Dariya

209 14 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Ta gama shirin tafiya aiki, ta zuba duk abunda take bukata a jaka gudun kar abunda ya faru ranar friday ya sake maimaita kanshi.

Yau ma Abdulkareem ne yazo daukar ta duk da tace masa kar yazo amma se da ya zo din, kiranta yayi yace mata yana kofar estate dinsu. babu yadda ta ita ta sauko suka tafi.

farin cikin sa na daban ne don yau ne day 1 na shagalgulan Aniversary da aka tsara. Yau ne ranar da ma'aikata da special guest din da aka gayyata zasu zagaya manya manyan site din da company take aiki a kai. Abdulkareem ne a kan gaba wajen tsara tafiyar tunda shine head na building department.

Ya kasa dena satar kallon ta saboda yadda tayi kyau yau. Akwai ranar da khairi bazatayi masa kyau bane? sede wani ranar yafi na wani ranar. Atamfa ta saka gown me flittings, sannan ta saka boyfriend jacket me dogon hannu a saman atamfar saboda sanyi, ta yafa karamin mayafi a kanta wanda ya tsaya iya kafadunta.

"Ummulkhair"
Abdulkareem ya kira sunan ta a hankali da wani irin kasalattarcen murya me kashe jiki.

Duk yadda khairi ke dodging irin wannan yanayin se da taji yadda ya kira sunan ta ya tsarga cikin jikinta. A hankali kamar maganar baza ta fito ba tace

"Naam"

Dogon numfashi ya ja sannan yace

"Na dade ina son na samu courage din da zan iya fada miki wani sirri da na dade da boye miki, amma ina ganin lokaci yazo da zan fada miki"

"Menene"
Khairi ta tambaya fuskarta da alamun damuwa a ciki

"Kar ki damu zan fada miki anjima Insha Allah"
Ak ya bata ansa tare da kallon ta, itama kallon shi takeyi.

Akwai wani abu na musamman da yake attracting dinta zuwa gare shi, abu na farko shine nutsuwar shi, sannan tana jin dadin yadda yake mutunta ta.
Na biyu kuma yanayin cikar zatin sa na cikakken namiji. Na uku yadda yake da tsafta don ita tana da tsananin tsafta shiyasa take son ganin mutum me tsafta.
Kullum jikinsa fess fess motarsa tsabtsab ga kanshi da ke tashi ta ko ina

Bata taba tsayawa ta kare mishi kallo sosai ba se yau, me kyau ne, kyaun nashi daidai musali ba na tashin hankali ba. Gashi dogo wanda idan ta tsaya kusa da shi se ta ganta yar karama, duk da itama tana da tsahon amma bazata hada tsahon namiji da mace ba

Idon sa wani irin coolness yake emitting. Ido ne calm wanda ze iya sa ka bata a cikin sa, ya sa ka manta kanka a cikin sa.
Ta kula tun ranar da ya fara dawo da ita gida take yawan tuno shi a ranta. Tana tuno yadda yake kallon ta, tana tuno yadda idonsa yake kai sakon da ke sa ta shiga kokwanto

Ance baki yana iya karya amma ido baya taba iyawa. Tana gani so a kwance a idon sa, son da shi kansa be isa ya boye shi ba saboda bashi da control akai domin so baya buya.

Tunani me zurfi ta fada, ba yau ta fara ganin so a idon samarin da ta taba kulawa ba, amma na Ak na daban ne. Na Ak kogi ne wanda bashi da iyaka.

Da farko tayi tunanin nata assumption din ne amma maganar da yayi yanzu ya tabbatar da zargin da takeyi.

To idan ma yace yana son ta, ita son shi take yi?

"Baki bani ansa ba"
Muryar Ak ne ya katse mata tunani

"Naam??"
Ta tambaya da confusion a fuskar ta

Ak yayi dariya sannan yace
"baki ji me na ce ba kenan"

"Hmmmm eh to"
Khairi ta amsa tare da sa hannu tana murza ido saboda kunyar da ta ji

"Cewa nayi idan zamu tafi tour zanso mu tafi tare"

Da sauri ta dago kai suka hada ido
"Aa dan Allah, zanbi sauran ma'ikatan a bus din da aka tanada.

