Episode 1

6 0 0
                                    

    👀 IDON BAKAR MAGE A DUHU👀

*Daga Kundin ✍️📚✍️*
*Alkhamis KSA*
Wattpad: @KhamisSulaiman
Whatsapp: +2348095933008

Bismillahir rahamanir rahim wa sallallahu allan nabiyyil karim wa ahlihi wa sahbihi wa sallam.

Dukkan godiya ta tabbata gun Allah sarki guda daya mai kowa mai komai, tsira da aminci su kara tabbata ga Shugabanmu masoyinmu Annabi Muhammad SAW da ahalin gidansa da sahabbansa.

Ni Muhammad Khamis Sulaiman Abdullahi wanda ku kafi sani da suna Alkhamis KSA, ina gabatar muku da wannan littafin mai suna IDON BAKAR MAGE A DUHU ban yishi don cin zarafi ga kowa ba, kuma ban yarda wani ya daukar min littafi ko ya juya min shi ta kowacce irin hanya ba Sai da izinina. Na gode.

                        

                        *page 1*

                 

                   BIRNIN KANO
A karni na goma sha takwas kasar kano tana daga yankin tsakiya na arewacin kasar hausa, daga gabas tayi iyaka da kasashen borno da bauci, daga kudu tayi iyaka da kasar
zariya, daga yamma tayi iyaka da kasar katsina, daga arewa kuma tayi iyaka da kasar neja.

     A wannan karni na goma sha takwas anan kasar hausa cikin birnin kano, an taba yin wani mutum mai suna Dauda, yana da mata guda kuma Dauda talaka ne sosai amma Allah ya azurtashi da haihuwar 'ya kyakkyawa mai tsananin kyau da kwarjini ga Ilimi ga tarbiyya ga ladabi da biyayya ga bin iyaye da girmama na gaba sannan akwai ta da kunya, gaskiya, hakuri, da kuma hankali. Sunanta Fatima fara ce mai dogon hanci ga dara daran idanu akwai fari ya kewaye baki da wani dan kore kore kadan a tsakiya duk a cikin idon nata, tana da baki madaidaici Idan ta bude shi sai kaga fararen hakoranta sun bayyana a fili suna sheki, gashin kanta baki ne sidik. Shekarun Fatima ba zasu gaza ko dara goma sha shida ba.
      
       Fatima ta kasance tana da masoya sama da guda ashirin kuma duk suna sonta da aure, kullum cikin fadace fadace suke da doke doke da jefe jefe da asirce asirce. Da Dauda yaga abin yayi yawa haka sai ransa ya baci hankalinsa ya tashi ganin akan 'yarsa ake yin wadannan muggan aiyuka gashi har wasu cikin mutane sun fara zundensa wasu na ganin baikensa. Sai Dauda ya tambayi Fatima wanda take so cikin wadannan samari, a sa'in kuwa suna zaune shi da ita da babarta.
    
      Dauda yace "Ina son in tambayeki Fatima, shin wai cikin wadannan samari naki guda kusan ashirin da uku wa kike so ki aura?"
    
      To duk cikin samarin nata daga 'ya'yan sarakuna sai 'ya'yan masu mulki sai kuma 'ya'yan attajirai saurayi daya ne dan talatawa ana ce masa Imam.
   
        A sa'in da Dauda ya tambayi Fatima, sai ta ka sa fada masa sai da matsa mata sannan ta sanar dashi cewa "Aini Baba, Imam nake so duk duniyar nan kuma nayi masa alkawarin ba zan auri da namiji ba in ba shi ba, kuma nayi wannan alkawari ne saboda shi Imam mutum ne mai kyau da kyan hali, kuma shine dai dai dani babu karya babu wani buri da son duniya shi dan talakawa nima haka, su kuwa sauran samarin kyawuna ne yake rudarsu don da ba don shi ba da babu mai ko kallona cikinsu haka zasu ce ba matsayinmu daya ba. Don haka naji na gani ba wanda zan aura naji dadin zama dashi in ba Imam ba." gaba daya ma ta manta da cewa a gaban iyayenta take ta ke ta zuba kamar 'ya'yan kanya.
      
