GUGUWAR ZAMANI...🌺🌺🌺
Written by Zaynab Yusuf ✍🏼
Bismillahir Rahmanir Rahim
PAGE:01
Kowani dan adam na dauke da kundin qaddara,wasu kundin kaddararsu na dauke da shafuka masu matukar firgitarwa dakuma jarabawa kala daban daban,kundin kaddarar Zainab tasha banbam da saura,domin cikinta babu komai face bakin cikin rayuwa mara gushewa,Sannan tawuce tunanin duk wani mai tunani,da'ace tanada iko da tuntuni ta goge wahalar datake ciki acikin kundin qaddararta sannan ta nesanta kanta daga al'ummar data fito.
Ta jima tana kallon naira darin da ahmadu ya jefeta da ita,hawaye na racing daga idanunta,ta rasa gane awani gurbi zata saka halayyar ahmadu,rashin so ne ko kuma tsantsar qiyayya yake mata itada'ya'yanta?ta jima tana tunani sannan ta miqe ta dauki darin tana juyata,zuciyarta na tafarfasa,Hijab dinta dake saqale ajikin igiya ta saka,tunani yasha kanta kawai jefa kafa take har ta qarasa shagon shazali,miqa masa darin tayi batareda tace komai ba,zuwa ynxu yasan abunda taje buqata dakuma adadinsu,garin kwakin 80 da sugarn ashirin..ya miqa mata ta karba hawayen baqin ciki na zubo mata,yanzu wannan shine abincinta dana 'yayanta biyu na yau,what sort of life is this?what wrong has she done?she hs been a good person all her life,a good daughter,a better wife and an amazing mother to her kids.share hawayen tayi ta daga kafa domin she's quite sure her kids are back from sch,so she guessed right suna matsakaicin tsakar gidansu azaune,elder one na koya ma qaramin karatu,basu lura da shigowarta ba,ita kuma saita jingina da bango tana kallon su yayinda wasu zafafan hawaye ke sauka daga idanunta,ahaka rayuwar 'ya'yanta zata chigaba da kasancewa?cikin halin rashin kula,rashin cima mai kyau,dakuma rashin ilimi tsayayye?sai ahmadu ya gadama yake biya musu kudin PTA,halayyarsa gareta tamkar kisa ne batareda d'igon jini ba,ya kashe fitilar farin cikin rayuwarta,runtse idanunta tayi Ahankali zuciyarta nace mata"be strong,kodan 'yayanki".
saida ta sauke ajiyar zuciya sannan ta shiga tsukakken kitchen dinta ta wanke garin ta zuba acikin kwano da spoons 2 sannan tafito,zama tayi akusa dasu tana sakin murmushi,da murna sukace"sannu da aiki Mami".tace"kune da sannu,gashi kunsha rana,Bismillah kuci abinci".murmushi babban yayi batareda yace komai ba domin he knows where their prob lies,he knows exactly what they're going through,he knows the kinda Dad they have at this tender age of his.Cin garin sukai hankali kwance suka kora da ruwa.
Suna shirin zuwa islamia Ahmadu yay sallama cikin gidan da voice nashi mai saka yaro mara ji nutsuwa,mai saka yaro mai nutsuwa maida hankali,mai saka babba shakkarsa matuka...zubewa sukai a gabansa "Sannu da zuwa baba".,yace"yawwa,har anyi shirin islamia?to maza ku tafi"yafada trying to initiate something else,dasaurinsu suka tafi shikuma yabi Inda Zainab dake tsaye da kallon tara saura kwata yace"Nalura rashin mutunci gaba kika samasa ba baya ba,har kinkai matsayin da zan shigo kikasa min Sannu?".
Tsura mishi idanu tayi for some minutes sannan tace"ka wuce dukkan wani matsayi agareni ada,amma baa yanzu ba dakai watsi da haqqin mu,ka wofantar da rayuwarmu,taya zan ga matsayin ka bayan kai bakada buri saina tozarta rayuwata?taya zan riqa tunawa da matsayinka awurina bayan ka watsar da nawa matsayin?taya zan cigaba da faranta maka bayan kai baka damu danawa farin cikin ba?".
