🎐🎐BAMBANCIN AƘIDA 🎐🎐
( ƙaddarar Soyayya )Based on true life story
Haƙin Mallaka
Queen Nasmerh
&
Nana M Sha'aban*PRESENTED BY KING AIMAR PALACE*
_NOTE: Wannan labarin anyi shi a gaske, zai taɓa aƙidu daban-daban, dan haka duk wanda ya karanta littafin ya ji bai ji daɗi ba, ko kuma ya yi dai-dai da halin da ya taɓa tsintar kansa yayi haƙuri, ba mu yi shi dan cin zarafi ba, true life story ne. Akan aƙidun da za ku ci karo da su kuma ba mun yi ba ne dan nuna matsalolin aƙidun ba, mun yi ne da bayyana asalin labarin, dan haka ba mun ce lallai haka halayyar su ke ba._
*_GODIYA TA TABBATA GA UBANGIJIN SAMMAI DA ƘASSAI, YA ALLAH MUNA ROƘANKA YADDA MUKA FARA LITTAFIN NAN LAFIYA MU GAMASHI LAFIYA, ALLAHU, ARRAHMAN, ARRAHIM._*
WANNAN LITTAFIN DAGA FARKONSHI HAR ƘARSHE SADAUKARWA NE GARE KU MASOYAN LITTAFIN NAN.
__
*CHAPTER 09*"Mamyn yara!"
"Na'am Abban yara" Mamy ta amsa tare da mai da hankalinta gurin Abban, "jiya mijin Raheema ya zo da daddare, wai yana so yau Raheema ta zo ta kwana saboda yau da safe zai je Zamfara gurin aikinshi sun tura, dan yayi wani aiki a chan zai yi sati" Mamy tace "Raheema abin nema ya samu wai matar ɗan sanda ta haifi bindiga, to me zai sa ta zauna a gidannata idan yaso ko ƙanwarsa ce Faɗima ai ya turata ta tayata kwana, ba na son ta sabata da zuwa gida ta kwana, ka ga dai yadda nake fama da ita kafinta tafi, wani lokacin ma tana kuka take tafiya, kamar wata ƙaramar yarinya" Abba yayi dariya yace "barta! ai wannan karan idan ta zo sai na yi mata gargaɗi, mijinta yana dawowa ta tattara ta bar min gida, karta ƙara ko da mintina goma" Mamy tace "da ka taimaka, ƙila idan ka faɗa mata haka, tayi zuciya" Abba yayi murmushi tare da cewa "bari na fita ana jirana a waje, kin san har mun zauna karatu nace bari na dawo na ganki na sanar da ke zuwan rigimammiyar ƴarmu" Mamy tace "to Allah ya taimaka","Amin" Abba yayi maganar tare da miƙewa, ya fita farfajiyar gidan, inda suke karatu.* * *
Abbakar kuwa suna zuwa gidansu, ya shiga bubbuga gate ɗin gidan, saboda ya ga ya tura ya ji a rufe yake da alama mukulli aka saka ta ci, aka kulle gate ɗin, Mama wacce take tsaye riƙe da taɓarya daman jiran zuwansu take dan haka ta buɗe ƙofar gate ɗin tana cewa "Abbakar karka sake ka ƙara koda taku ɗaya ne kai da wannan bayahudiyar idan ba haka ba, zan chanza muku kamanni da taɓaryar nan" Abbakar jikinshi yayi sanyi dan ya fuskanci da gaske Mama take zata iya buga musu, "Mama dan Allah kiyi haƙuri ki bari mu shigo" Mama tace "Abbakar idan har ka ga ka shiga gidannan da Arniyar nan to wallahi mutuwa nayi!" Abbakar ya saki hannun Angela ya fara ƙoƙarin kama hannun Mama, Mama tayi saurin dakatar dashi cikin tsawa tace "karka sake ka taɓani, idan ba haka ba ranka zai yi mummunan ɓaci" Abbakar ya haɗe hannuwansa biyu waje ɗaya yana cewa "ki duba girman Allah, dan ƙaunar da kikewa Annabi Muhd (s. a. w) ki bari mu wuce" Mama ta kalle shi kamar za ta ce wani abu sai kawai ta ajiye taɓaryar, ta nufi ɗakinta, Abbakar ganin haka, ya sa ya juya ya kama hannun Angela suka shige ɗakinshi, akan gadon ɗakin su ka zauna, Angela ta kalle shi fuskarta cike da damuwa tace "yanzu a haka zamu ci gaba da rayuwa, kowa ba ya ƙaunar zamanmu a tare" Abbakar ya yi murmushi ya ce "Kar ki damu, insha Allah komai zai yi dai-dai kamar ba'a yi ba, daman da farko dole zamu fuskanci ƙalubale daga wajen iyayenmu, dan haka ina so ki zama mai haƙuri da juriya, ni kuma nayi miki alƙawari, ba zan taɓa juya miki baya ba, ina ƙaunarki sosai" Ya ƙarasa maganar tare da janyota jikinsa yana bubbuga bayanta, ajiyar zuciya ta shiga saukewa tare da lumshe ido, kalaman Abbakar sun sanyaya mata zuciya, kuma sun sanya zuciyarta cikin farin ciki, bacci ne ya fara ɗaukarta daman ta daɗe bata samu baccin ba, dan rabonta da bacci yau kwana biyu kenan, ko mintina biyar batayi ba, bacci mai nauyi ya kwasheta, ɗaukarta yayi cak kasancewar Angela siririya ce bata da nauyi, kwantar da ita yayi a tsakiyar gadon, shima ya kwanta yana rumgume da ita, ƙare mata kallo yayi gaba ɗaya, riga da wando ne a jikinta sunyi matuƙar kama jikinta sosai, sai wani siririn mayafin data yafa a jikinta, kansa ya dora kan kirjinta a hankali bacci ya fara ɗibansa.____°____°____
"Sani!"
