39

30 4 3
                                    

39.....

Asibiti mai kyau aka kai Mama da alamun ma na kuɗine,haka Daddynsu Jabir yayi parking muka fito kai tsaye ɗakin da aka kwantar da Mama muka nufa tun a bakin ƙofar muke jiyo tashin maganganun su Gwaggo da Aunty Maryam handling ɗin ƙofar Jabir ya murɗa,Gaba ɗaya muka tura kanmu cikin ɗakin da sallama bakinmu

Mama idona ya fara tozali da ita,kwance take a gadon da robar jini a hannunta yana tafiya idanunta rufe yake da hakan ya sake tabbatarmin jikin Mama babu zancen sauƙi sai dai na wajen ubangiji

Ƙarasa shiga cikin ɗakin mukayi da su Gwaggo muka tarar dasu kan kujerun Roba guda biyu kusa da gadon da ɗaya Gwaggo ce ke kai ɗayar kuma Aunty Maryam, tsugunne mukayi gaba ɗayanmu muna gaishe su da tambayar ya mai jiki

Su Abbah ma haka suka yi ,Miƙewa mukayi  muka ƙara sa gefen gadon da Mama ke kai muna mata sannu dukda ba amsawa zata iya yi ba ba,Abbah dake tsaye bayanmu muka dawo ƙasa kan tabarma muka zauna shi kuma ya ƙara sa gefen gadon yana jerawa Mama Sannu

Gwaggo da tun shigowarmu naga yadda ranta yake a haɗe naji cikin ɗaga murya tana cewa
"Hauwa'u bata buƙatar sannunka Abdulllahi ganinka ma bata buƙatar yi saboda bata farko ta ganka ba,ka tafi yawon da bazai amfaneka ba saboda bakaine ka haifarmin ita ba idan ta mutu wata matar zaka canza,shiyasa ka rainawa mutane hankali gaka gaka zaka je ka dawo ka samo kuɗi babu kai babu alamunka"

Daddynsu Jabir ya juya inda Gwaggo take da har da yakai bakin ƙofa yana shirin fita
"Haba Gwaggo baikamata ki faɗi hakan ba gashi gaban yara,kuma asibiti koma mene yakamata ayi haƙuri ayi masa uziri,tunda gashi yazo yanzu"

Gwaggo cikin yanayin ɓacin rai ta sassauta murya ta ce"A'a Zaidu ai banso ayi masa wannan uzirin ba,ta kwana matarshi ta fara tarar da hantsi bai zo dubata ba dama nasan ko ba daɗe ko ba jima ungulu gidan ta take komawa ya bi zugar da ƴan uwanshi a kullum sukeyi masa akanta saboda ta fara tara ƴaƴa, shiyasa bai damu da ciwonta ba"

Daddynsu Jabir da na tabbatar shine Zaidu ɗin goshi ya dafe"Kash Gwaggo ya kamata kiyi shiru ko badan yara ba dan ita Hauwa'u ɗin ki duba fa a yanayin da take ciki mana Gwaggo,yanzu ma wajen likitan zan koma,kuma Abbahn Ahmad bakwai ba tayi ba yazo gidana yamin bayani kuɗi yake nema bai samu ba tunda ya fita da yadawo dare yayi ga yara babu damar yabarsu ya taho neman asibitin da aka kai matarshi ko ya fara tafiya neman gidana dan nasan bai sani ba,ki masa uziri,yakamata ki tausaya masa magidanci kamarsa yana fama da abincin da zasuci,ba shida wani mataimaki sai Allah sai wanda yaga Allah yayi koyi da annabin tsira(SAW)"

Jin kalaman Abbah Zaid yasa Gwaggo kuma fashewa da kuka"Nagode Zaidu dukda ban haifi matarka ba bare kuma kai da haƙuranka talatin na ganka da yaranka sainace a jiya ma nasanka,amma ka tunasar dani abinda namanta,inaso na ƙara wa zuciyar surikina wani mikin da yake cin ransa"

Sai kuma ta juyo ga Abbah ɗin tana cewa"Abdullahi ka yafemin dan Allah gaba ɗaya damuwar Hauwa'u mantar dani komai take yi tana cikin jarrabawa Hauwa'u ina tausayinta da yaranta,da babu Rumaisah tayiyu wani labarin ake bana Hauwa'u ba yau na yarda komai daga Allah ne amma akwai sababi, Allah ya kawo muku canji na alkhairi waɗanda suka zalinceku Allah yayi gaggawar saka muku waɗanda suka muku alkhairi Allah yayi gaggawar biyansu da alkhairi linkin waɗanda suka yi muku"

Gaba ɗaya jikinmu sanyi yayi Abbah ya goge hawayen dake bin fuskarsa duk juriyar Abbah yau gaza ta yadai daure yace"Amin Gwaggo"

Abbah Zaid ne ya fasa murza handling na ƙofar  ya dawo cikin ɗakin

"Abdullahi taho muje wajen Doctor ɗin,kaga da ba'ayi maganar nan ba na manta ban ce ka taho ba"Daganan suka fice tare da Abbah

Aunty da take tsaye tana goge hawayenta,Aunty Maryam ta miƙe gami da kallonta cikin sanyin murya tace

"Ga kujera Rumaisah kizo ki zauna mana"

Aunty ta girgiza kai "A'a Yaya Maryam nan ma yayi ina zama A'isha farkawa zatayi"

Aunty Maryam ta ce"ƙyaleta inta farka sai ki bawa Sumayyah ko takwararki su lallasheta,Ni gida nakeson zuwa tunda kunzo dama jiranku ya tsaidani"

Aunty ta ce"Eh hakane ya kamata kije gidan aga halin da ya ke ciki"ta ƙara sa maganar tana dawowa inda Aunty Maryam ta tashi ɗin

