*A CIKIN IDO...*
_Ake tsawurya_
_Wattpad @SaNaz_deeyah_
*_Heart touching love story🥰_*
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amula tagari]__Na sadaukar da littafin nan gaba ɗayanshi ga BEEBAH LUV Allah yayi mata rahama ya kuma kai haske kabarinta Amin.🙏_
*Ko wane ɗan kasuwa yana da burin ace yau ya tara customers, wanda za su riƙa sayan kayanshi a koda yaushe. Kuma ko wane ɗan kasuwa zai so ace ya ƙawata sana'arsa.*
*Shiyasa muka shirya tsaf domin kawo muku abubuwan da zasu jawo muku customers ta ko ina, ta hanyar amfani da kuɗi ƙalilan domin a miki ƙayatacciyar Flyer Logo ko Sticker da zata ƙawata ta kuma tallata kasuwancinki. Har ma da I.V na biki da kuma Cartoon Advert muna yinsa cikin farashi mai sauƙin gaske.*
_*Abubuwan da mukeyi sun haɗa da:-*_
1- Special Flyer ₦1000
2- Flyer ₦500
3- LOGO ₦500
4- Wooden Mockup ₦600
5- Invitation Card ₦500
6- Business Sticker ₦200
7- Book Cover ₦200, ₦300 it defend
8- Menu ₦600
9- Transparent Logo ₦300
10- Cartoon Advert ₦3000
*Sannan abubuwan nan gaba ɗaya zamu koyar dasu ga masu buƙata akan farashin ₦3000 har na tsawon sati guda, amma banda cartoon Advert shi zamu koyar dashi ne akan farashi ₦5000 ga masu buƙata.*
Ku tuntuɓi wannan _number 07035111671__Shafi Na Biyu_
_____________Yana driving ita kuma ta kafeshi da idanunta, ko ƙiftawa bata yi.
_Ta ko ina ka haɗu Maheer, kyau, gayu, aji, da kuma kyakykyawar kamala, ina sonka Maheer amma na lura ba ta ni kake ba, zuciyata na sonka amma kai zuciyarka na ga wata, Maheer dan Allah ka fahimci saƙon zuciya, ka kalli ƙwayar idona za ka fahimci saƙonta._ Jin an dafa kafaɗarta ne ya saka tayi saurin dawowa cikin hayyacinta."Beautyn-beauty tunanin me kike haka?"
Ɗan ƙirƙiro murmushi tayi sannan ta ce "Ba komai, kawai dai..." Sai kuma tayi shiru.
"Ko dai ya ce zai zo ni kuma na ɗaukoki?"
"Wa kenan?" Ta tambaya tana kallonsa.
"Na ƙarfen mana, Allah yasa ba cewa yayi zai zo ba"
"Kaga nifa ban son zolaya" Ta ƙarasa maganar tana turo baki.
"Am so sorry ba zan sake ba, nima ana yi min shagwaɓar nan ina ga..." Sai kuma yayi shiru ya guntse dariya yana fita daga mota.
"Ai da ka ƙarasa ko?"
"Ni a suwa."Tare suka jera har cikin restaurant ɗin, sai da suka samu seat da ya yi musu sannan suka zauna.
Service ne yazo ya tambayi abinda za a kawo musu."Coffee and Chips" Maheer ya furta sannan ya kalleta ya ce "And you?"
"Ayi min takeaway na masa ya isa, ba zanci anan ba"
"Oh! Sorry" Ya furta sannan ya kalli Waiter ɗin ya ce "Ka kawo mata abinda za ka kawo min, Then ka saka masa ta 2k sannan ka saka 2plates of chips duka takeaway namu kuma ka kawo yanzu."
Yana tafiya ta kalleshi, za tayi magana kenan wayarshi ta fara ringing, kallon wayar ya yi yana murmushi ya kalleta ya ce "Mubina ce..."
Ɗan murmushin yaƙe tayi ba tare da ta ce komai ba, shi kuma ya ɗaga wayar.
"Babe...!" Ya faɗa yana murmushi idanunsa akan Amal.
"Oh am so sorry Babe kin ga Beauty ce ta riƙe ni, amma anjima zamuzo da yamma"
"Amal mana." Murmushi ya yi sannan ya ce "Babe rigima, to yanzu dai ayi min afuwa, idan munzo zamu ƙara bayar da haƙuri."
"Okay take care of your self"
"Bye-bye." Bata jin maganar Mubina ɗin, sai amsoshin da yake bayarwa.Yana gama wayar ya kalleta "Ya naga baki fara cin komai ba?" Ya furta yana kai duba da kan table ɗin da aka dire abubuwan da sukayi order.
Murmushin yaƙe kawai take, a haka suka fara cin abubuwan ba tare da wani ya sake cewa komai ba.
YOU ARE READING
A CIKIN IDO...(Paid Book💰)
Historical FictionTa kasance budurwa mai matsakaicin shekaru, a dalilin so ta ɗauki kasadar da har ta mutu ba zata taɓa daina dana sani ba. Bata taɓa aure ba, bata taɓa zina ba, ba kuma a taɓa yi mata fyaɗe ba, amma ta ɗauki ciki. Duk wani buri da take son cikawa ta...