*NAZIR..!*
_(The journalist)_
*(Based on luv and Romantic story)**Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty❤️**🅿️6*
"Tunda suka shigo anguwar Nusiba tabar kuka takoma ba idonta Abinci,domin tundaga farkon anguwa tafahimci anguwace tamasu dashi,kokuma kososhi a gwannati.
Bata gama mamaki ba sai da taga an zuba hon awani tamgamemen gida wanda tsaruwanshi,kamar akasar turai,ai Nusiba bata kara Raina kanta ba sai da suka sulala parking space din,haka take bin ko"ina da kallo cikin nuna zallan kauyanci,dole ta nuna don duk a iya tsawon Rayuwarta bata taba ganin gidan daya tafi da ita ba irin wannan.Ashe kallonta na tafe domin,sai da sauko daga motar tana karema,Harabar gidan kallo,tabbas ba shakka Naira na inda take ba abunda yafi daukan,hankalinta irin tsararrun motocin dake pake a harabar gidan masu kyau da tsari birjit kamar ma bamasu hawa,tana chan gurin kalle kallenta har Su kawu sukayi gaba bata fargaba sai da taji kawu na mata mgana.
VC Adam galadanchi ne akan gaba yayi sallama acikin falon,musty ne ke tsaye cikin shirinsa na zuwa asibiti harda rigar likitocinsa ,ya kalli Abban nasa cikin mamaki zai yi mgana kenan,sai yaga Kawu jibo yashigo da Anty bayansa Sai Nusiba tana ta zuba kauyanci baki sake.
Abbu yace yana kallon musty"Kai mustapha kiran min Amminku"Yafada yana fadin"Bismilan ku,ku zauna don Allah"Dukkansu akasa suka zauna suna bin tsararran falon da kallo ita kuwa Nusiba wanda aka kira da mustapha dake bi da kallo,kamar tasan fuskan nan awani guri bata dawo daga tunaninta ba Ammi tasawo kai Falon tana Fadin"Abbu lafiya kadawo kuma? Alhalin yanzu ka fita..?
Tafada tana karisowa falo karaf idonta akan Nusiba wacce ke kallon inda taji mganan suna hala ido,suka sakarma juna mirmishi lokaci daya.Abbu yace yana gyara zama"Kedai bari Fatima ina tafe ne da baki"tace tana zama gefensa"Allah Sarki sannunku da zuwa"Kawu ya amsa yana gaisheta,ta amsa da sakin fuska idanunta nakan Nusiba,Anty tadago suka gaisa,kana Nusiba ta gaisheta,mikamata hannu tana fadin"Zo nan yata,Abbu ina kasamomana yar budurwa mai kyau haka"Tafada tana dariya.
Nusiba tatashi a kunyace ta isa ga Ammi tana dukar dakai,Zata zauna akasa Ammi tayi saurin zaunar da ita kusa da ita,tana fadin"A"a zauna kusa dani,yata kinsan ni uwar maza ce,to duk inda naga budurwan mace sha"awa take bani"
Abbu yayi dariya yana fadin"To gashi Allah ya baki ai"Yafada yana yawaita dariyarsa,kafin yafara koramata jawabin komai tagumi ta zabga tana fadin"kaji ko,wlh wasu mutanen sam basu da imani,ita Rayuwa babu lamani"Abbu yace"Ai haka wasu suke,babu komai ai mallam jibo mun dade muna aiki tare,yanzu shine nake tunanin Mustapha yakaisu gidana dake zoo road.
Ammi tayi saurin cewa"A"a Abbu don Allah kabarsu anan gidan don Allah"Tafada hartana dangwabe kai Dariya Abbu yayi,yana kallon mallam jibo yace"Kaji mallam jibo,shin zaku zauna damu? Zama na Amanar juna"
kawu yadago hawaye yacika idanunsa yace"Yallabai bamu dace da zama daku ba,dadai an barmu...."Meyasa zaka ce haka mallam jibo? baku son zama damu ne"Ammi ta katsesu tacigaba da cewa"Anzama daya fa muma,mutane ne kamar ku,don Allah ku zauna damu wlh ganin farko na muku kuka shiga Raina,don Allah"Tafada tana rikema Nusiba Hannu.
Kawu yayi saurin cewa"Mun yarda hajiya,wlh mun yarda kun wuce mtsayin komai agurin mu,muda zaku taimakamawa,mungode Allah ya saka da Alheri,Allah kara girma"yafada kwallah tana zubomai Abbu yace"Ashh..Mallam jibo meye kuma Abun kuka? don Allah bari.
Anty itama tana ta godiya Ammi tace"Babu komai wlh,ni wata alfarma ma nake nema? Anty tace cikin mamaki"Wata alfarma hajiya? Ammi tace tana dafa Nusiba"Diyarki zaki bani,nikuma na baki mustapha,gashi nan tsaye"tafada tana Nuna mustapha dake tsaye Hannunsa akirji,Anty tayi mirmishi tace"Ah!Babu komai na baki ita,nikuma na dauki dana Mustapha"Tafada tana kallonsa.