Hawaye masu dumi ne ke saukowa daga idanunta,
"Kaji tsoron Allah ahmadu,kasani dani da yaranmu amana ne awurinka,sannan yayanmu ababan kiwo ne agaremu,Akwai ranar da zamu ma Allah bayanin irin kiwon da mukai musu,laifin me mukai maka?idan ni baka tausayina ai kaji tausayin 'ya'yanka,idan baka sona ai kaso 'Yayanka,Idan baka kaunata ai ka kaunaci 'Yayanka,amma ka rufe ido kayi fatali da rayuwarmu,kabarmu cikin qunci da matsin Rayuwa yayinda kake shoshalewarka awaje son ranka,kaji tsoron ranar da baki bazaiyi magana ba ahmadu....."tafashe dawani gigitaccen kuka mai taba zuciyar mai sauraro da imani,kuka take of two different types,nafarko kukan rayuwar datake ciki,na biyu kuma kukan rayuwar daza cigaba dayi.
Dogon tsakin da ahmadu yaja ne ya tsayar da kukan nata,da mamaki in transfixed take kallonsa,babu shakka ahmadu na sawun farko acikin marasa imani da tausayi,sulalewa tayi qasa ta zauna tana kallon yadda idanunsa suke bin jikinta cikeda,tsantsar matsifa ce ke cinsa wanda kallo daya zaka tabbatar da hakan,saida ya qare mata kallon banza sannan ya hankade curtains din dakin ya shiga,wannan na daya daga cikin halayyar ahmadu da Zainab tayi disliking with passion,he can spend 3days without saying a word or so,even to the kids.....miqewa tayi jiki ba kwari tabisa cikin dakin,yana tsaye yana qirga kudade,ganinta baisa ya boye ba sannan Hakan bai zamto abin mamaki ba gareta,asanyaye tace"ba qaramin mistake kake aikatawa cikin rayuwar mu ba,ka gyara tun kanada sauran lokaci"..
Smiling yayi yace "ga Kudin ahannuna ki kwata mana".
Tace"bazan qwaci kudinka ba,kamar yadda bazaka iya kwatar yafiyar mu ba,domin babu shakka sai Allah ya bimana haqqin mu,kada ka manta,adduar wanda aka zalunta batada hijabi ".tana kaiwa nan tafice daga dakin,hijab dinta ta mayar tafita,tana tunanin inda zataje tasamu sauki dakuma shawarwari,Nafisa aminiyar ta ce tafado mata arai,layi daya ne ya raba gidajen nasu,ta tarar da Nafisan tagama girki,murmushi tayi tace"kin iya zuwa,yanzu na sauke abinci".murmushin takaici Zainab tai tace"magana nazo muyi Nafisa,duk duniya banda yar uwa kuma qawa tamkarki,nasan zaki share min hawaye na sannan ki sanya farin ciki acikin zuciyata koda na mintuna kadan ne kafin na koma gidan uquba ".
Zaunar da ita Nafisa tayi sannan ta zubo musu abinci,saida suka gama ci sannan tace"Ina jinki Zainab ".
"Rayuwata na gab'ar rugujewa Nafisa,narasa kaunar mijina narasa farin cikin rayuwata,narasa kulawarsa narasa jin dadin rayuwa,na rasa tausayinsa na zama abar a zubar ma hawaye,matsaloli kullum qaruwa suke,rashin imanin ahmadu sai ninkuwa yake,ban san yadda zanyi ba Nafisa,nayi kukan,nayi adduar,nayi nasihar,nayi waazin,nayi matsifar amma duk abanza,nafisa ya zanyi da rayuwata?".
Sosai nafisa ke tausayin rayuwar Zainab,asanyaye tace"kicigaba da haquri,sannan ki dage da addua,ki nemi sana'a,we're in the 21st century,not all women depend completely on their spouses ,it pains me alot because anyi normalising Hakan,amma inason ki tashi ki nemi nakanki kodan rayuwar 'yayanki".
Murmushin takaici Zainab tai tace"saida kudi ake neman kudi,sanin kanki ne dafaffan abinci MA gagarata yakeyi bare jarin Sana'a ".
