*ƳAR ME MAGANI*
*Story and writing*
*Oum Hairan**5-6*
Rike hannuta yayi ya jata suka zauna ya sanya hannu ya dauke mata hawayen fuskarta yace “Karki sanyawa zuciyarki damuwa abinda zai yuwu shi zaayi Hindu yau zan sanar da su Baba Mai gari abinda ke damuna Hindatu inasonki ne da aure kuma bana bukatar bata lokaci...."
Girgiza masa Kai taci gaba dayi tanaci gaba da matse hawayenta tace “Ka daina furtawa Yaya Ila inason kayi rayuwa me tsayi banason kaima ka shiga layin mazan da suka rasa rayuwarsu saboda sunyi yunkurin aurena"
Murmushi yayi ya mike yana tafiya yana cewa “ko zan rasa rayuwata na yarda na mutu dalilin soyayyarki karki damu ki shirya gobe da kaina zan kaiki makaranta saidai Ina neman alfarma daya"
Juyowa yayi dubeta duba na tsanaki yayi mata murmushi me sanya zuciya cikin nishadi yace “To be Me wife Hindatu inasonki tun kina zanin goyo" maganganu yaketa fada mata na soyayya kuma yaki Bata damar cewa komai shi kadai yake kidansa yake rawarsa ana Kiran magaruba Suka tafi gida wata kulawa me ratsa zuciya Ila yake Bata itama tanajin sakonsa a kasan ranta da haka Suka isa gida ya fita ya kawo mata shayi da bread hadin masu shayi yasha Madara harda wainar kwai bai jima ba ya shigo da abinci ya aje mata tana sallah ya fice koda ta isar batasha shayin ba abincin taci domin shi zai iya lalacewa bayan ta gama tayi alwala ta kwanta yau dinma dai batayi baccin kirki ba tanata tunanin yanda makoma zata samu a rayuwarta.Sama² bayan bacci ya dauketa taji kamar ana tabata ta bude idanunta a razane domin tariga ta sani ita kadai take rayuwa a gidansu to waye zai tabata? Zubawa gefen shimfidar tata idanu tayi duk da duhun dake mamaye da dakin bai hanata ganin hasken farin abun dake gaban shimfidar ba ta dauki fitila da sauri ta kunna bakinta dauke da addu'a cikin mugun tashin hankali da kaduwa hadi da kidima tayi tsalle gefe tana huci.
Ba komai ne ya sanyata wannan hucin ba sai ganin wata wata mace sanye cikin likkafani Babu abinda ake gani a jikinta sai fuskarta itama din hancinta toshe yake da auduga sannan idanunta a rufe yake Amma bakinta dauke yake da murmushi rawa sosai jikin Hindu yakeyi har tana sakin fitsari bakinta ta bude tace “Wacece ke me kikazoyi gurina?" Takowa matar ta rinkayi har ta kure gudun Hindu ta sunkuya daidai fuskarta tace “Yarinya banzo don cutarwa gareki ba duk da nasan baki sanni ba nima bansanki ba ubangiji na ya bani ikon zuwa na isar da sako gareki karki auri Ila shi ba mijinki bane mijinki zai dawo gareki bada dadewa ba Amma bazai bayyana ba sai abubuwa sun lalace rayuwarki ta kara kuntata kinji dama kece mu da muka mutu muka bar muku duniyarku muke rayuwa a barzahu.....
Firgigit ta zabura ta Mike daga wannan mummunan mafarki tana salati tare da karanto duk addu'ar da tazo bakinta tana me laluben fitila domin ta kunna daidai lokacin data kunna daidai lokacin da taji kukan wani tauntsu dake firgita duniyarta ya fara rerawa cikin kukan nasa ta dade da fahimtar sunanta yana fita cikin sautinsa har Baba Mal tasha sanarwa sai yace mata Babu koma to yau dinma dai sunanta taji tsuntsun yana ambata tayi wuki² jikinta sai rawar firgici yakeyi can bayan kamar shudewar mintuna talatin kukan tsuntsun ya dauke cak sai kuma ta rinka jiyo dariyar wata siririyar murya tun daga nesa ta rinka jiyo dariyar kamar matsota takeyi cikin kidima tayi wurgi da fitilar tana furta La'ilaha illah anta subhanaka inni kuntu minazzalumin, A'uzubikallimatullahi tammat minsharri ma kalak..."Bata gushe tana addu'a ba kuma Bata daina jiyo dariyar ba har Saida aka saki wata walkiya me karfi tare da tsawa sannan taji dariyar ta tsaya cak ta ruwa ya kece Hindu ta sauke ajiyar zuciya ta koma ta zauna baccin da Bata koma ba kenan har akayi Kiran asuba tayo alwala ta tayar sa sallah bayan ta idar ta zauna tana addu'o'inta tana tuna abubuwan da suka faru da ita marasa dadi a daren jiya, da Baba Mal yananan da tuni ta zayyane masa komai Amma yanzu saidai tayi kuka ta share hawayenta.
