02

350 14 0
                                    

*GASHIN ƘUMA*

Na
© Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 2.

Bilal ya nufi bangaren masu aiki, ta can baya aka ware na masu aikin gidan, daki ciki ɗai ɗai ne a jere guda uku sai bayi a gefe mai hade bayan gida da wanka, yana isa sashin ya kwada sallama ba tare da ya buga kofa ko daya ba, dan bai san wanne ne dakin Musa mai wanki ba, saboda akwai dakin mai gyaran fulawa da sharan gidan da kuma na mai wanki sai kuma na drivern momy, ko wanne da dakinsa ba takura, Musa ne ya fito daga bayi alamun yayi alwala cikin sakin fuska yace.

Karamin Alhaji kai ne da kanka kazo nan bangaren, ai da ka aiko mun zo gareka dan cika bukatarka.

Karka damu, na zo wajenka ne ka ara mini kaya dan na san kana da tsafta, ka duba mini wanda suka ɗan koɗe, ka bani inna gama amfani dasu zan dawo maka damu.

Karamin Alhaji me zakayi da kayana? ai kafi karfinsu sai dai...

Bana son jayayya ka shiga ka fito mini da jakar kayanka na zaba.

Cewar bilal daya katseshi, da sauri Musa ya shiga dakinsa ya dauko gana mazgo dinsa ya dire a gaban Bilal.

Ai ko duka kace sunyi maka to ka tafi da su yallabai.

Bilal bai ce komai ba ya tsuguna ya bude jakar ya shiga duba kayan, abinda ya burgeshi har ya kwantar masa da hankali yadda yaji kayan suna kamshin turare duk da ya gane irin turaren nan ne mai arha, amma yaji natsuwar saka kayan dan Musa akwai tsafta, ya dibo riga shirt da wando jins wanda suka dan sha jiki amma fes suke, sai ya dauki wata shadda riga da wando wanda dinkinsa yake tazarce, duk da tadan yi haske amma yana da kyan gani, yana gama dibansu ya mike yayi gaba ba tare da yace komai ba, Musa ya bishi da kallo yana girgiza kai cike da mamakin wannan lamari, yasan dai da akwai abinda Bilal zai yi mai muhimmanci da yasa shi daukar kayansa, ajiyar zuciya ya sauke yana cewa.

Allah ya sa Alkhairi ne.

Sai ya dauki jakarsa ya mayar daki ya fito ya nufi masallaci. Bilal kuwa yana isa daki ya saka kananun kayan ya adana shaddar kana ya fesa turare a jikinsa sai ya dauko wani p-cap ya saka a akansa ya dauko key da wayarsa ya fito, alla alla yake kar wani ya ganshi, har ya fito falon bai yi karo da kowa ba sai da ya isa parking space ne yana kokarin shiga mota sai ga Yaya Abdul ya fito daga motarsa da shigowarsa kenan yayi parking, yana ganin Bilal yadda yayi wani shiga kamar bai da gaskiya ya sashi yin sauri ya isa wajensa yana dubansa, shima Bilal kallonsa yake fuska daure dan sam bai so ya ganshi ba, Abdul yace.

Yau kuma shaye shayen da kayi irin shigar daya saka kayi kenan? Ko kuma club dinku suka saka gasar saka kodaddun kaya saboda hauka. Ina fatan abinda ya sameka karya samu sauran dangi, Allah ya shiryeka.

Ameen, malam ban son sa ido babu ruwanka da rayuwata ehe, munafuki kawai na tabbatar kan na dawo ka fesawa su Momy dan halinka kenan gulma.

Cewar Bilal a hasale kana ya bude mota ya shiga tare da rufe motar da karfi kamar da shi yake fada, Abdul murmushi kawai yayi dan ya saba da halin Bilal duk da ya girme masa amma sam baya ganin girmansa saboda basa shiri, basa zama a inuwa guda dan halinsu ya bambanta, Abdul mutum ne mai hankali da natsuwa ga ilimi da sanin yakamata kuma shi mutum ne da bai da magana, sabanin Bilal da shi sam baida hakuri ga surutu da raina mutane, hasalima shaye shayensa yasa baya ganin kowa da gashi Abba da Momy ne kawai yake dagawa kafa, shi kuma Abdul baya taba ganin kuskuren Bilal yayi shuru dole sai ya tanka, shi kuma bilal sai ya rama tare da yi masa rashin kunya, haka suke zama tamkar annabi da kafiri sai kace ba jini daya suke ba.

GASHIN ƘUMAWhere stories live. Discover now