AURE UKU
(a hospital romance )
By chuchujay
wattpad :@chuchujay
https://whatsapp.com/channel/0029Va9RLKT2P59fHSa7Ia1j
Join My whatsapp channel inda Zan baku noorurrahman kyauta.
Yes paid novel ne amma Zan baku shi a channel ɗina kyauta,
Just follow and share i want audience domin baku.
Episode2⃣5⃣➡2⃣6⃣.
Baki ɗaya haka nan Umaimah ta karasa ranarta a sukurkuce,bata san kasancewar paki a tare da ita ba Ya kamata sosai sai a yau da kwata kwata bata ji sa ba ko tagansa,
Motar yaya Abubakar da ta gani a gida Shine Ya tabbatar mata da yana gida ,
Parking motar ta tayi a gefen tasa ta nufi sashen sa kai tsaye,
Tun a ƙofa taganshi yana shirin shiga,
Yana ganin ta Ya faɗaɗa fara'ar sa yace "umaimah Kin dawo kenan,"
Murmushi tayi tace" wallahi yaya na dawo and ganin motanka yasa nazo na gaishe ka cos na kwana biyu ban ganka ba,
Shiga yayi tana biye dashi a baya,
A falo ta tarar da iyalan sa ,da gudu yaran sukazo gareta suna mata oyoyo inda mahafiyarsu ke ta mata fara'a tana Mai faɗin dama wai kina gidan nan umaimah,yaushe rabon da na saki idona?
Zama tayi tana Mai faɗin"maman sultan baza ki gane ba fitar ce da sassafe wani lokaci bana shigowa sai dare Chan,".
"Gaskiya dai Allah Ya taimaka ,aikin ku Ai sai ku,
Bari na kawo miki abinci,
Da saurinta tace "a'a Aunty Im okay dama nazo magana ne kawai da yaya Abubakar."
Ƙaramun murmushi tayi tace "bari na baku guri dan tsakanin ki da yayanki sai Allah"
Bayan tafiyarta Ya Kalleta yace "umaimah Allah yasa lafiya,"
Murmushi tayi tana Mai Wasa da hannunta tace"Yaya dama ina san magana da kai ne,ko nace ina san na nemi shawarar ka saboda ina tsoran nayi abunda zai dameni,wasa ta cigaba dayi da hannunta Kafun tace"Yaya I've found someone ,i mean wanda yake san Ya Aureni and im not against it,
I might sound somehow amma yaya Im loving the idea saboda ive fallen for this guy,
Sannan yaya bai tab'a Aure ba and He's just a month older than me,
Shine babban abunda nake tsoro sabida abunda mutane zasu ce,wasu zasu ga kamar Im selfish ina ƙokarin jansa cikin rayuwata bayan nasan ko Aure bai tab'a yi ba,amma yaya abunda nake ji a tattare dashi ko akan Hafiz banji ba,sannan yana mun soyayyar ni kaina takan bani tsoro,
Ban san Ya zanyi ba,
Duk abunda na fuskanta a rayuwa ta a wannan karan bana ganin komai sai alaƙata dashi
Shiru Yaya Abubakar yayi bayan takai ƙarshen zancen ta Kafun yace"a ina yaran yake ,ɗan gidan wanene".?
Licking lips ɗin ta tayi tace"Yaran Admiral Muktar paki ne"
Riƙo hannun ta yayi yace kali nan umaimah,eh nasan abun sound somehow amma it doesn't matter ,nasan dole mutane zasuyi magana kamar yarda kika ce amma abu mafi muhimmanci Shine muddin idan zuciyarki ta kwanta dashi ta yarda dashi ki saurareta ,saboda you deserve some happiness Sannan yaran nan bake kika masa dole Ya soki ba ,shine yaji yana sanki kuma ya amince zaiyyi rayuwar sa dake so Allah wadai duk abunda mutane zasu faɗa.
YOU ARE READING
AURE UKU(completed)
RomanceDR UMAIMAH USMAN BULAMA,Mace yar kimanin shekara ishirin da tara , Babbar surgeon A asibitin CITY TEACHING HOSPITAL , Aure Uku, ƴaƴanta uku . Mace mara san hayaniya wadda tasan kan Aikinta ,babu abunda tasa a gabanta illa bawa Aikinta babban muhimm...