Komawa tayi ta kwanta bacci ya dauketa tunda dama da ramuwarsa a kanta cikin baccin taji ana busa mata iska ta firgita ainun ta Mike cikin rashin hayyaci ta sauke idonka kan Ila taja ajiyar zuciya tace “Amma Hamma Isma'il ka shiga kaina na tsorace ainun" murmushi yayi yana shafa sumarsa dan kyakkyawan saurayi fari tas dashi zubin Fulanin Chadi Wanda boko ta Dan shiga jikinsa da wayewar zamani sakamakon karatu da yayi a Niger da kuma kasuwancin safarar shanu da sukeyi da mahaifinsa Baba Laminu.
Kamo hannunta yayi ya matso da ita kusa dashi suna fuskantar juna yayi kasa da fuskarsa daidai tata numfashinsu na bugun na juna yace “Barka da safiya Sarauniyata" wani gwauron numfashi ta sauke ta janye jikinta yayi murmushi yace “Saura watanni shida ki gama karatunki inason cikawa Baba Mal burinsa na ganin kinyi karatu Hindu idan mukayi aure bazamu zauna a Chadi ba Niger zamu koma zamufi samun nutsuwa muyi rayuwarmu me dadi Babu me sanya Mana idanu ko?"Murmushi tayi masa me dauke da yanayi na tausayawa mafarkinta na daren jiya yana dawo mata tabbas tanajin so kauna da muradin kasancewa da Isma'il duk da cewa tayi masoya da yawa daidai har shida kowanne baya wucce sati da furta mata kalmar so ajalinsu yake riskarsu Jamil ne kawai yayi dogon zango aka sanya musu ranar aure ana saura sati biki yayi hatsari a hanyar Niger ya rasu shi ko gawarsa baa samu ba tunda motar tasu wuta taci suka kone kurmus.
Tun shekara hudu baya da wannan abubuwa Suka yita faruwa ta rasa wanda zai kalleta yace yanasonta tun Baba Mal yana damuwa itama tana damuwa hardai Suka dangana tunda sunsan cewa komai lokaci ne idan lokacin yayi Babu wani abu da zai goge faruwa ko yuwuwarsa.
Firgigit ta dawo hayyacinta ta sauke idonta cikin na Ila tace “Hamma Ila kanajin wani abu bazai iya biyo bayan soyayyarmu ba nikam da ka hkr dani ka nemi wata kunyi aure kun rayu cikin aminci ni rayuwarka tanada muhimanci a gurina inajin tsoron kada kaima ka mutu...."Rufenta baki yayi yana girgiza mata Kai yace “Karki kara fadar haka Hindatu duk ran da kikaga ta mutu kwananta ne ya kare idan kwanakina kayyadaddune ko dake ko Babu ke sai na mutu to ki cire jin cewa alakata dake zatasa na rayu ko na mutu Allah shine kadai yasan abinda zai faru gobe nikam koma meye zai faru inasonki kuma zan aureki muddin Ina raye"
Lumshe idanunta tayi tace “Shikenan Allah ya tabbatar mana da alkhairi kaje zanyi wanka na fito" fita yayi yana cewa da ita “amma karki daɗe cikin gari da ƙauyen nan da nisa banason muyi shigar dare" bata bashi amsa ba ya fice itama ta shiga wanka ta fito ta sanya uniform ta fito da akwatinta da Baba Mal ya siya mata lokacin da yaje Umrah tayi kyau cikin shigar kayan makarantar tana fita ƙofar gidan sukayi kaciɓis ya dubeta sosai yace “masha Allah Hindu tsarki ya tabbata ga Allah daya ƙera halittar sa ke komai kyau yake miki shiyasa nakeson muyi rayuwa a birni dake"Yana maganar yana karɓar akwatin suka nufi tasha suka hau motar Galfarin cikin gari daga can suka shiga motar garin da makarantar ta su Hannah take basu isa ba sai huɗu saboda nisan dake akwai tunda suka taho walwalarta ta ɗauke take matsar hawaye duk dawowa Baba Mal ne yake kawo ta yau gata ta dawo babu Baba Mal sai Hamma Ila ne ya maye mata gurbinsa ita kuwa dame zata sakawa Hamma Ila bayan bashi amsar tayin soyayya da yakeyi mata har yake mafarkin ganinta matsayin mata a gareshi saidai tsoronta da amsawar yafi mata alkhairi domin bashi amsar a'a bata sonsa yafi alkhairi akan tace tana sonsa tunda anyi ba ɗaya ba ba biyu ba indai ta amsa tayin ƙaunar namiji to wa'adin rayuwarsa ya ƙare.
