Page 8

42 5 0
                                    

*LOKACI NE...!*
_Fitattu Biyar_

©️ *OUM MUMTAZ.*

    _No: 8_
_Free Page_

"Kiyi haƙuri Umaima, ki yafe min dan Allah! Wallahi ban ƙara auren nan da niyar cin amana ko kuma tozarta ki ba."  Lawal ya faɗa ma Umaima da take kwance kan doguwar kujera mai cin mutum uku,tin bayan tafiyar Innayo.
"Na riga da na faɗa maka, babu komai na yafe maka dik da nasan ni baka min laifin komai ba, amman ina neman alfarmar ka barni na fara sana'a, sannan naci gaba da karatu na, tinda kaga daman dalilin auren mu nayi diapering." Umaima ta faɗa muryarta a sanyaye, wanda har cikin zuciyarta bata jin kishin Lawal ɗin da hakan yake bata mamaki, a ranta tana addu'ar Allah ya daura ta akansa.
Lawal da daman naiman abinda zai faranta ma Umaima rai yake  babu gardama yace,"Na amince lamince miki Umaima, ki kama sana'a, sannan kuma kici gaba da karatunki, amman kuma kinsan sha'ananin kasuwa ta bazan iya daukar nauyin karatunki ba saboda yanda abubuwa suka taɓarɓare mana a wannan marrar da muke ciki?" Ya ƙare maganar yana ɗan ɗinke fuska haɗi sosa kai, wanda hakan yasa Umaima murmusawa ba tare da ta shirya ba, a ranta kuwa faɗi take mai hali dai bazai taɓa chanza halinsa ba.
"Kar ka damu da batun ɗaukar nauyi na, tinda kaga daman shekara ɗaya ce kawai ya rage na kammala, kuma daman kaga yanzu zanyi registration na first semester level 4 cikin satinnan da naji ance an fara,kasan sai da na rubuta exam na second semester level 3,kuma results da ya fito Alhamdulillah bani da matsalar carry over ko guda ɗaya." Umaima tayi maganar tana kallon Lawal da har ya saki fuska jin cewa zata ɗauki nauyin karatunta ba tare da yabi ba'asin inda ta samo kuɗin ba, wanda ita daman tasan cewa tin farko zallar maƙo da ƙin fidda kuɗi irin na shi ne ya hana shi ya barta taci gaba da karatun ta, amman sai ya fake da cewa wai shi bashi da ra'ayin matarsa tayi karatun boko, wanda ita kuma a lokacin da yake giyar soyayya na ɗibanta, babu gargada ta amince da abinda ya faɗa, sai daga baya ta fuskanci alkiblar sa na tsantsar son kuɗi da ƙin kashe su.
"Ah to masha Allahu abu yayi kyau, Allah yasa ki fara a sa'a. Mai kike son ci naje na kawo miki? Naga alama ko karyawa baki yi ba har yanzu tinda na shigo Amir sai faman kuka yake amma baki jisa ba"
"Kai da ka bar amarya a gida, ai bai kamata ace kazo ka tare anan ba Abban Amir, kawai ka tashi ka tafi,ni kuma kar ka damu zan tashi na nemawa kaina abinda zanci." Inji Umaima da ta tashi daga kwancen da take, fuskar ta da murmushin karfin hali, wanda tin dazu shi take sabida ya boye mata yanayi na ƙunci da take fama da shi.
"Kar ki damu da amarya, dan Allah ki faɗi abinda za ki ci naje na kawo miki na hutar dake." Lawal ya faɗa ba tare da ya maida hankalinsa akan zancen amaryarsa da ta masa ba, wanda dik wani abinda ake ta faman yi tin dazun tana nan maƙale cikin zuciyarsa sabida ba rabuwan dadi suka yi ba kafin ya fito, akan yace zai tafi wajen Umaima, ita kuma ta dage sai ta bisa yace ba zata ba.
"Ka karbo min awara to." Inji Umaima a taƙaice ganin Lawal ya dage sai ya kawo mata, sabida so take yayi ya tafi ya bata wuri ta zauna tasha kukanta da take kokarin dannewa, wanda daman ita kuka ya jima da zama abokinta ba wahala yake bata ba.
Da rawar jiki kuwa Lawal da yake jin shakkar Umaima ya fice, a ransa kuwa kima da kuma kaunarta kara yawa yayi a cikin zuciyarsa sabida bai taba tsammanin magana ta arziki zai sake shiga tsakanin sa da ita ba idan taji labarin aurensa, amman sai gashi ta basa mamaki kwarai da gaske wanda wani ɓari na zuciyarsa yake tambayar sa anya kuwa ma tana son sa kaman baya?.
Wanka ta shiga, bayan ta miƙa Amir tsakar gida wajen yara, da yake yau babu makaranta. A dai-dai sanda ta fito daga wankan Lawal ya shigo daga sayo mata awarar, wanda ya ɗan jima sakamakon layin da ya tarar a wajen, tare suka shiga parlon, Umaima ta shige daki, shafa mai tayi, sannan ta zabo wani less ɗinta da ta ɗinka a auren Aunty Hamida, sosai ɗinkin riga da skirt ɗin yayi mata kyau, ya kuma dace da farar fatar ta mai daukan idanuwa. Powder ta shafa, sai kuma lips glow mai danko da ta shafa a labbanta masu dan kauri da suka kasance kalar pink mai duhu. Sosai tayi wani irin kyau na ban mamaki bayan ta daura ɗankwalinta na network, kasancewar ta kyakkyawa son kowa ƙin wanda ya rasa, wacce take da diri mai ɗaukar hankalin dik wani lafiyayyen namiji(coca cola), wai don ma a hakan yanayin ta ya sauya sakamakon fitina da tashin hankalin da Lawal yayi ta faman wulla ta a cikin tsawon zamansu, ga kuma matsalolin yan gidansu da ya sako ta gaba.
Sosai ta mugun tafiya da hankalin Lawal a sanda ta fito, bugu da kari ga kuma wani kamshi mai sanyi na musamman da yake tashi a jikinta. Umaima zama tayi a kan kujera, taci awarar ta a natse kaman babu wani abinda ke damunta cikin zuciya.
"Zan je can unguwar, idan na dawo akwai magana mai mahimmanci da za mu yi da ke." Lawal yace a lokacin da yake mikewa tsaye hadi da gyara karin hularsa ta zanna da ke kansa.
"To a dawo lafiya, ina son zuwa gida, daga can kuma zan tafi bakin kasuwa akwai kananun abubuwan da nake son saya dan Allah."
Kallon ta yayi kaman banzai amince da tafiyarta gidan ba, sabida yana tsoron kar ta tafi gidan a cikin wayannan yayun nata da yaga suna masa kallon tara saura kwata, a samu wacce za ta zuga ta, tazo tayi masa bore, amman kuma da ya tuna cewa akwai mahaifiyarta da Umaiman take bukatar lallashin mahaifiya a wannan gaɓar babu tantama idan yace kar ta tafi gidansu bai mata adalci ba, hakan yasa shi faɗin, "To sai kin dawo, ki gaisar min da su Ammahn, anjima da yamma nima zan shiga mu gaisa da su, ga wannan dari biyar din kiyi kudin mashin, wannan dubu biyun kuma ki samu ki sayi wasu abubuwan da baza a rasa ba." Ya mika mata dubu biyu da dari biyar, tasa hannu biyu ta karba tare da godiya, a ranta kuwa fadi take, 'dik da ina da kudi, amman raba arne da makami ma ibada ne.'

LOKACI NEWhere stories live. Discover now