Nafisa tace"karki damu,zamu tattauna zancen da maigidana,zai nemo solution Insha Allah ".
"Kinyi sa'ar miji nafisa,daya tamkar da dubu,mai kaunar ki dason ganin farin ciki,wanda ya tsaya tsayin daka saida ya tabbatar baki rasa komai ba na rayuwa,Allah barku tare".cewar Zainab
Hararar Zainab din tai tace"Insha Allah mijinki zai dawo kan hanya shima ".
Saida tacikama Zainab flask da abinci sannan tabar gidan cikeda shakku,yauce rana tafarko data taba karbar abinci zuwa gidanta,koma Meya faru waya ja?
+++++++++++
Agaban tukubar tsire suka ga babansu na faman ci,suka karasa wurin da murnarsu "baba mun dawo"...takaici ne ya tokare masa wuya,kafin yay magana Manu mai tsire yamiqo masa wani tsiren daban yace"shima tsinke biyar dinne"hannu yasa cikin aljihu ya baiwa manu kudinsa,Kallon Aliyu yayi yace"kama qaninka ku je gida".
"Baba Ina zaka ?"Aliyu ya tambaya yana rau rau da idanu,murmushi Ahmadu yay yace"zanje wurin antynku,wai tsire take kwadayi,maza ku wuce gida"yakarasa maganar yana zare idanu,da sauri Aliyu yaja Ayan suka shiga gida.
Da sallama suka shiga gidan,Zainab dake alwala ta d'ago da murmushi,amsawa tayi tanajin farin cikin ganin yaranta,they truly are blessings in her life,ganinsu na sanyaya ranta yayinda maganarsu ke sanya mata hope,dauriyarsu ke qara mata courage sannan haqurinsu ke sanyata tunanin mafita,tana Tsaye sukai Alwala suka tafi masallaci,da kallon birgewa tabisu tamkar ba ita ta d'ora su kan turbar dacewa ba da ikon Ubangiji,ta hadiyi wani miyau mai d'acin masifa dakuma kaifi,wanda kaifinsa zai iya yanke makoshi,tsuke idanu tai ahankali hawaye masu d'umi na zubo mata,Tabbas Nafisa tayi gaskiya,lokaci yayi daya kamata tafara cin gumin halak dinta,lokaci yayi daya kamata ta nuna ma ahmadu cewar idan kanada garin hakuri dana nutsuwa, yana da kyau ka hada su a turmin kunyah ka daka su da tabaryar ilimi sannan ka zubasu a tandun wadatuwa da Dan abinda Allah yabaka.Daga sannan ne zaka fara jin qanshin fure na rayuwa mai dadi....shimfida tabarma tayi ta ajiye flask din abincin da plate da spoons dakuma kayansu,Yaran na shigowa suka cire uniform din islamia,wanka sukai suka zauna bisa tabarmar,"Aliyu zuba muku abincin "cewar Zainab dake bakin famfo tana wanke musu uniform dinda suka cire,"Dan Allah mami ki bari na wanke".Aliyu yafada sounding helpless,tai dariya tace"Bismillah ".da saurinsa ya taso tana wankewa yana dauraya,ahaka suka gama,ta zuba musu abinci suna ci Ayan yace"mami yau muka ga baba awurin manu mai tsire,...."bige masa baki Aliyu yayi yana huci,ya tsani abinda zai sa Zainab kuka ko damuwa,shiyasa bai taba fada mata sun sha ganin ahmadu awurin masu kaji da sauransu,Murmushin takaici tayi tace"Kadena saurin hannu kaji Aliyu na?"tafada hawaye na zubo mata,shima hawayen yakeyi zuciyarsa na tafarfasa,at this tender age of his yasan muhimmanci dakuma darajar mahaifiyarsa,yasan farincikinta yafiye masa komai,da sauri ya miqe ya shiga daki,kan katifarsu yafada yana kuka mai cin rai,kallon Ayan tai wanda shima yake kallonta yana hawaye,she hugged him tightly crying out loud,she never thought they knew what they're going through,even for once,even after trying to hide things,even after her fake smiles and acts...bataso su taso da qiyayyar ahmadu aransu,bata fatan Hakan.