39

699 23 0
                                    

Jama'a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=

Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI

EPISODE 3️⃣9️⃣


Murmushi kowa na dakin yayi mata duk suka amsa suna mata yajiki ahankali ta amsa feeling so uncomfortable tarasa maisa kowa ke kallonta, zuwa Gwaggo tayi kusada ita tazauna tana mika mata cup dake cike da fura tace "ga huran ki to" makema Gwaggo kafada tayi tana turobaki dan haushin ta takeji sosai datasata taje ta kwana dakin Abee murya chan kasan makoshi kaman munafuka dan batason wani yajisu tace "bara'a shaba din" ta harareta tareda juyarda idanunta karaf suka hada idanu da Abee da idanunshi ke kanta hannunshi rikeda cup na furan, wani kalan kunya taji dasauri tasauke kanta kasa, Gwaggo tace "to mekikeso nafa miki har farfesu iyyee Lulu wai mesa aduniyan nan da tsufa na idan baki bani wahala ba bakijin dadi ni kadai ne me jika aduniyan nan jibi Hajiya dan Allah bulbul da ita bata komi saidai amata amman nida nama fita tsufa nine kema jikata aiki, Allah ma zuciyata yagani yabani karfi izuwa yau ban gurgunce ba" kowa na falon danne dariyanshi yake Musty ne yace "Lujain mezakici to"? Dan dagokanta tayi tadan kalleshi saikuma takalli Gwaggo dukdan ta kule Gwaggo tace "tuwoo" baki Gwaggo takama tace "wlh karya take babu abinda Lula ta tsana kaman tuwo wahalar dani kawai takeson yi" for the first time dan murmushin mugunta Lujain tasaki murya chan kasa irin ta marasa gaskiya tace "ni kitashi kimin" tai maganan tana juyarda kanta gefe still tana murmushin muguntan karaf tasake hada idanu da Abee dake mata wani mugun kallo dasauri tadauke kanta Hajiya tace "Lujain zakici tuwo da gaske idan zakici saikuje kitchen dake da Kausar dakuma Maman Aneesarh ta nunnuna muku komi kuyi kidaina wahalar da kakanki babu kyau kinji" ahankali ta gyadama Hajiya kai, murmushi Hajiya tayi tace "zakici tuwon ne da gaske"? Girgiza mata kai tayi tace "a'a tea zansha" yanda tai maganan kaman ka cinyeta it was so sweet, Hajiya tace "tafi dinning Kihada tea kisha tea ki kinji" gyadamata kai tayi tamike tsaye ahankali tawuce feet nata Abee yabi da kallo kaman jini zasu fito wani iri yaji yanda kowa ke ganin kafan nata zai dinga sata tana saka safa, zama tayi a dinning tahada tea awani big cup tafara sha abinta sukuma yan falon sai hira suke, kowa na falon yay mamakin yanda Abee yazauna yanajin hiran dudda baya cewa komi but zaman kadai dayayi zai nunamaka yanajin dadin hiran.

Saida tagama shan tea danshi tasha sosai bataci egg da chips ba sabida yanda cikinta ya cushe, kitchen tawuce ta wanke cup datai amfani dashi ta ijiye sannan tafito tawuce sama tana tafiya ahankali tana kama karfen bene dan cikinta yafara ciwo daga cin abinci, tana shiga dakinta Hijabin tacire ta ijiye kan gado tareda tsugunnawa anan kasa tadaura kanta saman gado tarike maranta kaman wacce ke nakuda, jin cikin yafara usulin ciwo kaman zai kasheta yasa ahankali tafara. "Wayyoooo cikina Gwaggoooo" saikuma tafashe da kuka ahankali ko kadan batada dauriyan ciwo tun tana yarinyar kodan sabida yanda ko bigewa tayi Gwaggo tadinga riritata kenan yasa oho amman dai batada dauriya ko kadan.

Bude kofan dakinta akai ahankali hakan yasa dasauri tadago kanta tareda juyowa takalli kofan da rinannun idanunta Abee ne yana tsaye jikin kofan yazuba hannunshi a aljihu yana kallonta, kokarin mikewa tsaye tayi ahankali tana dafa jikin gado ahankali sannan tajuyo tadan kalleshi tana yarfe hannu, anatse yace "kinsha maganin ki?" Girgizamai kai tayi ahankali tana goge fuskanta da bayan hannunta, anatse yace "dauko maganin kizo nan" gyadamai kai tayi tajuya ahankali tafara tafiya dan magungunan nakan mirror, wani kalan dauke kai Abee yayi daga kallonta dayakeyi, daukan ledan maganin tayi tajuyo ahankali tazo dan nesadashi ta tsaya tareda mikamai ledan sai alokacin yajuyo ledan yasa hannu Ya karba batare daya kalli fuskanta ba yace "ba'ashan magani da ruwa ko" dasauri tajuya wani bottle water na sabo tadauko tajuyo tadawo tasake tsayawa nesa dashi, dago idanunshi yayi yazubamata hakan yasa dasauri hannunta har rawa yake tashiga kokarin bude goran ruwan amman takasa dan ba karfi, hannunshi yamika mata alamun tabashi hakan yasa ta mikamai goran da sauri karba yayi murdawa daya yabude mata goran sannan yabata karba tayi ahankali takurbi ruwan magungunan daya ballo yabata a hannu kaman zatai kuka babu yanda ta iya ta watsa maganin bakinta tahadiye tana tabe fuska takai ruwan bakinta tashiga kwalkwala kusan rabin goran tasha sannan tasauke goran mika mata ledan magungunan yayi ahankali tasa hannu ta amsa yajuya saikuma ya tsaya chak batare daya juyowaba hakan yasa ta kalleshi, anatse yace "stop wearing irin rigunan nan agidana!" Yana maganan yawuce turo baki tayi tareda maida kofan tarufe murya chan kasa tace "nima kayan gabaki daya sun isheni" tai maganan tana komawa gado kwanciya tayi tana juye juye dan cikin ciwo yake mata ahankali yafara lafamata ahaka bacci yay awon gaba da ita.

