part 35

8 0 0
                                    

*SANADI*

*Wasila Abdul Muhd*
     *_Ummu Aisha_*

*AREWA WRITERS ASSOCIATION*

*35*

  Wata irin soyayya da shaƙuwa ce ƙara ƙulluwa a tsakaninsu a cikin kwanakin, a kokacin Khairat ji ta ke ta kusa ta yi wa kanta asara, da ta fasa auren Zaid da ta so fasawa a baya, lallai ta tabbatar ba ƙaramin gata iyayenta su kai mata ba da au ka aura mata shi ba tare da sake jin ra'ayinta a karo na biyu ba.

  Duk wanda ya kalle ta sai ya sake kallonta saboda wani irin kyau da ta yi, jikinta ya ƙara gogewa.

  Ranar da ta cika sati biyu a gidansa ya kai ta gidansu gurin mahaifiyarsa, a nan ta ga tsantsar soyayya kamar ta haɗiye ta, har dare ta na gidan, don sai bayan sallar isha su ka tafi gida.

  Bayan kwana uku kuma gidansu ya kai ta, nan ta ga murna a gurin Aunty Maimuna kamar ta goya ta, sai ina ka sake ta ke da ita, komai ta ɗauko ta kawo mata.

  Lokacin da Daddy ya dawo kuwa a nan ta ga ainahin soyayya irin ta ɗa da mahaifi, ganinta a gidan ya fasa fita ko ina ya zauna a gida su kai ta hira.

  A ranar idan ka tona zuciyar Aunty Hadiza kamar ta kama da wuta don ɓacin rai da damuwa, babbar damuwarta yadda ta na zaune da Sa'ad shekara da shekaru ba ta taɓa ko ɓatan wata ba, amma wata da ta zo daga bayanta ta haihu, kuma ta na kallon ƴaƴan babu yadda ta iya da su, sannan kuma SANADInsu anyi mata wata kishiyar, abinda ta fi tsana fiye da komai a rayuwarta.

Da za ta fafi  kuɗi sosai Daddy ya ba ta ya ce "duk abinda ki ke so kar ki matsawa mijinki ki tambaye ni, insha Allahu ko menene zan yi miki shi, ba na ki dinga yawan damunsa da kawo-kawo.

   Zaid ne ya zo ɗaukarta ya sha guri Daddy bayan sun gaisa da shi ya ke tambayarsa da cewa "kun je gidan Hajiya Mama kuwa?"

  Zaid ya ce "a'a."

  Daddy ya ce "saboda me? yanzu idan kun bar nan ka tabbata kun biya ta can."

  "Ka yi haƴuri Daddy yanzu dare ya yi, amma insha Allah gobe zan kaita." Zaid ya faɗa kansa a sunkuye.
 
  Sai ya ce "Allah ya sa mu na da rabon ganin goben"

  Ta yiwa matan gidan sallama kamar yadda Daddy ya bata umarni, Aunty Hadiza kam ko ɗaga kai ba tai ta kalleta ba bare ta saka ran za ta tanka mata.

  Aunty Maimuna kuwa sallama su kai sosai ta bata wata leda, tai mata godiya mai yawa su ka tafi.

  Washegari da yamma ya kai ta gidan Hajiya Mama kamar yadda yai wa Daddy alƙawari, nan gidan kam ba ta yini ba, don sai bayan azahar su ka je kuma ana yin sallar la'asar su ka tafi, saboda ganin yadda Khairat ta kasa sakin jiki a gidan.

  Zaman lafiya suke gudanarwa sosai a tsakaninsu, kowanne a cikinsu burinsa ya farantawa ɗan uwansa rai.

  Kallum sai ta kira Ummi a waya sun ji lafiyar juna, haka ma Aunty Maryam su na yawan waya akai-akai, wannan ya ƙara kwantar da hankalinta sosai.

_________________________________________________

  Watansu huɗu da aure tafiya Kano ta kama ta, saboda bikin Ummulkhairi da ya taso, duk da itama ta na fama da laulayin ƙaramin cikin da ta ke ɗauke da shi wanda bai cike watanni uku ba.

