zuciya cike da farinciki tace

SAI DAKE.!Where stories live. Discover now