30

202 12 0
                                    

💧💧 *KUSKUREN SO.*

FREE BOOK

*HASKE WRITER'S ASSO.*

   *FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm

  _Ga ba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE, maman jinjiri, Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._

_Ina kike Aunty Zainab Abubakar Kotorkoshi? Ke ma ina maki fatan alheri._

*030*

Jikina ya soma rawa, yayin da hawaye ya fara sunturi a saman fuskata, hawayen farin cikin da na shafe wata biyu da ƙwanaki ba tare da sun fito daga idona ba, tsabar farin ciki ya saka na kasa ɗaukar wayar har sai da kiran ya katse, yayin da na ɗaura hannuna bisa baki na gudun kar na kurma ihun da zai janyo hankalin ƴan bakin cikina..

"Sufyan Fannata, Sufyan ne ya kira ni." Na faɗa cikin rawar murya har lokaci hawayen farin ciki bai daina fita daga idona ba, wallahi sai na ke jin tamkar an zunduma ni aljanna.

Ta taɓe baki tana faɗin "To sai me? Shine kike wannan rawar jikin sai ka ce wata tsiya ce a kiran na ki?"

Na zaro ido cike da mamaki ina tambayar "Bangane ba?"

"Eh, abin jin daɗi ne don ya kira ki bayan shafe wata biyu bai neme ki ba?"

Na girgiza kai tare da cije laɓɓana ina ƙoƙarin danne abinda na yi niyyar faɗa mata, kafin na bata amsa kiran na shi ya sake shigowa, na wani ja numfashi na sauke ina godiya ga Allah da ya karya asirin ba tare da taimakon wasu ba, na ɗauke hawayen da suka sake zubo min da babban yatsana, sannan na kanga wayar a kunne yayin da bugun zuciyata ya ƙaru linkin ba linkin.

Cikin muryar shi da ke ƙara rikita ni, da rura wutar ƙaunar shi a zuciyata ya kira sunana "Nafeesa....."

Na fashe da kuka mai ƙarfi hannuna na rawa, wata biyu fa kenan cikin ƙunci da kewar abinda zuciyata ke so, sai na ke jin tamkar na yi shekara dubu biyu ba tare da shi ba.

"Ko na kashe wayar idan kin gama kukan sai na ke kira..." Ya furta a kasalance.

Na hau girgiza kai, ni kaina na san yadda kuka na ke ɗaga mishi hankali, don ya sha faɗa min ƙara a ɗiga mishi dalma da ya ji sautin kukana.

Cikin shashshekar kuka na ce "Idan ban kuka ba me kake so na yi Sufyan? Sakina fa aka sa ka yi, sannan baka neme ni ba tsawon wata biyu, kullun cikin tsumayen ka nake, ina jiranka, babu kai Sufyan, idan na kira wayar ka baya shiga, na shiga tashin hankali, na shiga ƙunci, ya zan yi......

Kai tsaye ya ce" Duka laifin ki ne Nafeesa.."

"Laifina?"

Ya jijjiga kai, da alamu shima yana jin radaɗi fiye da ni, don wallahi ko ban ganshi ba, na san ba ƙaramar rama da baƙi ya yi ba.

"Me na yi?" Na furta jikina na rawa, don da alamu har yanzu asirin su na tasiri akan mijina

Ban yi tsammani ba sai tsinkayar shi na yi yana tambayar  "Me yasa ba ki kira mahaifiyata ba kin bata haƙuri akan abinda ya faru Nafeesa?

Kamar wacce ruwa ya cinye haka na yi difff da wayar a kunnena hannuna na rawa, Lallai sai yanzu na ƙara tabbatar da asiri aka na Sufyan wallahi, wai ni ce zan kira uwar shi na bata haƙuri? To wai ma uban me na mata?

"Wannan shine son da kike min Nafeesa? Shine alƙawarin da kika min zamu rayu mu mutu a tare? Shin baƙya tunanin halin da zan shiga idan  na rasa ki? Ba ki taɓa tunanin daga ribs ɗina aka halicce ki ba? Ba ki yi tunanin idan babu ke ba zan iya rayuwa ba? Why Nafeesa, me yasa kike azabtar da mu.?

Cikin rawar murya na kira sunan shi "Sufyan....

Ya katse ni "Bana son jin komai daga bakin ki Nafeesata, almost 2 month baƙya tare da ni, amma ba kiyi tunanin gyara kuskuren ki ba, am highly disapppointed on you wallahi, ki sani idan na mutu ke ce kika kashe ni..."

KUSKUREN SO Where stories live. Discover now