       Sai babarta mai suna Harira tayi farat tace "Ka ji mu da maras kunyar yarinya, a gaban namu kike fadin haka?"
     
           Sai Dauda yace "A'a ba rashin kunya ba ce ai wannan fadin gaskiyar, abinda yake cikin zuciyarta ta fada ta amayar abinda ke cikin cikinta, kuma nima abinda yasa na tambayeta wanda take so, saboda in raba rigimar da take tsakanin wadannan samari ne"
      
        Yayi shiru na dan wasu dakiku sannan yayi ajiyar zuciya hade da gwauron numfashi yace "To ga wani hanzari ba gudu ba, lallai idan na fito fili na gayawa duniya zan aurawa Imam 'yata Fatima, to bani ba kwanciyar hankali domin cikin samarin nan sai an sami wanda zai kasheni ko a jefeni ko a kashe 'yar ko shi Imam din!"
    
       Fatima tayi farat tace "Haba Baba ka daina wannan zance ai ba abin fada bane da n har za'ayi mana asiri ko jifa!"
    
        Dauda yayi murmushi yace "Har yanzu akwai alamun kuruciya a tare dake, kuma kina da mantuwa ko kuma rashin wayo ne oho! amma bari fada miki, in Za ki iya tunawa Rakiya diyar malam Buba da ta auri wani saurayi taki aurar wasu, har gidanta na aure aka je aka kasheta. Kuma Maimunatu diyar malam Sambo da samari suke ta fada akanta ubanta ya bawa wani saurayi ita, ai kinga kashe saurayin aka yi. Ga kuma Basira diyar sallau ai kinga saceta aka yi aka kuma yiwa ubanta kurciya har  yanzu ba wanda ya san inda dukansu suke. Kinga wannan ya isa kiyi tunani akan naki al'amarin, ance idan gemun dan'uwanka ya kama da wuta sai ka shafawa naka ruwa, kuma ai gani ga wane ma ya ishi wane tsoron Allah!"
     
          Harira tace "Gaskiya bata da wayo a lokacin da aka yi wannan masifa. Amma wannan magana gaskiya ce ba wai, yanzu meye abinyi?"
     
        Dauda yace "A'a ba komai, zanyi tunanin abinyi in Allah ya yarda zamu samu mafita!"
     
       Fatima cikin yanayin sanyin jiki tace "Amin summa Amin Allah yasa mufi karfin duk wani makiyinmu!"
     
       Dauda yace "Ai dama masu iya magana sunce, da sannu makiyinka zai zama masoyinka kuma da sannu masoyinka zai koma makiyinka"
    
       Yayi shiru na 'yan wasu dakiku yaga basu ce komai ba, sai yace "Ku tashi ku tafi gurin aikin da kuke"
    
        Sai suka tashi suka tafi duk jikinsu yayi sanyi gwiwowinsu duk sun kwale.
    
      Da maraice bayan anyi sallar la'asar kadan sai ga Imam yazo kofar gidansu Fatima ya sami wani yaro ya aikashi ya kirawo ta jim kadan ta fito sanye da riga da zani da kallabi duk na atamfa sannan kuma ga mayafi tasa, tana fitowa ta tsuguna har kasa ta gaishe da Imam bayan sun gaisa.
     
          Imam yace "Da fatan dai baki yi fushi dani ba domin na kwana biyu ban zo ba"
    
          Fatima tayi murmushi tace "Ai masoya in har sun amsa sunansu na masoya daya baya fushi da daya koda me dayan yayi"
    
       Imam yace "Ai nima na san da haka saboda irin sounds nake yi miki ya kasaita a cikin birnin zuciyata."
     
