ZAMANINMU!!!
(Hattara yanmata)
Written story
By
AUTAR AREWA.
Pls subscribe my You Tube channel Autah Novel Tv.
Bismallahi Rahamanir Rahim.
🅿️6
📝 A takaice Farrah duk yinin wannan rana a cikin kunci tayi shi .Kin fitowa tayi daga dakinta,Har saida Momy taga shiru bata da niyar fitowa,kannan ta leka dankinta.
Har zuwa wannan lokacin Farrah a kwance take.
"Farrah wai yau meyake damunki duk yinin yau na ganki cikin damuwa,?Dan Ina tinanin ko break banga kinyi ba".Tashi zaune tayi tana kokarin gyara hular kanta.
"Walllahi Momy banjin dadin jikina ne,Amma yanzu zan fito insha Allah".
"Tau ki fito ki ci abinci sai kisha magani ko"?
Cewar Momy ta juya zuwa kiching dan ta karasa girkin da ta dora." Da addu'a a bakinta bakinta ta shiga toilet ta fara kokarin yin wanka,sosai take durzar fatar jikinta kamar mai shirin sauya colour jikinta.
Bayan ta fito cikin nitsuwa take shiryawa,riga ta saka orange colour ta material doguwar riga ce hap gount.gashin kanta tayi parking a tsakiyar kanta,Daurin dankwali ta murza yayi kyau sosai domin ya zauna das a kanta. Duk da ba wata kwalliya tayi sosai ba amma tayi kyau.
Tana fitowa ta tadda Yaya Jabir a dinning table,Bata yi mamaki ba dan ya saba irin haka zuwa da sassafe.Har ta ji sanyi a ranta,dan shi Yaya Jabir baya da matsala jininsu ya hadu,Koda tana yarinya idan har suka zo katsina tana makale da shi.
Da sauri ta karasa gurinshi da murmushi akan fuskarta.
"Ah Yaya Jabir Kai ne yau a gidanmu " ?tana kama bakinta alamar mamaki.
Kallanta yakeyi sosai yanda jajayen labbanta suke motsawa gwanin sha'awa.
"Oh! ni Yaya Jabir irin wannan kallo haka kamar na sauya kamanni"?
Kujerar kusa da shi ta zauna ta riko hannunshi,kayi hakuri ba laifina ne ba wallahi Yaya Yasir ne ya hanani fita ko'ina.
Hannunshi ya yi kokarin zarewa daga nata Yana kallanta ya ce "ai nasan ba laifinki ne ba,shiyasa ni na zo".
"Tau nagode daka fahimce ni, Ina kwana ? Ya su Ummah?.
"Duk suna lafiya lau"
Plate din da yake gabanshi ya turamata,mu ci abinci dan nasan Baki ci ba ko? Ya yi tambayar yana tsareta da ido.
Zunburo bakinta tayi alamar shagwaba, "wallahi kaman ka sa ni banyi break ba".
"Ja'ira aiko yanzu zanyi maki dura,dan haka gwamma ki ci da yawa,"oya maza ki shanye wannan, Yana turamata cup din kakkauran tea gabanta.
Sosai ya bata dariya har fararan hakoranta suka fito,ta ce wallahi har ka tinaman lokacin kana yiman duren abinci".
"Ai lokacin bakya san cin abinci".
Abinci suka ci gaba da ci cikin nitsuwa,da annashuwa.sosai suke kama duk da ta fishi haske da dogon hanci.
_____________
Yinin wannan ranar cikin farin ciki tayi shi,sai ta ji kamar bata da wata damuwa a rayuwarta.Dan girkima tare suka shiga kiching ya tayata sukayi.
Momy kuwa tuni tana bangaranta Nusaiba kuwa tana Auwal direver ya kaita islamiyya.
Bayan ya dawo daga masallacin magriba,dakinta ya nufa knocking ya yi.Budewa tayi ganin shine ta ce" har ka dawo kenan"
"Eh ki zo muyi denner ni wucewa zanyi"
Ciki ta koma ta cire hijaf din da tayi sallah ta fito.
Suna cikin cin abinci Momy ta fito da waya a hannunta ta mikawa Farrah, "Anshi Auntyn ku ce ta kira watanki a kashe".
Ita harga Allah sai yanzu ta tina da batun wayanta da zalimu ya ansa,shaf ta manta saboda zuwan Yaya Jabir ya daukemata kewa sosai.
Karawa tayi a kunnanta tare da yin sallama.
"Amen wa'alaikas salam Farrah Ina kika saka wayanki inata kiranki swich off".
Ta danyi shiru saboda ta rasa abida zata ce,sai wata dibara ta fadomata tayi saurin ce wa
"Aunty wayan matsala ta samu sai na ajeta"."To farrah da kin fadama yayanki tun kafin ya taho,Amma ba matsala ki ba matar Yaya wayar" (tana nufin Momy).
Da sauri ta Mika wayan saboda yadda ta ji kirjinta na bugawa da karfi .
Momy daki ta nufa tana ci gaba da waya da maman Farrah.
Jabir kuri ya yi Yana kallanta , kamar mai San gano wani abu,saboda yana kokwanto akan abinda ya ji ta fada.
Kara sadda kanta ta yi tana jujjuya cokalin hannunta.
Ji tayi yana ce wa "Farrah abinda kika fada gaskiya ne kuwa?. Ya kafeta da idanunshi.Sosai Yaya Jabir yake yimata kwarjini , Amma duk da haka tana ji a zuciyarta bazata iya sanar da shi ba Wanda ya anshe wayanta ba.
Hmmmm "ni zan wuce" Yana kokarin mikewa tsaye ya tattara wayoyinshi ya zuba a Ajjihun wandon juens dinshi .
Tare suka jero zuwa inda yayi parking din motar shi,Bayan ya zauna a cikin motar ya Kai dubansa inda take tsaye,ya ce "wallahi ki daina tsoransa,ya anshe maki waya amma bazaki iya fadi ba".
"A a Yaya Jabir ba haka ne ba"
"Matsa daga nan ko na mintile bakinnan mai ciwa,Amma idan Yaya Yasir ne sai kiyi kaman ruwa ya cinye ko".
Ita dai Bata Kara ce wa komai ba sai wasa takeyi da zoben hannunta.
"Ni na wucesai Allah ya kaimu next week"
"Tau Allah kiyaye Nima zanzo insha Allah"
"Allah yarda" cewar zabir da yake kokarin fita daga gidan.
Ta dade tsaye a wurin har aka budemashi gate ya fita,kafin ta samu damar Jan kafafuwanta da sukayimata sanyi zuwa cikin gida.
Pls
Following
Vote
Comment
Share 👏.BY
AUTAR AREWA.
YOU ARE READING
ZAMANINMU!!! (Hattara yanmata) (Complete)
RomanceKowacce rayuwa na cike da kalubale,musamman rayuwa da kawaye,ta amince da su,ta basu amanar kanta,Amma su burunsu suga bayanta. Amintar dake tsakaninsu yasa ta mallaka masu sirrinta,sai dai kashhhhhhh ta makaro. A kokarinsu na ganin su ja...