*PART (2)*
*EPISODE (9)*•••••(GIDANSU AAREEF NIGERIA)•••••
Shiru Falon Yayi Na Yan Sakanni Bakajin Komai Sai Karar Fankar Dake Juyawa A Saman Falon Mommy Ce Ta Sake Cewa " Wata Matsalar Ce Tareda Result Din? "Bama Karama Ba Sam Result Din Baiyi Kyau Ba Saboda Gwajin Ya Nuna Shi (AS Itama SS) Auren Su a Hakan Babbar Illa Ce Ga Yaran Da Zasu Haifa 99% Zasu Iya Kasance Wa Dauke Da Cutar Sikila, Abba Yafada Cikin Rashin Jin Dadin Abun, "Ya Salam To Kai Aareef Dama Jinin Naka AS Ne Tun A Gwajin Da Kayi A Bayan? Mommy Tafada Tana Kallon Aareef Din, A Hankali Ya Dago Kansa Yace "Mommy Nima Nayi Mamaki Saboda Wancan Gwajin Da Nayi A Can Asibitin (Dignity Health - St. Rose Dominican Hospital) Result Din Ya Nuna Mun Genotype Dina (AA) Ne, Shiyasa Nayi Mamaki Da Genotype Result Din Yanzu Ya Nuna (AS), Saudert Shin Dama Hakan Ka Iya Faruwa Ne, Cewar Aareef Yana Kallon Saudert Da Hankalinta Ke Kan Message Dinda Ayyush Ta Turo Mata a Whatsapp Kan Shiryen Shiryen Bikin Tareda Batun Karbo Dinkunan Ankon Shagulgulan Bikin Da Zasuje Jibi, Tama Rasa Me Zata Cemata Tausayinta Ne Ya Kamata Tana Tunanin Idan Hakan Ta Tabbata Wanne Hali Ayyush Zata Shiga, Dagowa Tayi Tace "Eh To Brother Meybe Hakan Yana Faruwa Especially Idan Aka Dauki Shekaru Dayin Gwajin Kuma Kaga Yanayin Weather a Las-Vegas Da Banbanci Da Na Nan, Ta Karashe Zancen Nata Idanunta Nakan Yayan Nata, Shiru Yayi Ba Tareda Yace Komai Ba Ya Rasa a Wanne Feeling Yake Farin Ciki Ko Akasarin Hakan, Dr. Abubakar Ne Ya Dauki Wayarsa Tareda Lalubo Number Dr. Mu'azzam Ya Kirasa Saida Takusa Katsewa Sannan Ya Dauka Da Sallama Yace "Dr Afuwa Kajini Shiru Naje Meeting Din Likitoci Na Kasa Ne Abuja Yanzu Haka Ina Kan Hanyar Dawowa Kano, Cewar Dr. Mu'azzam "Hakane Dr Dama Ai Ku Dole Amuku Azuri Saboda Yanayin Aikin Ku Bana Zama Bane Fatan Anyi Taron Lafiya, "Lafiya Klau Alhamdulillah Ya Aareef Kuwa Yaje Ya Karbi Result Din Nasu, "Eh Ya Karbo Tun Jiya Sanadin Hakanne Ma Yasa Na Kiraka Dr. Abubakar Yafada Tareda Yimasa Bayanin Duk Abunda Yafaru Ya Karasa Maganar Da Cewa Shekaru 4 Da Suka Huce Da Yayi Gwajin a Can Las-Vegas (A•A) Result Din Ya Nuna Masa, "Ikon Allah Eh To Ana Samun Haka Amma Yiwuwar Hakan Kaso 10% Ne Cikin 100% Amma Yau Idan Na Dawo Gobe Bazanje Asibitin Ba Jibi Saisu Zo Nayi Musu Gwajin Dakaina Danmu Tabbatar Da Sahihancin Sakamakon, "Okay To Babu Laifi Nagode Dr Allah Yakaimu Jibi, Abba Yafada Sannan Sukayi Sallama, Mikewa Yayi Sannan Yace "Nidai Yanzu Zanje Na Kwanta Saimu Jira Jibin In Allah Yakaimu Saikuje a Sake Gwajin Bayan Nan Sai Musan Abunyi Amma Kafun Nan Karfa a Sanar Da Ameena Ko Ita Aysha Din, "Dama Abban Aareef Ai Bama Za'a Iya Sanar Dasu Ba, "Ke Kenan Amma Su Tsaf Dan Shashanci Saisu Iya Sanar Musun Badan Nayi Maganar Ba Musamman Aareef Wani Abun Idan Yayi Saikace Dan Shekara 10 Dr. Abubakar Yafada Tareda Shigewa Dakinsa.