Ɗagowa yayi ya kalleta, dan tun da suke tare bata taɓa kiran sunansa ba, sai dai tace *Habibi ko Masoyi* "Na'am Zeenart" Ƙura masa ido tayi tace "Ina sonka sosai, ba na tunanin zan iya rayuwa ba tare da kai ba, a duk lokacin da aka ce na zaɓi ɗaya rabuwa da kai ko mutuwa, zan gwammace na mutu da na rabu da kai, a kullum idan na tuna da cewa muna da BAMBANCIN AƘIDA, ina jin zuciya kamar ta fashe, dan nasan shine zai rabamu, iyayena ba za su taɓa bari na auri wanda ba aƙidarmu ɗaya dashi ba" Sani ya sauke nannauyan ajiyar zuciya yace "Zeenart! ina ƙaunarki fiye da yadda kike ƙaunata, dan haka nayi miki alƙawari BAMBANCIN AƘIDA, ba zai taɓa rabamu da ke ba, ko me zai faru sai na aure ki" Zeenart ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Allah ya tabbatar" Murmushi ya yi ya ce "to ki ɗan yi min murmushi mana, na ji daɗi a zuciyata" Murmushi tayi wanda har sai da fararen haƙoranta suka bayyana, "yauwa ko ke fa" Sani ya faɗa yana gyara zamansa akan dakalin da su ka zauna. Zeenart ta ce "Yau na ji daɗi mun daɗe tare da kai" Murmushi ya yi ya ce "gaskiya kam! ya kamata ki je gida, kada a biyo sahu" dariya tayi sosai ta ce "lallai kam, kasan kuwa cewa Umma nayi zanje siyo biscuit" Sani yace "laaa, ai kuwa muje na siyi biscuit dan kada ta ji kun daɗe kuma ki koma ba biscuit hannu na dukan cinya" Dariya Zeenart tayi tace "amman wallahi kana da ban dariya sosai" Sani yace "tashi mu tafi" miƙewa Zeenart tayi sai da suka bi shagon Ali, Sani ya siya mata biscuit na ɗari biyar sannan ya rakata layin gidansu, kamar dai kullum sai da ta shiga gida sannan ya tafi gida.* * *
Kwance take akan makeken gadon ɗakinta, hannunta riƙe da wayarta tana chatting da Suleiman, voice note yayi mata yake faɗa mata cewar yanzu zai zo gidan, zata rakashi yayi shopping, ta bashi amsa da to, ta kashe data, ta shiga toilet dan tayi wanka, tana fitowa daga wanka ta ɗauki wata baƙar after dress, ta sakata ta yafa mayafinta, gaban mirror ta nufa tana kallon kanta "ba sai na shafa wata powder ba, a haka zanyi tafiyata, dan ko ba kwalliya ina da kyauna" tayi maganar a fili tana wani fari da ido (mu kuwa Aminan juna mu ka ce , Mehreen ki daina yabon kanki ki bari wani ya faɗa miki) Knocking ɗin ƙofar ɗakin ta ji ana yi, "yes come in" Tayi maganar cikin yanayin iyayi, Suleiman ne ya shigo da sallama a bakinsa, ƙura mata ido yayi yace "My kinyi matuƙar kyau, kin ganki kuwa" Dariya tayi tace "Thank you brother" Tayi maganar tare da ɗaukar glass ta saka, tace "can we go?" Suleiman ya gyaɗa mata kai alamar eh, tayi gaba yana biye da ita a baya, Mateen da Lareesa a falo suna kallo, ɗagowa Mateen yayi yana dariya yace "wai wa ya ga kwaɗo da glass" yayi maganar yana kallon Mehreen, Lareesa ma dariyar tayi jin abinda Yayannata ya faɗawa Mehreen, Suleiman yace "wallahi Babban yaya zamu saka ƙafar wando ɗaya da kai" Hawaye Mehreen ta shiga yi tare da cire glass ɗin ta wurgar, Suleiman yace "haba ƴar beauty, karki ɓata fuskarki da hawaye kiyi shuru" Mehreen tace "Yaya Suleiman kaji abinda yace min wai ni ce kwaɗo da glass" Tayi maganar tana kuka, Suleiman yace "kin fi shi kyau ne, shiyasa yake baƙin ciki"*ANAN ZAMU DASA AYA,*
*#SHARE*
*NASMA & DIJARTY*
_(AMINAN JUNA💃🏼)_