*********
Aunty Maryam na fita a ɗakin su Abbah su ka shigo tare da likita ledar jinin da ya sanya mata ya kalla da take daidai rabi

"Allah ya bata lafiya,matsalar da na faɗa muku itace dai ba wani damuwa bayan ita"Likitan da suka shigo taran naji yana ambatar hakan yana danna inda jinin ke ƙara gudu

Su Abbah suka haɗa baki gurin cewa "Amin"

"Yara gaba ɗaya sun ruɗe sunga Mamarsu haka kwance"Abbah Zaid ya ɗaura da faɗar hakan

Likitan yayi murmushi yana kallanmu "Karku damu insha Allah mamarku zata samu lafiya da wuri"

Muka ɗaga kai alamun gamsuwa duk da ni nawa ƙasan zuciyar yana tantama dan na ɗauki babban ciwo ne kaɗai kesa ayima mutum ƙarin jini kuma mutum yakai tsawan lokaci yana sharar barci,na dai fi tsammanin yunwa ta yiwa Mama kamun kazar kuku,Saidai yadda likitan yace Insha Allah hakan yasa na ajje wancen tunanin na sallama komai ga ubangiji Mai kunfayakun yana cewa kasance sai ya kasance komai da ikonsa yake samun gurɓin kasantuwa,Ah saboda shine gaba ɗaya wasu tunaninka basu samun gurbin zama a zuciyata bare su gurɓatar da tunanina na yarda komai yayi farko zaiyi ƙarshe kuma duk abunda yayi tsanani yayi tsanani ƙarshe sauƙi zai haifar na har abada amma saida izinin ubangiji ɗin in yaso sai rayuwar ta ƙare a haka amma akwai gidan madauwami da idan ka yarda da ƙaddarar Allah gareka sai yama musanye koba gidan duniya ba toh a gidan Aljannah

Muryar Abbah Zaid ta katsemin tunanin da nake Aunty ya kallah
"Ba yanzu zaki je gida bane zan wuce ne tunda angama komai"

Aunty da take bawa A'isha madara tace"A'a zani mana ka jiramu madarar A'isha ma ai ya ƙare saina haɗo wata"

Abbah Zaid ya riƙe baki da ya dubi Abbah"Abdullahi kaji dai Rumaisah kukayi wasa zata muku magaji da ɗiyarku fah"

Abba Zaid Aunty ta hararesa ta wasa tare da cewa"Nidai banasan irin wannan abun fa haɗa rigima yayima yawa"

Abba Zaid ya hararareta shima"Faɗar gaskiyar ce haɗa rigima, shikenan nayi shiru gaki ga masu ƴar nan"

"Ai ɗiyartace tunda yarinyar Hauwa'u ce saisu ma fini iko da ita tunda ɗiya macece"Abbah ne maiyin maganar da sai yanzu ya saka baki a zancen

Gwaggo kuwa cigaba tayi da fifita Mama ko uhmm bata ce ba dan da alama ta barwah yara firarsu ne sai dai murmushi da yake ɗauke da fuskarta da yayi nasarar ɓoye tsintsar damuwar da lamarin ciwan dake damun Mama

Abbah Zaid inda muke zaune dasu Jabir ya kallo tare da cewa"Kunga Jabir ku taso mu fara fita  tafiyin hanzari kuma kunsan zakiyi girki ?"

Aunty itama miƙewar tayi "A'a nifa na shirya,da Sumayyah zan tafi ta tayani aikin girkin ma"

Gwaggo maida dubanta tayi ga Rumaisah"Anya kuwa hidimar nan bata yawa Rumaisah kinga fa su Asiya duk anjima kaɗan zasu zo kuma kowacce zatazo da abincinta ga Sha'aban nasan zai baiwa ƙannensa su ƙara wani akan na gida ai...."

Da sauri Abbah Zaid ya tsaida Gwaggo maganar da take ƙoƙarin cigaba dayi"A'a Gwaggo babu wata hidima ai Rumaisah komai ta yiwa Hauwa'u inajin bata faɗi ba ai abotar makaranta wani lokacin sai ta ma ɗara wani zumuncin na jini musamman yadda abun ke taɓarɓarewa ki mana fatan Allah ya karɓi ayyukanmu"

Aunty ta yi murmushi ita ma ta cewa Gwaggo"Toh Gwaggo idan banma Hauwa'u Bama waye zai mata bata dashi mijinta babu kuma babu sai rufin asiri da za'ace kawai,tare muke komai daga Primary har junior,muna ma waɗanda alaƙarmu bata kai haka bama,shi arziƙi kyawunka dashi ka morawa wasu ai,shine zai sake yalwata"

Itadai Gwaggo rasa bakin magana tayi sai zuba sanya albarka take wa su Aunty Ni kaina Aunty da rayuwarta ta gama burgeni hakan ya ƙara min san Aunty yadda ya kamata a raina Aunty na ansarwa Aisha na rungumeta muka fito muna gaba nida su Jabir muna fira su Aunty na bayanmu dan mun rigasu fitowa da Jabir rabin firar tawa nakeyi dan shikam Muhammad saboda Abbah Zaid ya jera damu a yanda na fahimta kenan dan muna tafiya yana hangen Aunty a haka muka ƙara sa parking space na asibitin inda Abbah Zaid yayi parking motarshi muka ƙara sa muka tsaya jikin motar, kafin su Auntyn suka ƙara so suka buɗe motar muka shiga gidan baya a motarm firar muka ɗaura da Jabir ɗin duk da ni a ɓangarena firar batamin wani daɗi yarda tunanin ciwon Mama ya addabi zuciyata...........

NA CANCANTA!Where stories live. Discover now