Bayan Kwana Biyun Kuwa Ranar Lahadi Aareef Ya Fito Da Shirin Sa Da Niyyar Zaije Gidansu Ayyush Ya Sanar Da Mama Amina Cewa Bayan Isha'i Zaizo Ya Dauki Ayyush Suje UMC Domin Sake Gwajin Na Genotype, Zama Yayi Kusa Da Abban Nasa Yace "Abba Zantafi Gidansu Ayyush Din Domin Sanar Da Mama Batun Komawar Tamu Asibitin Karfe Nawa Ma Yace Muje, "Karfe 8 Na Dare Yace Amma Bari Na Kirasa Yanzu Muji, Yana Kiran Nasa Kuwa Ringing Daya Dr. Mu'azzan Ya Dauka Bayan Sun Gaisa Kafun Dr. Abubakar Ya Tambayesa Batun Lokacin Da Aareef Zasuje UMC Din Yau, Katsam Abba Ji Yayi Dr. Mu'azzam Yace "Dr Yanzu Dama Nakeson Kiranka Wannan Result Dinfa Dake Wajenku Bana Su Aareef Bane Cikin Matukar Mamaki Abba Yace "Ahh Ban Fahimceka Ba Dr Bashi Bane Kuma, "Eh Tabbas Yanzu Dana Shigo Office Dina Naga Result Din Nasu Aareef Akasi Aka Samu Maimakon Nakai Wa Dr. Bash Nasu Suje Su Karba Sai Nakai Masa Na Wasu Da Nayi Dasu Yau Suzo Su Amsa Saida Yanzu Sunzo Na Dauka Zan Basu Abun Mamaki Sai Naga Sunan Aareef Kuma Alhamdulillah Shi Wannan Result Din Nasu Yayi Kyau Yadda Akafi Bukata Saboda Duk Genotype Din Nasu (AA) Ne, "To Masha Allah Mungode Wa Allah "Yawwa Dan Haka Ko Yanzu Zai Iya Zuwa Ya Karbi Shi Wannan Result Din Inyaso Sai Ya Tawo Da Wancan "Shikenan Yanzu Zaizo Kuwa Mungode Fa Da Kokari Dr, "Babu Damuwa Dr Kahuce Haka Ai Cewar Dr. Mu'azzan Sannan Sukai Sallama, "Abban Aareef Ya Akayi Cewar Mommy Da Fara'a A Fuskarsa Yace "Kinga Ashe Wannan Result Da Aareef Ya Anso Ba Shine Nasun Ba Nasu Alhamdulillah Ya Cika Duk Wata Ka'idah Da Ake Bukata, "To Masha Allah Har Naji Hankalina Ya Kwanta, "Mommy Wallahi Nima Bakiji Yadda Naji Dadi Ba, Inji Saudert, Shikuwa Aareef Tunda Yaji Bayanin Da Abbansa Kewa Mommy Da Saurin Sa Ya Nufi Dakinsa Ya Dauko Wancan Result Yadawo Falo A Hankali Yace "Abba Kaga Kuwa Sunan Nuradden Da Salma Shine Ajikin Result Din Nayi Mamaki Ya Akai Ma Bamu Kula Ba Aareef Yafada Sannan Ya Mikawa Dr. Abubakar Result Din Fuska Ba Yabo Ba Fallasa, "Kwarai Kuwa Ance Dama Hankali Shike Gani Sam Bana Cikin Kwanciyar Hankali Lokacin Da Na Duba Yanzu Dai Karbi Katafi UMC Din Yanzu Yana Nan Kaje Ka Kai Masa Wannan Result Din Ka Karbo Nakun "Tho Abba Aareef Yafada Sannan Ya Amshi Result Din Yayi Musu Sallama Da Niyyar Fita Saudert Ce Tace "Brother Please Ka Kaini Gidansu Ayyush Din Kafun Katafi Tun Dazu Taketa Kirana Zamuje Karbo Dinkunan Mu Na Bikin Bansan Yadda Abun Zai Kasance Bane Yasa Naketa Yimata Hanya Hanya Amma Tunda Yanzu Komai Yayi Normal Sai Naje Mutafi, "Zaki Batan Lokaci Dai Kawai Nida Zanje UMC Janbulo Ana Jirana Mezai Kaini Gidansu Ayyush Kuma? "In Banda Abunka Aareefu Ina Gidan Nan Ina Gidansu Ayyush Ka Kaita Mana Saika Huce "To Shikenan Mommy Yi Sauri Ki Shirya To "Ashirye Nake Ma Mayafina Kawai Zan Dakko 2Minutes Tafada Tareda Shigewa Dakin Nata Ba Dadewa Ta Fito Tayiwa Su Mommy Sallama Sannan Suka Tafi Saida Ya Sauketa a Gidan Su Ayyush Din Sannan Ya Huce Asibitin Na (UMC).
YOU ARE READING
MAFARKINA NE (2)
RomanceGenre : Romance Story/Novel/HeartTouching. Labari Ne Daya Kunshi Mafarkin Zama Wani Abu a Rayuwa, Tasirin Kyautatawa, Soyayya, Hadin Kai Da Kalubalen Rayuwa Da Sauran Su .