11&12

7 1 0
                                    


*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

*11*

✍🏻Matar Rasheed

  Su SAFRAZ nabi Don ganin wace wainar suke toyawa.....

   A mota nagansu zaune SARFRAZ yayi parking a Gefen titi "haba malama! You should treat me like a brother....  Ace kina cikin damuwa ki'ki fadamin meke damunki?

   Aiya kamata ki fad'a min tundazu fa nake ta tambayarki....

   Murmushin ya'ke tayi "SARFRAZ tunda nace maka babu komai ya kamata ka yarda,  kawai dai banajin dadine.....

   "to shikenan in kaiki Rosario park?

"eh tace domin batason ta gwaleshi da yawa....
  
    Murmushin jin dad'i Yayi jin cewa ta amince "to mutafi kenan koh?

   "Eh Amma Don Allah kada mu dad'e domin inaso ka kaini gida saboda akwai kayan danakeso na dauko kuma bayannan wayarka da tawa....

  'bata fuska sarfraz yayi "haba sister nidai kibar zancen zuwa gidannan kawai....

   I promise you bazan dad'e ba....

   "aini ba dad'e warki bace damuwata, kawae Ina tsoro kada muguwarnan ta kara cutar dake ne..

    Murmushi tayi "haba aini nasan babu abinda zata iyamin balle gakama ☺

   Sarfraz  yaji wani dad'i aranshi ganin Nawaz tayi relying akanshi.....

   Reverse d'in motar yayi zuwa hanyar gidan su Nawaz...

    yan mintoci ne yakaisu, parking yayi "madam Mun iso 🥰

   Murmushi tayi "okay nagode bari na shiga yanzu zan fito In'sha Allah....  Sannan ta bud'e motar tafita zuwa zauren gidan.

    tsaye SARFRAZ yayi Amma sai yaji Sam zuciyarshi bata kwanta mishi akan ya barta ita kadai ta shiga ba ......

    bin bayanta Yayi, tsakar gidan ya kalla kopopi yagani guda Hudu kuma ya kasa gane waccece tasu Nawaz...
    Da bangon zauren ya jingina Yana Kallon ta inda Nawaz zata fito.....

    ita kuma Nawaz tana d'aki domin kopar dakin ma a bud'e ta ganta gashi duk anyi musu kaca kaca da wardrobe da drawer...

    Mamaki take to waye yayi haka, kuma me suke nema?

     Da sauri ta Duba inda ta ajiye wayar SARFRAZ,  ajiyar zuciya tayi domin tazata an dauke.

    Parcel d'in ta duba shima bataga an dauki komai a cikiba....

    tunani ta Fara domin ta rasa me aka dauka a d'akin...

   wayarta Ta nema Ta rasa, babu inda bata dubaba Amma babu ita babu ala munta....

    zama tayi a Gefen gado tana tunanin me kuma aka shirya mata dayasa aka daukar mata waya....

   SARFRAZ dake tsaye a jikin zaure,  umma ya gani ta fito daga wani d'aki Ta shiga wani....

   zancen zuci ya Fara "ko wannan ce ummar  to wane d'aki Ta shiga kuma?

   bin bayanta yayi domin Sam yaki samun natsuwa a cikin zuciyarshi...

   sama sama yake jiyo fad'a "wato Nawaz saboda mahaifiyarki batanan shine kika ƙi kwana a gida ko?
    Salon ki kwaso cikin Shege ace nice ban kula dakebako?

   "haba umma wai meyasa kullum Ke bakya ta'ba min Fatan Alkhairi ne?  Yanzu umma ninayi miki kama da yar iska?

    "kwarai kuwa kinyi domin, ko ba'a fad'a ba mutum yaji shekarunki kuma yaji bakiyi aureba sannan Bakida niyyar yi ai dole yasan Maza gareki a Waje ......

SARFRAZ Where stories live. Discover now