Wuraren 1 tafarka ita kanta har mamakin baccin datakeyi take, Gwaggo tagani adakin tana karkada magunguna ganin ta tashi zaune yasa Gwaggo ta washe baki tace "sauko kizo kigani Lulu nadafa miki kaza da tantabara" hararan Gwaggo tayi tawuce ta tafi bayi, Gwaggo tace "wai baraki daina fushi dani ba Iyyee Lulu sabida namiki Auren gata, jibi yanda yan uwan mijinki keji dani, kinsan nawa abokanenshi suka bani, dukansu dubu Hansin Hansin fa, Mujittafa Hamsin, Haruna Hansin, saikuma dan sandan nan Abdul hansin, ai wlh kinyi saa kinzo katon gida ga jama'a aciki kuma kowa na sonki ni Allah ma makirin dan iskan nan daya batamuku suna Albarka dan abinda yayi yazame miki alkhairi" tana maganan wayanta yashiga ringing wayan ta kalla tace "ai nasan ubanki ne kome zakayi baran dawo gidanka gidan wahala ba, dana dinga rokonka ka kaini ka kaini ne ina ba saida nakira surukina ba da Allah yabani number shi da kyar ba oho saikuma kayi" tana maganan ta ijiye wayan tacigaba da abinda takeyi, fitowa Lujain tayi daure da towel taje gaban wardrobe nata ta shirya tsaf takara komawa bayi ta ijiye wannan towel din tadauko sabo blue ta daura tazo tazauna kusada Gwaggo data ijiyemata kula agabanta, bude kulan tayi tana turobaki sanan tashiga cin naman Kazan dana tantabara da Gwaggo tamata farfesu dudda farfesun magani ne amman bala'in dadi, tass ta cinye ta ijiye kasusuwa koba komi tayi kewan Gwaggon ta wani ruwa Gwaggo tabata na sayuwa tace "sha wannan babu daci ko kadan kaman ruwa ne" dandanawa tayi jin babu daci yasa ta shanye tace "Gwaggo me shi"? Wani Leda Gwaggo ta ijiye tace "ba'a fadima yara meshi, anjima zakisha wayan nan su Abida sunce na gaisheki "  wani kalan murmushi tayi tace "Gwaggo ai tare zamu koma ko"? Dan kallonta Gwaggo tayi saikuma tai kaman bataji ba, Ahankali Lujain tace "Gwaggo bana iya bacci agidan nan, ban sansu ba, bansaba dasu ba, Gwaggo kuraba auren Mandawari zai aureni" wani kalan dakuwa Gwaggo tamata tace "wlh idan kina kiramini sunan wani namiji kina matan aure saina makeki Lulu" kaman Lujain zatai kuka tace "toni nagaya muku ina sonshi ne, ni wlh Mandawari na nakes........" empty farantin roban gaban Gwaggo data gama kwashe magungunan ciki ta dauka ta rapka mata akai tace "rufamini baki" wani kalan ihu Lujain tayi gabaki dayama ta manta ba a gidansu takeba dan haka take agida idan Gwaggo ta bugeta Aiko ranan tashiga uku saita lallasheta da kyar sannan zatai shiru, wani kalan mikewa tsaye tayi da towel din tana kuka sosai amugun shagwabe tabude kofan dakin tafita Gwaggo data bitada idanu tace "aisai kiyi fitsararriya" daidai tana fitowa tana kukan ta kama kanta da Gwaggo tabugama plate daidai Abee nashigowa saman ita ko kadan batama luradashi ba, tundagakai zuwa kafa yabita da kallo yadan tsaya yay jim kaman yajuya yakoma falo saikuma yacigaba da tahowa ko kadan bataji sahun takalminshi ba as usual kamshin turarenshi kadai yagayamata yana wajen hadiye kukan tayi tass sannan tadago kanta kaman munafuka tana sauke hannayen kasa, hada idanu sukayi dawani kalan sauri tajuya zata bude kofan dakin tashiga yace "come here" dawowa tayi ahankali kanta akasa tashiga wasa da yatsunta dan she's so restless, "what happen"? Taji Abee yamata tambayan muryanshi ataushashe, dago kanta tayi takalleshi saikuma ta kwabe fuska kaman zatai kuka taredakai hannunta saman kanta inda Gwaggo tabugama plate tace "Gwaggo ne tadakeni tabugamin plate akai" kanda ta taba yabi da kallo ga wajen har datti datti na abinda ke plate din ke wajen, kaman baraiyi magana ba saikuma ashanyaye yace "what did you do tadakeki?".

SAKON SOWhere stories live. Discover now