Har cikin makaranta ya rakata get na farko ya bata kuɗi da shopping ɗin da yayi mata ta karɓa tanayi masa godiya yayi murmushi yace “Yana cikin aikina kula da matata ki rikemin amanar kanki sannan ki rinƙa jin kamar ina tare dake zanje Sudan karɓo result ɗina kuma zanyi gyaran jarabawa zan iya ɗaukar wata biyu inna dawo zan shigo na ganki farin cikina idan kuma bandawo ba zanyi miki aike ina kuma fatan ranar gama makarantar ki ta zama rana ta farko ta lissafin kwanakin aurenmu insha Allahu"......*Bonus bonus bonus*
*Daga*
*Oum Hairan*Aslm alaikum
Barkanmu da sfy fatan kowa ya tashi lfy alkhairin dake cikin wannan sabuwar shekara da muka shiga ubangiji ya sadamu dashi akasin hakan Allah kayi Mana maganinsa Allah ka shiga lamarinmu bamu iyawa ka iya Mana don alfarmar Annabi Muhammad (S.A.W)
Kamar yanda muka saba bonus na sabuwar shekara mun farashi daga jiya munyi sauki akan sabin littafaina biyu da nakeyi YAR ME MAGANI da MARTANI maimakon 700 biyu yanzu idan kina/kana son biyu zaka biya 500 ne kinga ka siyi daya an baka daya kyauta kenan💃
Sannan zanyi muku bonus na littafaina guda ashirin da biyar zafafa duka zaku samesu kan farashin 1500 please bonus din daga 1-1-1445 ne zuwa 7-1-1445 tabdi kwasha² mutanena abokan arziki karku bari ayi babuku 💃💃💃Domin biyan kudinku ku tura ta wannan acct din 3184512451 Fauziyya Tasiu Umar First bank Sai ki tura evidence of payment dinki ta 09013718241
Idan ba Littafin Oum Hairan bane ba daidai yake dana Oum Hairan ba👍🏼👍🏼1- Habibullah
2- Queen Farha
3- Gidan Uncle
4- Adandi
5- Waceceni
6- Dhoom Ishaq
7- Auran Bazawara
8- Dubai
9- Matar Lamir
10- Juhud
11- Wani Qangi
12-Masarautar Mayu
13- Meya jamin?
14- Wata karuwa
16- Bamagujiya
17- Ruwan Jira
18- Rumah
19- Jinkirin aure
20- Zarrah
21- Zaman Period
22- Yar Kale
23- My Besties Husband
24- The deputy governor bride
25- This would
26- Hayar mace
27- Tukuici gataPlease banda Rumah, tukuici gata, da hayar mace, a cikin bonus dina
*Gold pen from Oum Hairan*
YOU ARE READING
ƳAR ME MAGANI
Fantasylabarin wata yarinya marainiya da danginta suka tsaneta saboda tunaninsu na itan ba mutum bace, ƙaddara ta sake haɗa ta da wani ɗan mafiya, shin yaya rayuwar Hindu zata kasance a hannu Imran?