"Meyasa baza ki bini ba"

"Me yasa zan bika"
Khairi ta amsa tare da daga gira daya sama.
Kallonta yayi suka kara hada ido, da sauri dukkan su suka dauke idon su saboda spark da ya hadu

Shiru sukayi a motar babu wanda ya kara magana har suka isa company, kowa da abunda yake sakawa a cikin zuciyar sa. Khairi tana mutuwar son jin ansar da ze bata, shi kuwa Abdulkareem ya ainayo ansoshi sunfi dari a cikin kansa.

Yana yin parking khairi ta bude kofar motar sannan tace "na gode" ba tare da ta kalle shi ba ta fara kokarin fita daga motar

Kamar daga sama taji muryar Abdulkareem

"Because you are important to me"

Kunya ce ta kama ta kamar zata nutse .tayi sauri ta rufe masa kofa motar ta bar gurin da sauri harda dan tuntuben ta,

Zama yayi acikin motar ya kasa fitowa. ba karamin confidence da karfin hali ya tattaro ba har ya iya fada mata haka ba
Murmushi yayi sosai har se da hakoransa suka fito, ya dunkule hanun saya bubbuga a kan striring a hankali yana fadin "yess, yess" a fili, yana jin wani farin ciki na ratsa shi

Khairi kuwa shiga company tayi da sauri saboda kar Abdulkareem ya kamo ta Ta haura bene da gudu. Se da ta kai corridor din office dinsu inda babu kowa sannan ta tsaya ta saki wani murmushi me kayatarwa. Bakin ta ya kasa rufuwa se murmushi takeyi, Murmushi da yasa ta kasa gane takamammai meyasa abun da ya fada ze sa ta farin ciki haka

Da murmushi a fuskarta ta bude kofar office dinta da key, tana budewa taga mutum a kusa da desk dinta ya juya baya.

"Wayyo!!!"
"Ta saki kara saboda tsoron da taji, hankalin ta a tashe.

Umar ya juyo tare da hade rai sannan yace
"Mene haka"

"Me ka....ke...yi?"
Khairi ta tambaya a tsorace har tana i'ina.

Be bata ansa ba ya nufi dayar kofar da ta hada office dinshi da nata, ya barta a tsaye baki a wangale.

Da sauri ta bi bayan shi. har ya shiga office dinsa tana biye da shi a baya.

"Ya akayi ne"
Ya tambaya bayan ya zauna a kujera, saboda yadda yaga ta biyo shi kamar jela.

Takowa tayi har inda yake zaune sannan ta ajye masa paper bag me dan girma a kan table

"Menene wannan"
Ya tambaya yana yamutsa fuska shi a lallai boss

"Abayan da ka bani ne ranar"
Ta fada idon ta a kasa tana wasa da yatsun hannun ta saboda tsananin kunyar da take ji. Abun kunya kam tayi shi ranar friday

"Me zanyi da ita"
Ya kara tambaya da husky voice din da take tsoron taji yayi mata magana da shi"

"Kawai na dawo da shi ne"

"Ok sawa zanyi kenan"

Ainayo shi tayi a cikin ranta da abayar a jikinsa fuskar nan babu alaman rahma. dariya ne ya subuce mata tasa hannu ta rufe bakin ta. Yadda yayi maganar ba abun dariya bane, hasali ma fuskarsa a hade yayi maganar.

"Sorry sir"
Ta fada amma dariyar tana nan a cikin ta, da sauri ta fita ta koma office dinta ta ci gaba da dariyar.

Umar da ta bari a tsaye mamakin dariyar da takeyi yayi, wato yanzu ta raina shi sosai da har take masa dariya idan yayi magana kenan.
maimakon yaji haushin dariyar da tayi masa wani ikon Allah beji ba se ma murmushi da yayi sannan ya koma ya zauna.
Ko me ya sata dariya oho

🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763

SarkakiyaWhere stories live. Discover now