  Shiri sosai ta yiwa tafiyar, ga kuɗi sosai da Zaid ya bata saboda tsaraba, da farko ce wa yai su fita su sayin kayan tsaraba, sai ta nuna masa da ya haƙura idan ta je can a sayi abinda ya kamata kamata kaya, cikin sa'a kuma ya amince.

  Hajiya Mama ma turamen atamfofi biyu ta bata ta kaiwa Ummi da kuma saƙon gaisuwa, kuma ta ce ta gaya mata ta na nan tafe takanas za ta zo don neman yafiyarta akan abinda ya faru a baya.

  Aunty maimuna ma ta bata turaren wuta masu kyau ta kaiwa Ummi, haka suka tafi cike da tsaraba, duk da ba ta son kaya, tare su ka tafi da Zaid, amma shi ba kwana zai yi ba, washegari zai koma.

  Sosai su kai murnar ganin juna ita da Aunty Maryam,Khairat ta sha mamakin ganin cikin Aunty Maryam da ya yi girma soaai, don ita ba ta ma san ta na da cikin ba.

  Ta je sun gaisa da Ammie kadaran kadahan tun da dama tun farko babu sakewa a tsakaninsu.

  Washegari tare su ka fita da aunty Maryam ta sayo tsaraba tare da gudunmawar da za ta bai wa amarya, daga nan kuma su ka wuce gidan Ummi Habiba.

  Cewa tai su koma da tsarabar gidan Abba Maryam ta yi duk abinda ya dace, wannan kara da Ummi tai mata ba ƙaramin daɗi ta ji ba.

  Bayan sun koma gida haka ta zauna ta kasafta komai yadda ya kamata, abin mamaki da aka kaiwa Ammie sai ta sa aka dawo musu da shi wai ba ta buƙata.

  Misalin huɗu da rabi na yamma Khairat ta fito a shirye cikin kyakkawar kwalliyar da ta yi ta wani lace ɗinkin riga da skirt da yai matuƴar karɓar jikinta.

  Drivern gidan ne ya ja ta zuwa gidan su Ummulkhairi, din a ranar za'a fara gudanar da shagalin bikin.

  Daga Ummulkhairi har mahaifiyarta babu wanda bai yi mamakin irin gudunmawar da Khairat ta kawo ba, ta sha godiya kuwa.

  Tun daga ranar kullum sai ta je har aka gama biki aka sada amarya da ɗakin mijinta, Ummi ma ta je ranar yini tare da Aunty Maryam.

  Washegari kuma gidan Ummi ta yini har dare, sun sha hira ita da ƙannenta.

  Satin ta ɗaya a Kano tattara ta koma da tarin tsarabar da aka haɗa mata, duk da ba ta son kaya, don ma drivern Abba ne ya mayar da ita a mota, saboda yanayi na hazo, ranar babu jirgin da zai tashi.

  Shi kansa Zaid bai san da dawowarta ba, saboda ya san babu damar zirga-zirgar jirage sakamakon hazon da rufe sararin samaniya, misalin uku da rabi ya na kwance a parlour ya na kallon ball, shi da ƙaninsa mai su na Khamis, sai su ka ji ana danna bell, Khamis ɗin ne ya je ya buɗe, ganin Khairat ce ya fara yi mata sannu da zuwa.

  Da mamaki Zaid ya juya don ganin wa ake  yiwa sannun da zuwa, ya na ganin Khairat ya tashi da sauri ya rungume ta cikin farin cikin ganinta.

  Shi dai Khamis komawa yai ya zauna cike da basarwa, bayan sun gama murnar ganin juna su ka nemi mazauni, sai sannan Khairat ke sanar masa cewa tare ta ke da driver.

  Nan take ta haɗo ruwa da lemo ta bawa Khamis ya miƙa masa, sannan ya fara shigo da kayanta cikin gidan maigadi na taya shi.



*Ummu Aisha*✍️

 

SANADIWhere stories live. Discover now