       Fatima tayi murmushi wanda ya bayyana fararen hakoranta tace "Ai soyayyar da nake yi maka tafi wadda kake yi min."
    
         Imam yace "A'a! kin shiga zuciyata kinga irin son da nake yi miki ne?"
    
        Fatima tace "Nima ai baka shiga zuciyata kaga irin sonka da yake a ciki ba."

Suka kwashe da dariya baki daya.
    
Fatima tace "Dama da baka zo ba ni zan aika a kira min kai."
    
     Imam yace "Amma dai lafiya ko?"
    
     Fatima tace "Lafiya kalau"

     Ta fada masa duk yadda suka yi da mahaifinta, a sa'ilin data gama gaya masa abinda ya faru, sai ta ganshi yayi kasake alamun ya shiga kogin tunani.
     
      Sai Fatima ta katse masa tunanin da cewa "Lafiya kake kuwa?"
     
     Sai Imam yace "Lafiyata kalau! wannan maganar da kika fada mini ce ta sosa min zuciya, lallai Baba yayi tunani mai kyau kuma maganar gaskiya ce! to amma meye mafita?"
     
       Fatima tace "Nima sai dana tambayeshi amma yace min zai yi tunani"
      
       Imam tace "Me zai hana yaje gurin Baba na kowa ya nemi tunda Allah ya bashi basira zai iya taimaka mana"
     
       Fatima tace "To shikenan zan fada masa Allah yasa ya yarda"
     
Imam

        Imam shima kyakkyawa ne kuma farar fata yana da doguwar fuska da siririn hanci da kananan idanu gashin kansa kwantacce ne kuma baki sidik yana da dan karamin saje akwai alamun jarumta a tare dashi.

      Mahaifiyar su Imam bafulatana ce shi kuma mahaifinsu balarabe ne, su hadu sunyi aure ne a yawon fataucin da uban yake yi, wannan dalili shi yasa su Imam suke da matukar kyan halitta da farar fata don idan ba magana suka yi ba ka ji ba zaka taba cewa suna jin hausa ba. Mahaifin su Imam babu yaren wata kabila da bai iya ba a duniya, kuma wannan ya samu ne saboda fataucin da yake yi tun yana matashi.

       Imam yaro ne mai ilimi yana da hazaka da basira baya raina hanyar sani komai kankantarta kuma ko a gurin waye, saboda haka nasarar koyon wasu yaruka a wajen mahaifin su irin su hausa, fulatanci, larabci, turanci, hindanci wanda a yanzu ake kira da indiyanci, da kuma sinanci wato mandarin, da dai sauransu.

Mahaifinsu ya dade da mutuwa a yanzu Imam yana tare da mahaifiyarsa da kannensa biyu Aisha da Aminu.

     Suna nan tsaye sai yaji Fatima tayi shiru alamun jikinta yayi sanyi, sai yace "Ni kuma nayi miki alkawarin ba zan taba aurar wata 'ya mace ba face ke"

     Suka yi ta hirarsu cikin nishadi da annushuwa har zuwa magariba sannan suka yi sallama da zai wuce ya kawo kudi ya bata amma taki karba yayi yayi da ita akan ta karba amma taki, sai ya tambayeta ko meye ya hanata karba.
     
       Fatima tace "Ni fa tsakanina da Allah nake sonka ba wai don kudi ba"
     
       Imam yayi dariya yace "To ina ma abin yake, nima nasan ba don kudi kike sona, da kuwa don sune bani za ki so ba sai dai ki so 'ya'yan attajirai ko 'ya'yan basarakai. Shikenan sai na kara dawowa" ta shige gida shi kuma ya kama gabansa.

Kada ku manta da:
>Like
>Share
>Follow
>Comments

                       📖.............✍️
                   *Alkhamis KSA*

  IDON BAKAR MAGE A DUHU Where stories live. Discover now