Episode 2

2 1 0
                                    

    👀IDON BADAR MAGE A DUHU👀

*Daga Kundin ✍️📚✍️*
*Alkhamis KSA*
Wattpad: @KhamisSulaiman
Whatsapp: +2348095933008

                           *page 2*

      Da daddare bayan sun gama cin abinci sai Fatima tace da mahaifin Dauda "Baba me zai hana baza kaje gurin Baba na kowa ba akan wannan maganar ta dazu ina ganin zai iya taimaka mana da wani abun"

       Dauda yayi shiru bai ce komai ba, sai can kuma sannan yace "Nayi tunanin hakan da, sai kuma na watsar, amma tunda kin ce haka gobe in Allah ya yarda zan je gurinsa"

     Kashegari kuwa da hantsi sai Dauda ya tashi ya nufi gidan Baba na kowa.

Baba na kowa

Shi dai Baba na kowa wani dattijon arziki ne wanda duk garin ana ganin girmansa kuma ana mutunta shi saboda fadar gaskiyarsa da kamalarsa da kuma taimakon mutane da hikimomi da Allah ya bashi, duk wanda yake cikin wata matsala yaje wajensa yakan bawa mutum shawara kuma in har mutum yabi shawararsa akan dace, idan kuma abu na nasiha ne yakan yiwa mutum, kuma shi kowa nasa ne talaka da mai attajiri da basarake, kuma babu wanda baya zuwa wajensa neman shawara, kuma duk cikin su babu wanda baya nuna kuskurensa matukar yayi kuskuren. Shi yasa ma ake masa lakabi da Baba na kowa.

     Da Dauda yaje gurin Baba na kowa ya sanar abinda ke tafe dashi ya gaya masa matsalarsa. Sai Baba na kowa yayi shiru yana tunani sai can kuma yace "Kayi tunani mai kyau kuma mai amfani, amma kana ganin idan na baka shawara ka yarda su samarin zasu yarda kuwa?"

      Dauda yace "Eh in wasu ma basu amince ba wasu zasu amince kuma duk wanda bai yarda ba sai na koreshi na hanashi zuwa kwata kwata wajen 'yata"

      Baba na kowa ya jinjina kai yace "To amma kada abinda ake gudu ya auku kaga anki cin biri anci dila kenan!"

      Dauda yace "Ai da yardar Allah ma haka ba zata faru ba!"

     Baba na kowa yace "Allah yasa haka, kuma Allah ya kiyashe mu da mugun ji da mugun gani"

      Dauda yace "Amin, duk shawarar daka bani haka zan gaya musu ba tare dana sauya koda wasali ba"

     Baba na kowa yace "To shikenan, dama ba wata shawara bace zan baka ta daban, ina so ka tara duk samarin diyarka, kace za'ayi gasa kuma sai wanda yaci gasar ne kadai zai auri 'yarda, idan sun zo kace musu kana so duk su tafi birnin sin suje tsuburin mongoliya su debo ruwan dake kan tsuburin, duk wanda ya samu nasarar debo wannan ruwa kuma ya dawo a cikin shekara biyar to shi zai auri Fatima"

      Dauda yace "To idan dukkansu suka samu nasarar debo ruwan fa?"

     Baba na kowa yayi murmushi yace "Kana ma tunanin zasu yarda suje kenan da har kake fadin haka? kama taba jin labarin tsuburin mongoliya kuwa?"

     Dauda ya girgiza kai yana kallon Baba na kowa.

      Baba na kowa yace "Kaje ka fara tarasu ka gaya musu nan da kwana uku zaka zo ka gaya min abinda suka ce maka"

      Dauda yayi shiru yana tunani daga bisani kuma yace "To har da Imam din za'a tafi ko kuwa babu shi?"

      Baba na kowa yace "Eh mana har shi, ai in kace babu shi to zasu zaci zakayi musu shigo shigo ba zurfi ne"

      Dauda yayi zugum kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwa, can kuma ya kalli Baba na kowa, yace "To yanzu meye abinyi?"

     Baba na kowa yace "Abin yin kenan kawai su tafi tare, idan fa sun amince kenan"

     Dauda cikin yanayin sanyin jiki yace "To shikenan na gode"

     Baba na kowa yace "Wannan shine kwanciyar hankalinka"

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Apr 01, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

  IDON BAKAR MAGE A DUHU Where stories live. Discover now